Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Legas: Malami Ya Yi Wa Dalibarsa Fyade A Dakin Nazarin Kwayoyin Halitta

Published

on

A rannar Litinin ce, alkalin kotun Ikeja ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wani malami mai suna Idowu Daniel dan shekara 28, bisa laifin ya wa dalibarsa ‘yar makarantar sakandare mai shekaru 17 fyade. Alkali mai shari’a Olufunke Sule-Amzat, ta yi fatali da duk wata hujja da wanda a ka tuhuma ya bai wa kotu, inda ta bayar da umurnin a cigaba da tsare shi a gidan yarin Kirikiri. Sule-Amzat ta bai wa ‘yan sanda umurnin su taru fayal din shari’a ga maka’aikatar shari’a na jihar domin samun shawarwari. Sannan ta dage sauraron wannan kara har sai ranar 21 ga watan Oktoba.

Shi dai wanda a ke tuhuma ya na zauna ne a yankin Abule-Egba da ke cikin Jihar Legas, ya na fuskanta tuhuma na fyade.

Tun da farko dai, lauya ‘yan sanda mai gabatar da kara, ASP Benson Emuerhi, ya bayyana wa kotu cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan aika-aikan da dakibarsa ne a ranar 27 ga watan Yuli da misalin karfe 9.25 na safe, a dakin nazarin kwayoyin halitta na makarantar sakandare ta Anastasia Comprehensibe College da ke yankin Abule-Egba cikin garin Ikeja.  “Malami ya ja dalibarsa zuwa dakin nazarin kwayoyin halittu da ke cikin makaranta, sannan ya yi lalata da ita,” in ji lauya mai gabatar da kara. 

Wannan laifin dai ya saba wa sashe na 137 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015. Sashen ya tanadi daurin shekara 14 a gidan yari ga duk wanda a ke samu ya aikata laifin fyade.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: