Connect with us

TATTAUNAWA

Mun Samar Wa Matasanmu Hanyoyin Dogaro Da Kai – Hon. Jabir Rigasa

Published

on

HONORABUL JABIR KHAMIS RIGASA shi ne Shugaban Karamar Hukumar Igabi da ke jihar Kaduna. A wannan tattaunawar da ya yi da LEADERSHIP A YAU ya bayyana irin ayyukan da ya ke tinkahon ya aiwatar, da wadanda yake da niyyar yi a wannan zango na mulkin nasa, inda a ciki ya bayyana cewa sun mayar da hankali matuka wajen ganin matasan Karamar Hukumar sun sami ayyukan da za su yi don dogaro da kansu.

Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa duk da Karamar Hukumar ce mafi girma a fadin Kananan Hukumomin jihar, ya zuwa yanzu ya aiwatar da ayyukan da ko da ya bar kujerar, za a rinka tunawa da shi. Akwai bayanai da dama a cikin wannan tattauna. A sha karatu lafiya.

Karamar hukumar Igabi ta kasance daya daga cikin kananan hukumomin da suka fi yawan jama’a a kasar nan.  za mu so jin abubuwan da ka aiwatar a wannan shekara guda da ka yi ka na shugabantarta?

Bismillahir rahamnirrahim. Gaskiya ne, kamar yadda ka fada, Karamar Hukumar Igabi tana daya daga cikin Kananan Hukumomi mafi girma a kasar nan, a jihar Kaduna kuwa ba na jin akwai wata Karamar Hukumar  da ta kai ta girma. Kuma cikin ikon Allah, bisa yanayin da muka samu Karamar Hukumar, za mu iya cewa mun taba abubuwa da yawa.

Saboda lokacin da muka zo mun samu gwamnatin jihar ta yi wasu ’yan gyare-gyare, musamman ta bangaren ma’aikatan ilimi da sauransu, amma a lokacin wasu ma sababbi ne ba a fara biyan su ba. Saboda haka gaskiya a lokacin mun samun kudi, har ma a lokacin mai girma Gwamna yana ce mani attjiri ne, saboda ya san da kudin da muke samu na rara a lokacin. Saboda haka daidai gwargwado ana samun kudaden da za a yi wa jama’a ayyuka.

Kuma daidai gwargwado mun yi ayyuka a cikin shekara dayan nan, domin za mu iya cewa mun yi hanyoyi guda shida, cikin wadannan hanyoyi yanzu haka an kammala guda hudu, ba a kammala biyu ba. Akwai wacce muka ba da a garin Jaji ta tafi zuwa Zango, an kammala ta. Akwai wacce ta ke a cikin Birnin Yero Tasha, ita ma an kammala ta. Akwai Kamfanin Zango zuwa Kadauji. Akwai nan Lokoja Road da ke cikin Rigasa, akwai kuma wacce tatashi daga caji ofis na ’yan sandan Rigasa zuwa Maigiginya.

Cikin wadannan ayyukan na hanya akwai wacce muka gada, wanda yake aiki ne kusan babu wata Karamar Hukuma a Kaduna da ta taba yin wannan aikin. Saboda aiki ne wanda ya hada Kananan Hukumomi biyu, ta Igabi da ta Kaduna ta Kudu. Amma saboda Karamar Hukumar Igabi ta fi ta Kaduna ta Kudu yanayin samun kudi, sai ba a tsaya an kalli Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu ba, sai aka kalli aikin kawai, wato hanyar da ta tashi daga Kurmin Mashi zuwa Mahuta.

Gada kaiwa da muka yi a wannan hanya, idan aka ce maka Karamar Hukuma ce ta yi aikin, sai ka jinjina, don ba a taba yin irinta ba. Kamar yadda na ce maka, mun gaji wannan aiki ne mu kuma muka dora. Ana nan ana yi.

Sannan kuma mun yi asibitoci guda hudu su ma, su wadannan asibitoci duka an kammala su, sai dai katange wani asibiti da ke Rikogi a Mazabar Birnin Yero, shi ne kawai ya rage ba mu kammala shi ba. Mun yi a Hayin Kogi, mun yi a Kalgo, mun yi a Rikogin.

Wadannan duk ina fada maka ne, ban da gadoji manya da kanana da muke yi a ko’ina, kamar nan cikin Rigasa akwai wacce muke yi a Abuja Road, akwai kuma wacce ta tashi daga Wusono.

Bayan wannan kuma akwai aikin samar da wutar lantarki, akwai wanda ya tashi daga Gwada zuwa Bina a mazabar Kerawa. Akwai kuma wacce ake yi a Mazabar Gwareje. Akwai wasu Tiransifomomi da muka samu, duk da yake lokacin da muka zo mun dan samu tarnaki a kan Tiransifomomin.

Saboda shi kamfanin da ke samar wutar lantarkin, ya kamata a ce ya samar wa da jama’a Tiransifoma, musamman a wuraren da suka lalace, to amma sai ya gaza. Saboda haka a nan mun yi kokari mun samar da wasu, musamman akwai na Kamfanin Fate da ke Jaji da wasu wurare guda uku.

Duk da yake na ce maka lokacin da muka zo mun samu kudade a asusunmu, amma a yanzu gaskiyar magana idan ma ba mun samu wani tallafi daga Allah ba, biyan albashi ma zai mana wahala. Saboda a yanzu halin da ake ciki, Malaman Firamare da aka diba, wadanda za mu fara biya yanzu, sai an cika mana ma kafin mu samu mu iya biyan albashin, domin a yanzu haka suna bin mu bashin kudin da ya haura Naira Miliyan Dari Uku (N300,000,000). Saboda duk wata guda abin da za mu rinkk biyansu, Naira Miliyan Arba’in da Takwas da Dubu Dari Uku da Sha Biyar da wani abu, wannan ina gaya maka a duk wata, wadanda aka diba.

Kuma tun daga Watan Janairu suka fara aikin nan, kuma ba a biya su ba tun lokacin har zuwa yau (lokacin wannan tattaunawar). Misali, a wannan watan in Allah sa muka samu kudin, kuma ana so mu ne mu fara biyansu da bashin baya. To ka ga idan za mu biya da bashin baya, a misali a ce muna samun rarar Naira Milyan Hamsin a yanzu, to sai aka ce za mi biya bashi, ka ga ke nan muna neman karin wasu miliyoyin ke nan kafin mu samu mu iya biyan albashin. Saboda haka wannan shi ne babban kalubalen da muke fuskanta a yanzu.

Sannan kuma akwai wasu ayyukan da muka gada, wadanda su mu ke son mu ci gaba da su. Domin shi aiki irin wannan, yana da kyau in ka gaji wani aiki da aka fa domin al’umma, to ka kammala shi don amfnin al’ummar, aiki ne na gwamnati, kai kuma mai gudanar da aikin gwamnati ne, kafin kai ka zo, wani ne ke gudanarwa, saboda haka in ka samu wani abu na alhairi da wancan ya fara, to kai ma ka dora akai don amfanin jama’a.

Saboda haka muna da irin wadannan ayyuka da muka samu a Igabi, wanda akwai wasu da muka kara masu kudade don a ci gaba da yi, wadanda yake akwai hanyoyi a cikinsu da sauransu. Wasu kuma ba mu kara kudin ba, amma mun ja hankalin ’yan kwangilar, lokacin da muka sa kwamiti suka duba, suka duba inda aka tsaya da kuma kudin da aka ba su. Kuma muna fatan mu kammala wadannan ayyuka, wadanda muka gada da wadanda muka fara don ci gaban al’ummar Karamar Hukumar Igabi.

Wannan ya nuna kenan kamar mu ke ganin a kafar da sadarwa ta soshiyal midiya cewa an sakar maku da kudade, kwanan nan za mu fara ganin ayyuka ta ko’ina?

Ka san ita Soshiyal Midiya tana da amfani da rashin amfaninta, to daya daga cikin rashin mafninta ke nan, yada karya! Har yanzu maganar nan da nake yi da kai babu inda aka turo mana kwabo, ka dai ga yau muna 8 ga watan Yulin 2019 ko? Muna nan dai muna jira mu gani.

Amma cewa an turo mana kudi, karya ce. Akwai wanda ma ya ce mani ya gani, ni  ne na ma farko, an tura mani Naira Miliyan Dari Shida. Addu’a na yi da na ji haka, na ce masa Allah ya sa. In dai har wadannan kudade suka samu haka, za mu biya bashi mu ci gaba da taimaka wa jama’ daidai gwarwado.

Ganin cewa matasa ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma. ba mu san ko wane irin taimako ka ke yi don ci gaban matasan ka ba?

Akwai abubuwa da dama da muke yi. Dole ne mu jawo hanklin matasanmu su shiga aikin dogaro da kai, musamman a yanzu wajen noma. Ko a yau mun raba ma matasa da dama kayan noma, wadanda suka hada da iri, maganin feshi da abin feshin da takalmin zuwa gona da abin sanyawa a hanci.

Saboda haka lallai muna nan muna kokarin ganin matasa sun shiga aikin gona, domin mu gona ba wiya ta ke yi mana ba a Karamar Hukumar Igabi, domin mu a Karamar Hukumar Igabi in akwai abin da muke takama da shi, shi ne filin noma, saboda duk wani mai ji da kansa in dai yana da gona, to za ka ji a Karamar Hukumar Igabi yake da ita. Saboda haka mun sanya matasanmu a wannan harka.

Sannan kuma akwai kayayyaki da muka saya na koyar da sana’o’i, wadanda za a raba ma matasa wadanda suka kammala horo, har ciki ma akwai wadanda muka fuskanci ba a koya wa mutane da yawa ba a wurin. Musamman yanzu abin nan na kwalliya da mata ke samun kudin shiga ta wannan sana’a.  yanzu haka muna shirin kara ci gaba da horar da matan don ganin kowa ta samu kayan sana’ar bayan ta kammala horon.

Domin mu wani abu da muka sa a gaba shi ne, ba wai koya wa matasa sana’ar kawai ba, idan muka koya wa matashi ko matashiya sana’a, to za mu hada masu ne da kayan aikin da suka koya, ka ga ka sallame shi ke nan. Amma idan ka koya wa mutum sana’a ba ka ba shi kayan da zai yi sana’ar ba, to zai yiwu kafin ya samu nasa ya zama ya manta da abin da ya koya.

Misali, idan aski matashi ya koya, to ya zama bayan horaswa ka hada masa da kayan aski, in da hali ma ka hada masa da jannareta. Wannan yana daga cikin hadafinmu, kuma yana nan cikin kasafin kudinmu. Amma babban abin da muke addu’a, shi ne mu samu kudin da za a yi wadannan abubuwa da su.

Kwanan nan ne aka rantsar da kwamishinoni a jihar nan. wace shawara kake da ita gare su don tallafa wa Gwamna Nasiru el-Rufai?

idan ka duba tsarin sunayen wadannan Kwamishinoni, gaskiyar magana, duk kusan sanannu ne a wurinmu, mutane ne hazikai wadanda suka  san makamar aikin, kuma in Allah ya yarda za su taimaka wa mai Girma Gwamna domin a samu ci gaba.

Wadanne abubuwa kake tunanin za a rinka tunawa da kai bayan barinka wannan kujera?

Babu wasu abubuwan bari kamar samar da abubuwan raya kasa, domin ko bayan ba ka za a ce ‘wane ne ya yi mana wannan abin.’ Kuma alhamdu lillahi na yi ayyuka ingantattu, ba ayyukan da za su lalace shekara daya ko biyu ba. Ka tabbatar ka yi aiki ingantacce, wanda yake da ma a tsarin wannan gwamnati wajibi ne ka yi aiki ingantacce.

Sannan kuma ina so a tuna da ni ta hanyar ayyukan da na gabatar wajen rayar da matasa. Domin a lokacin da matashi ya samu abin da zai rike kansa da kansa, to ba zai taba mantawa da kai ba. Idan wani ya taso zai rinka fada cewa ‘a zamanin wane ne na samu aikin yi, a da ba ni da aiki,’ musamman yanzu da babu aikin gwamnati isasshe. Domin ba wai a sana’a kadai muka tsaya wa matasa ba, hatta samar masu hanyar shiga aiki soja, dan sanda kwastan da sauran irinsu, muna yin kokari wajen ganin matasanmu sun samu shiga.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: