Connect with us

TATTAUNAWA

Sana’ar Sayar Da Kaji Mai Albarka Ce – Husaini Adamu Ya’u

Published

on

ALHAJI HUSAINI ADAMU YAU shi ne shugaban kungiyar masu siyar da kaji da kwai ta jihar Kaduna, kuma mataimakin shugaban kungiyar masu siyar da kajin ta kasa bakidaya. A wannan tattaunawar da LEADERSHIP A YAU ya yi ma na bayani ne a kan dalilansu na kafa kungiyar, alheran da ke cikin sana’ar, manyan kalubalen da suke fuskanta a kan sana’ar da sauran al’amurran da suka shafi sana’ar ta su. Ya zanta ne da wakilinmu UMAR A HUNKUYI. A sha karatu lafiya:

Manufofinmu da kafa wannan kungiya ta masu siyar da Kaji da kwai:

Babbar manufarmu da kafa wannan kungiya shine mu san kanmu da kanmu, mu kuma kara tsarkake wannan sana’ar tamu, domin duk wata sana’a da ka sani akwai batagari a cikinta, to domin haka da kuma inganta wannan sana’a tamu ne ya sanya muka ga ya kamata mu kafa wannan kungiya tun a mataki na Jiha har ta bunkasa zuwa mataki na kasa baki-daya. Kafa kuma wannan kungiya ya samar mana da yaukaka zumunta, domin duk wata harka da ka sani to babu abin da ya fi karfafa zumunci da sanin juna alheri a cikinsa.

A yanzun da kafa wannan kungiya, mun sami nasarar, da za a ce a yau na sauka a Jihar Katsina, alhalin ban san kowa ba, ni ne ko wani mambanmu misali daga nan Jihar Kaduna, ya kasance kuma yana neman wani taimako, to idan har na kira shugabannin kungiyarmu a can Jihar ta Katsina na shaida masu cewa ga wani mambanmu nan yana cikin halin neman a taimaka masa, to tabbas za su taimaka masa. To hakanan idan mamban kungiyar masu siyar da Kaji ne daga Enugu ya zo nan Kaduna, alhalin bai san kowa ba, to zai ji tamkar yana gidan babansa ne. Haka wannan zumuntan take a tsakaninmu a duk inda muke a sassan kasar nan a dalilin kafa wannan kungiyar.

Kungiyarmu tana da cikakken Rajista:

Kungiyarmu tana da cikakken Rajista, hatta kungiyar masu siyar da Kaji ma ta Anguwa tana da rajista, hakanan a mataki na kasuwanni, kananan hukumomi, jiha da kuma kasa baki-daya.

Matakan da mu ke dauka domin koran batagari:

Matakan da muke dauka domin koran batagari da tsarkake wannan sana’ar tamu, daga ciki akwai duk inda ka zo da Kaza, sai an tabbatar da cewa, tabbace daga gonarka ne ka zo da Kazar nan. Domin an fi samun kalubale daga irin batagarin yaran nan na cikin Anguwa masu debo kamar su Kaji Talo-talo da misalin su tantabaru haka. A duk inda yaro ko wani ya zo da irin su haka za ka taras mambobinmu ba sa saye, har sun sami tabbacin daga inda ya zo da su na halaliya ne. A bisa kwarewar ma da muke da shi a kan sana’ar, a kan sami wanda zai je ya debo misali Talo-talon daga wani waje, ma’ana ya sato su, sai ya kawo wani wajen ya zube su domin ya nuna kamar ai daman na shi ne, to mu masu saye da mun je za mu iya gane cewa wannan talo-talon sabon zuwa ne, kawo shi aka yi ba a nan ne wajen kwanan sa ba, akwai ayar tambaya a kansa. To da irin wannan da kuma sauran su ne muka samu hadin kai a tsakaninmu na kara tsarkake sana’ar tamu da raba ta da batagari.

Karin kiran da na ke yi ga ‘ya’yan kungiyarmu:

Ina kuma kara janyo hankalin dukkanin ‘ya’yan kungiyar masu siyar da Kaji tun daga mataki na Jiha har na kasa, a duk inda mutum yake sana’arsa ya ji tsoron Allah, domin muddin ka rike gaskiya da amana, tabbace za ka kai matakin da ba ka taba tunanin kaiwa ba, a kuma kowace irin harka ce kake yi za ka cimma nasara.

Ga wani sirri da ya kamata masu siyan Kaji su sani:

Akwai abin da ke faruwa a duk lokacin wasu bukukuwa na musamman, kamar lokutan Sallah ko bukukuwan Kirsimati da makamantansu. Za ka ga kananan masu gonakin Kaji ko irin mata da sauran masu kiwon kajin a cikin gida haka, suna fito da Kajin layi-layi, kwararo-kwararo, suna saidawa. Amma akwai abin da ilimin masu saye bai kai ba, domin za ka ga mutum idan ya sayi Kaza a irin wadannan wuraren a kan naira 1,500, to in Allah Ya so idan har da zai zo kasuwa sai ya sayi wannan Kazar a kan naira 1,200 ko ma kasa da hakan.

Dalilin tashin farashin Kaji a lokutan Sallah da sauran bukukuwa:

Ko da kake jin ana cewa farashin kaji misali ya tashi a irin wadannan lokutan, to mutum bai shigo kasuwa ba ne, a irin wadancan wurare na wajen kasuwa na kan sha mamaki, domin Kazar da zan ji ana siyan ta a kan naira 2,000, sai na ga ni na je na siyo ta a manyan gonaki a kan naira 1,100 ko ma 1,050, wacce ni zan zo na siyar da ita a kan kasa da 1,500. Amma saboda rashin sani, sai mutane suke ganin kamar siyan a wajen kasuwa ya fi sauki, wanda sam abin ba haka yake ba. Ko mai zafi a lokutan bukukuwan na Sallah da makamantan hakan, in ka zo cikin kasuwa za ka sami Kaza daga 800, 900, 1,000 ko 1,100 mai kyau lafiyayya da za ka kaiwa iyalanka ku sha shagalin Sallah ku yi walwala da ita.

Kalubalen da muke fuskanta:

Babban kalubalen da muke fuskanta a wannan sana’ar shi ne kamar na irin wannan lokacin, za ka ga daga lokacin da aka ce maka Sallah ta karato, za ka ga ‘yan ta yi dadi sun zo sun yi cunkoso a cikin sana’ar, wanda wannan lokaci ne da mai sana’ar ya ke sa ran dan samun wani abu a cikinta, amma sai ka taras wadanda ba sana’ar su ne ba, sun shigo sun yi kaka-gida a cikinta saboda albarkan da sana’ar take da shi. Amma idan kasuwa ta koma daidai a lokutan da ba a gudanar da bikin komai, to sai fa abin da ake cewa, “In ruwa ya baci sai kwarawan asali,” to sai dai kuma ‘ya’yan halas masu sana’ar. To wannan shi ne babban kalubalen da muka fi fuskanta.

Nasarorin da mu ka samu a wannan sana’ar ta siyar da kaji:

Batun nasarorin da muka samu a cikin wannan sana’a tamu ta siyar da Kaji, Alhamdu lillahi, wannan sana’a ce wacce take da dimbin albarka, idan za mu kwana da kai a nan ina lissafa maka nasarorin da muka samu a cikinta ba za su kare ba. Domin wannan sana’a ce mai albarka, ko kana da jari, ko ba ka da jari, tabbas za ka ci abinci a wannan sana’ar.

In ka duba ko a cikin gari za ka ga wasu matasa ko dattawa suna yawo da kajin ko a Kwando ko makamancin hakan, suna zagayawa suna siyar da Kajin, wanda kila an dora masu su ne a kan naira 1,000 ko 1,050, su kuma su dan dora wani abu a kai sai ka ga sun sami wani abu. Wani kuma ma adalci da dilolin Kajin su ke yi, za ka ga in sun dora maka ka zaga ba ka sayar da komai ba, to in ka dawo za su taimaka maka da dan abin da za ka yi cefane, domin su karfafa ka, ka ji dadi gobe ma ka dawo.

Kirana ga matasa:

A nan ne kuma nake yin kira ga matasa da ma kowa, da kar matashi ko wanin sa ya raina karamar sana’a, domin daga karamar sana’ar ne ake tashi a zama babba. Matukar dai kana son yin wannan sana’a tamu ta siyar da Kaza, har ka zo ka same mu, duk da ba za mu iya daukar ka ba hakanan kai tsaye har sai ka zo mana da wani fitacce da zai tsaya maka, da hotonka, da inda kake da zama, domin Duniya ba ta lalace ba, a kullum ma ado a ke kara ma ta, sai dai yanayin al’ummar da ke cikinta na wasu da ta gurbata. Domin haka ne har sai ka zo mana da mai tsaya maka, sai mu jarraba ka, mu dora ma ka kaya, domin wani zai iya daukan Kaji ko da guda Talatin ne, in a kan 1,000 ne, ka ga 30,000 kenan, to in babu taka-tsan-tsan, wannan ya wuce bai dawo ba, ka ga babu inda za mu samo shi kenan. To kan hakan ne mu ke cewa sai ka kawo mai tsaya ma ka, inda ka ke da cikakken adireshinka.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: