Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Aka Gudanar Da Sallar Idi A Unguwar Maje Dake Faskari

Published

on

A ranar Lahadin da ta gabata ne al’ummar Musulmin Najeriya da na duniya bakidaya su ka gudanar da sallar idin Babbar Sallar wannan shekarar ta bana kuma al’ummar Musulmin su ke cigaba da gudanar bukukuwan sallah a daidai wannan lokaci, haka ma a garin Unguwar Maje da ke karamar hukumar Faskarin jahar Katsina, al’ummar Musulmin unguwar su ka gudanar da tasu sallar idin a ranar Lahadin da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sallar idin wadda ta gudana a harabar makarantar firamare da ke garin Unguwar Maje a karkashin jagorancin shugaban kwamitin masallacin Juma’a na ’yan izala Malam Sabiu Lawan Unguwar Maje, ta samu halartar al’ummar Musulmin wannan yanki na garin Unguwar Maje da kewayenta bakidaya.

Manyan malamai a wajen sallar idin sun haDa da Malam Sabiu Lawan, shugaban kwamitin gudanar da ayyuka na musamman na masallacin juma’ar garin Unguwar Maje, da limamin Juma’a Malam Ibrahim Lawan Unguwar Maje da Malam Abdulmumini Mati Unguwar Maje da Malam Muhammadu Lawan Unguwar Maje da sauran makamantansu, masu unguwannin Unguwar Maje; Mai Unguwa na daya Malam Abdulhadi Isah da Mai Unguwa na Biyu Malam Labaran Bakanike.

A hudubarsa ga al’ummar Musulmi a wajen sallar idin, limamin masallacin Juma’a na garin Unguwar Maje, wanda shi ne ya jagoranci sallar idin Malam Ibrahim Lawan Unguwar Maje, ya cigaba da cewa ne al’ummar Musulmi a ko’ina su ke su cigaba da jin tsoran Allah a wajen gudanar da al’amuransu na yau da kullum tare da koya ma na bayansu kyawawan ayyuka na alkhairi, domin neman samun nasarar amincewar ubangiji a wajen cigaba da zaunar da Najeriya lafiya da duniya bakidaya.

A jawabinsa ga al’umar Musulmin Unguwar Maje, daya daga cikin malamai da su ka halarci sallar idin, Malam Abdulmumini Mati, ya ce, wajibi ne iyayen yara su cigaba da koya wa ’ya’yansu tarbiya tagari da kuma gudanar da ayyukan alkairi domin su ma idan sun taso su koya wa na bayansu kyawawan ayyuka nagari da tarbiyar addinin Musulunci a kowane lokaci domin samun zuri’a tagari wadanda za su cigaba daukaka kalmar Allah.

A cigaba da jawabinsa ga al’umarsa na unguwar Maje mai unguwa na daya Abdulhadi Isah unguwar Maje yaci gaba da jawabine kamar haka matasa su zama jakadu na gari a dukkan al’amuransu na yau da kullun, sannan kuma su zama masu koyan tarbiya ta gari a kowane lokaci a matsayinsu na yara manyan gobe kuma shuwagabannin jibi, anasa jawabin a wajen sallar idin mai unguwa na biyu M. Labaran Bakanike unguwar Maje bayan ya gode ma Allah ubangiji subahanahu wata alah a wajen ganin wannan lokaci na gudanar da sallar idin wannan shekarar ta bana yayi kira ga matasane musamman masu tukin Babura da motoci da suyi tuki a cikin natsuwa domin kaucewa haddurran dake sanadiyyar zuwan wasu asibitoci wasu ma su zarce zuwa lahira injishi da fatan Allah yak are al’umar musulmin Najeriya dana duniya bakidaya.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!