Connect with us

RAHOTANNI

Gidauniyar Gajjiya Charity Ta Kaddamar Da Koya Wa Almajirai Sana’o’i A Nasarawa

Published

on

A jiya Alhamis ce, Gidauniyar Gajjiya Charity ta gudanar da gagarimin taro a kan hanyoyin da za a bi a hana almajirai barace-barace a kan tituna ta hanyar koya musu sana’o’i.

Gidauniyar ta yi taron ne a wata tsangaya da ke anguwar Katsinawa cikin garin Maraba ta Jihar Nasarawa. 

Da take jawabi a wajen taron, shugaban Gajjiya Charity Foundation, Hajiya Hafsat Umar Gimba, ta bayyana cewa, makasudin kaddamar da koyon sana’o’in shi ne, a samu yadda za a yi a taimaka wa almajirai domin su daina barace-barace a kan hanyoyin kasar nan.

Ta kara da cewa, “Mun lura akwai wani hali da musulmai suke ciki a zamanin nan wanda suke bukatar taimako, kuma wannan hali shi ne, halin barace-barace da almajirai suke yi a kan tituna.

“Gidauniyar ta fara gudanar da irin wannan yunkuri a Jihar Yobe, inda daga nan ne ta garzayo har zuwa garin Keffi, sannan ta zo wannan gari na Maraba. Duk inda gidauniyar ta gudanar da irin wannan taro, to sai a ce mata babban makasudin da ke sa almajirai barace-barace a kan tituna shi ne, rashin abinci da kuma rashin sana’ar yi ga almajiri. Sai muka duba muka gani ta hannoyin da za mu iya taimaka wa almajiran, domin shi almajiri an mayar da shi mara gata. 

“Gidauniyar ta yi kokarin wajen koya wa almajireai sana’a, inda ta fara koya wa almajirai guda goma sanar dinki. Mun yi kokarin bude musu shago tare da saya masu kekunan dinki da kuma na zabi.

Shugaban ta ce, idan an ce almajiri ya koyi sana’a, ba wai an ce ya bar karatu ba ne, sai dai domin ya taimaki kansa. Dole wata rana almajiri ya gama wannan karatu, kuma yana bukatar yin aure, to dale zai nemi wata sana’ar yi domin ci da iyalinsa da kuma shi kansa.”

Ta kuma kara da cewa gidauniyar takan fuskanci wadansu matsarori daga wurin malaman tsagaya wadanda ba su fahimci muradin wannan kungiya ba, inda a wasu wuraran ba sa samun hadin kai malaman da kuma na almajiran. 

Daga karshe ta yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa wadanda ba su da shi, sannan kuma ta yi kira ga shuwagabanni da su tallafa wa wannan kungiya wajen ganin ta cimma burinta na dakile barace-barace da almajirai suke yi a kan tituna.

Malam Muhammed Idris Ibrahim, babban limamin masallacin Juma’a na Zulaihat da ke yankin Kubwa a garin Abuja, shi ne ya gudanar da jawabi a wurin wannan taro.

Malamin ya yi bayani dalla-dalla tun daga inda aka samo kalmar almajiranci a cikin addinan musulunci.

Malam Muhammed Idris Ibrahim ya fadakar da mahatta taro irin illoli da barace-barace suke haifarwa a cikin al’umma. Malamin ya ja kunnen mahaifan yara masu tura ‘ya’yansu karatun zuwa wani gari ba tare da ba su wani guziri ba, ko kuma tallafawa su malaman masu karantar da yaran. Ya kara da cewa, karatu ba ya yuwuwa sai da wata sana’a, domin gujewa fadawa cikin halin rogo ko kuma maula.

Ya ce, yana da kyau almajirai su samu wata hanya ta rike kansu ba tare da suna zuwa bara ba. Ya bayyana cewa, wannan kungiya ta taka muhimmiyar rawa wajen kokarin yaki da barace-barace da almajirai ke yi a kan tituna.

Malamin ya yi kira ga almajiran da su maida hankali wajen karatunsu da kuma wajen koyan sana’o’in da wannan kungiya ta daura su a kai.

Ya kuma bukaci almajiran da su dunga karfafawa malamansu gwarin giwa tare da jin tsoron Allah a kan karatunsu da sanarsu. Sannan ya yi wa shawagabannin wannan kungiya fatan alkairi tare da yi musa addu’a a kan abin da suke so su cimma. 

Taron ya samu halattar maza da mata da almajirai masu yawa da kungoyi da dama da kuma daukacin al’ummar garin Maraba, wanda suka hada da babbar limamin garin Maraba da na’ibinsa da mai unguwa da dai sauran su.   
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: