Connect with us

KASASHEN WAJE

Taron G7 Zai Tallafa Wa Yaki Da Gobarar Amazon Da Yuro Miliyan 25

Published

on

Shugabannin kasashe masu karfin arziki sun amince su samar da miliyoyin yuro don taimakawa yaki da gobarar nan da ke cin kungurmin dajin nan na Amazon da ke kasar Brazil.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce taron kasashen bakwai ya dau hanyar kauceea samun rigima dangane da shirin makamashin nukiliyar kasar Iran. Yayin wata ganawa da manema labarai a taron a kasar Faransa, Angela Merkel ta ce bakin shugabanni ya zo daya kan cewa Iran ba za mallaki makaman nukiliya ba, kuma Amurka ta yi marhabin da shirin tattaunawa tsakanin kasashen Turai da Iran.

A bangare guda kuwa, shugabannin kasashen sun amince da samar da yuro miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 22, don taimaka wa yaki da gobarar nan da ke cin kungurmin dajin nan na Amazon. Kaso mafi tsoka daga kudaden dai, za su tafi ne wajen aikawa da jiragen da za su gudanar da aikin kashe wutar, a cewar wata majiya daga fadar shugaban kasar Faransa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: