Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kotu Ta Nemi Minista Da EFCC Su Gurfana Gabanta Kan Kadarorin Yari

Published

on

Babban Kotun tarayya da ke Abuja, ta umurci Babban Lauyan gwamnatin Tarayya (AGF) da kuma Hukumar yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zakon kasa (EFCC) da su gurfana a gabanta a ranar Juma’a dangane da batun shari’a da kuma wasu batutuwan da su ka shafi kadarorin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulazeez Yari.
Mai Shari’a N. Maha shi ne ya yi wannan umurnin a lokacin da ke sauraron bukatar Lauyan tsohon Gwamnan, Mahmud Magaji, SAN.
Bukatar wacce aka mata alami da FHC/ABJ/CS/948/2019, an gabatar da ita ka bisa dogaru da sashi na 46(1) da (3) da ke kundin tsaron dokokin kasa na 1999 da kuma odar doka ta 3 da 4 na kare hakkin xan adam (tsarin tursasawa) na dokar 2009.
Mai Shari’a Maha ya kuma umurci a riskar da waxanda ake kara da wannan umurnin na kotu cikin awanni 48 kana su kuma gurfana a gabansa a ranar Juma’ar wannan makon.
Waxanda a ke kara dai su ne babban Lauyan gwamnatin tarayya da kuma hukumar EFCC.
A karar da Yari ga gabatar mai sakin layi 17, ya zargi waxanda yake kara da zalumtar shi haxi da wasu iyalan gidansa a kan al’amuran siyasar jihar Zamfara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!