Connect with us

WASANNI

Lukaku Ya Ce Ba Ya Fatan Koma Wa Manchester United

Published

on

Rumelu Lukaku, wanda ya bar Manchester United a watan da ya gabata ya bayyana cewa ba ya tunanin akwai lokacin da zai zo wanda ya yi sha’awar tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United, saboda ba su yi ma sa adalci ba.

A kwanakin baya ne tsohon dan wasan gaban a Manchester United, ya caccaki kungiyar da masu zargin cewa bashi da kwarewa inda ya ce tunda tsofaffin masu koyar dashi suka amince cewa yana da kwarewa dole kowa ya hakura.

Lukaku dai ya kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ne a watan Agustan daya gabata wanda hakan ya kawo karshen zamansa a Manchester United na shekara biyu kuma fam miliyan 74 Inter Milan din ta biya.

Sai dai tun bayan barinsa kungiyar tsohon dan wasan Manc0

 inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya iya zura kwallo a raga sai dai kuma bashi da wayo bai iya kula da jikinsa ba.

Amma Lukaku, wanda ya zura kwallo a wasansa na farko a sabuwar kungiyarsa ya bayyana cewa idan aka duba sunayen masu koyarwar da suka yabeshi tabbas za’a tabbatar da cewa abinda Garry Nebille yake fada ba gaskiya bane.

“Bana tunanin akwai wani lokaci da zaizo in inji inason komawa Manchester United saboda kana sha’awar komawa waje ne idan har kayi zaman lafiya kuma kun rabu lafiya da masu wajen amma ni bamu rabu cikin salama ba” in ji Lukaku

Ya cigaba da cewa“Bai kamata a gayamin cewa bani da kwarewa ba saboda duk abinda yakamata inyi domin ganin na taimaki jikina nayi kuma duk surutun da akeyi ina gida ina daukar horo ni kadai domin tabbatar da lafiya ta” in ji Lukaku

Ya kara da cewa “Zai iya sukar yanayin jikina da kuma yanayin daukar horo na amma ba zai iya sukar yanayin yadda nake girmama kungiya ba da kuma halin kwarewa da nake nunawa a kullum”

A karshe Lukaku yace abinda kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer yafada gaskiya ne domin akwai lokacin da kake bukatar barin wajen da kake domin ganin cigabanka kuma haka shi ma ya yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: