Connect with us

RAHOTANNI

Masarautar Kagara Ta Koka Kan Rashin Tsaro Da Damun Al’ummarta

Published

on

An nemi gwamnatin Neja da jami’an tsaro da su kawo karshen hare-haren barayin shanu da masu garkuwa da mutane da suka addabi al’umomin karkarun da ke kananan hukumomin Rafi da Shiroro.
Mai martaba sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko ne ya yi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar sa ranar alhamis din da ya gabata lokacin da yake karban bakuncin ‘yan gudun hajira da suka fito daga gundumomin masarautar Kagara da Minna da ke makota ka da juna.
Sarkin ya cigaba cewar yanzu haka a kullun muna samun bakuncin ‘yan gudun hijira da suka baro garuruwansu na zama inda suka rike noma da kiwo a matsayin madogarar rayuwa. Amma ‘yan ta’adda sun addabe su da hare-haren satar mutane dan garkuwa da su ana karban kudin fansa bancin dabbobin su da abincin da suka tanada ana awon gaba da su.
Yanzu haka harkokin noma na shirin tsayawa cak wanda idan aka yi wasa lallai sai an yunwa nan gaba, ya kamata gwamnati da jami’an tsaro su kawo mana dauki kafin abubuwan su kara dagulewa. Mata da kananan yara da dama sun bace a daji wadanda suka samu dama sun tafiyar awanni kafin su iso Kagara, yanzu rahotanni suna tabbatar mana da cewar akwai sansanin wadannan ‘yan ta’addan kilomita hudu kafin ka shigo nan cikin gari, ka ga ke nan in har ta tabbata ko mu da ke cikin gari ba mu tsira ba.
Ya kamata maigirma gwamna ya tabbatar ya dakile wadannan munanan abubuwan da ke faruwa, yanzu lokacin aikin gona ne, kuma an hana mana zuwa gonakinsu wanda shi ne ginshikin cigaban masarautar nan, masarautar Kagara da Minna na rokon gwamnati da ta kawo dauki cikin lokaci.
Ko a watannin baya da jami’an soja suka aiwatar da shirin samamen daji, masarautar ta roki gwamnati da a samar da barikin soja tsakanin Kagara da Birnin Gwari na jihar Kaduna dan tsoron abinda yake faruwa yanzu kar ya faru.
Jama’a dai da dama da suka fito daga kauyukan Kukoki, Madaka da Hana Wanka, Tudun Natsira, Wayam da sauran su na ta kara kwarara zuwa cikin garin Kagara duk da rashin tallafin gwamnati na abinci da wurin kwana.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: