Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Borno Za Ta Yi Amfani Da Mafarauta 10, 000 Wajen Fatattakar Boko Haram

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta fara gudanar da aikin daukar mafarauta kimanin 10, 000 don su taimakawa jami’an tsaro Nijeriya wajen yaki da matsalar tsaron Boko Haram, wadda ta dade tana addabar a jihar da ma arewa maso gabas baki daya.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna yadda ya kagara ya ga matsalar ta kau, tare do kokarin lalabo karin wasu sabbin hanyoyin da zasu taimaka wajen kawo karshen matsalar domin kowa ya huta da alakakai.

Wata kwakkwarar majiya da ke kusa da gwamnatin jihar Borno, kana da rundunar Cibilian-JTF, ta shaida wa wakilin mu aniyar gwamnatin jihar wajen daukar kyafaffun mafarauta 10,000 don wannan aikin. Wanda a halin da ake ciki yanzu kimanin mafarautan 2,000 sun shiga Maiduguri, wadanda suka fito daga sassan arewacin Nijeriya da kasashen da ke da makwabtaka da ita, wadanda kuma suka shirya tsab domin shiga surkukin dazuzzuka don farautar mayakan tare da sojoji.

Majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunan ta, ta kara da cewa, “Mafarautan, wadanda suka hada da dafaffun yan-tauri, wadanda bindiga ba ta cin su balle kuma karfe.

“Ina ganin an gudanar da daukar mafarautan ne a asirce, amma kuma dole lamarin ya fito fili ganin yadda aikin zai dauki lokaci yana gudana sannan kuma da yadda gwamnan ya kudiri aniyar yin amfani da wadannan gagararrun mafarautan, akalla 10,000 wanda ba zai yuwu ya gudana a boye ba, dole sai jama’a sai sun sani”.

Ilai kuwa, a yan kwanakin nan, jama’ar birnin Maiduguri sun shaidi yadda bakin fuskokin mafarauta dauke da bindigogin gargajiya (durum-kange), wukake da adduna da sauran kayan fada ke gauro -mari tare da yi wa birnin tsinke.

Wata majiyar kut-da-kut da gwamnati ta bayyana yadda Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya kagara wajen kawo karshen matsalar tsaron Boko Haram, wadda ta ki ta ki cinyewa yau kimanin shekaru 10 da suka gabata.

Ta ce, “Saboda ita ma rundunar sojojin Nijeriya ta shelanta neman hadin gwiwa da jama’a wajen kawo karshen Boko Haram. Wanda kuma kowanen mu ya yi marhabin da kikarin da yan Civilian-JTF suka bayar a yaki da Boko Haram.”

Wata majiyar ta ce, “Kuma mafi yawan mafarautan an gayyato su ne daga jihohin arewacin Nijeriya ne, saboda yadda su ne zasu fi saukin fahimtar al’adu da yanayin mutanen wannan yanki na jihar Borno”. In ji shi.

A hannu guda kuma, sojoji ne ke gudanar da aikin tantance mafarauta/ yan-tauri, kafin a basu kayan aiki. “wanda ana kammala tantance su, nan take sai gwamnatin jihar ta basu kudaden su na alawus tare da motocin aiki, wanda daga nan sai fita fagen fama tare da sojojin”.

“Sannan yanzu haka sai tururuwa suke yi zuwa Maiduguri, saboda an nemo su daga Taraba da Yola. Yayin da wasu kuma daga jihohin arewa maso gabas, wasu kuma daga jihar Nijar, don su zo su hadu da takwarorin su da ke nan Borno da Yobe.”

A farkon watan Junairun wannan shekara gwamnatin jihar Borno ta dauki mafarauta 500 don taimaka wa sojoji yaki da Boko Haram.

A cikin watan Yuni, a lokacin da babban hafsan sojojin Nijeriya, Yusuf Tukur Buratai ya kawo wa Gwamna Zulum ziyara ta musamman, gwamnan ya bukaci sojojin da su bai wa mafarauta da yan sa-kai horon dabarun yaki da matsalar tsaron Boko Haram.

Wanda Buratai ya yi maraba da wannan shawarar, tare da cewa a shirye suke, matukar gwamnati za ta iya zakulo hazikan mutanen da zasu aiki tare.

A hannu guda kuma, mai magana da yawun gwamnan jihar, Malam Isa Gusau, ya bayyana cewa ba zai ce komai ba dangane da lamarin tsaro “saboda yanayin tsaro”. Amma kuma ya ce, “tuni Gwamna Zulum ya dauki matakin lalabo wasu sabbin matakan yaki da matsalar Boko Haram”.

“Yau shekaru 10 da jihar Borno ke dandana kudar ta a hannun matsalar tsaro. Kuma a kokarin da Gwamna Zulum ke yi, hadi da dattijai masu ruwa da tsaki tare da sarakunan gargajiya, sun kagara matuka wajen nemo kowace hanya wadda bata saba doka ba don ganin bayan wannan matsala”.

“Kuma har kullum Gwamna kokarin sa shi ne ya ba sojojin Nijeriya goyon baya. Ya kuma kara kudin alawus din yan Cibilian JTF, mafarauta da yan sa-kai. Kana da basu motoci da kayan aikin da suka doshi 200, don ci gaba da yaki da matsalar tsaro”.

A nashi baren kuma, shugaban da ya jagoranci tawagar mafarautan zuwa birnin Maiduguri, Abdulkareem Umar, dan kimanin shekara 69 a duniya, wanda aka fi sani da sunan ‘Baba-Maigiwa’.

Baba Maigiwa shi ne wanda ya jagoranci taimaka wa gwamnatin Isa Yuguda a Bauchi murkushe tada kayar bayan da Boko Haram a shekarar 2009. Inda kuma ya ce sun kai su 700 a tawagar su.

“Yau mun doshi mako guda a nan, kuma da dama daga cikin mutanen mu sun tafi jihohin su domin yin ban-kwana da iyalan su, wanda yanzu haka suna kan hanyar su ta dawowa zuwa birnin Maiduguri, a zancen nan da nake yi da kai yanzu”. In ji shi.

“A karkashina kawai, akwai kimanin mazaje 5000 wadanda zasu tattaro zuwa birnin Maiduguri, a yan kwanaki kadan masu zuwa. Kuma yanzu haka muna ci gaba da tattaunawa da mafarauta daga kasashen Kamaru, Burkina Faso, jamhuriyar Niger, Afrika ta Tsakiya, da sauran wasu da dama a nan cikin jihohin Nijeriya”.

“Yanzu gashi mun zo saboda yadda Gwamna ya kagara ya ga karshen rashin hankalin abinda ake kira Boko Haram”. Ya nanata.

“Yau kimanin shekaru biyar da suka wuce, mun zo nan Maiduguri a kashin kan mu, da niyyar kutsa kai zuwa dajin Sambisa don mu fafata da Boko Haram, sai dai kash, ba mu samu goyon bayan gwamnati da sojoji ba, kuma a matsayin mu na yan kasa masu mutunta doka, ya sa muka dakata”.

“Amma a wannan jikon, wannan shi ne lokacin da muke jira, saboda yadda Gwamna Zulum ya bukace mu don mu zo mu taimaka wa sojoji tare da sauran jami’an tsaro a yaki da matsalar tsaro”.

“Yanzu haka, an bamu motoci kirar Toyota Hilud guda 10, wadanda aka rubuta Mafarautan Mai-Giwa a jikin su, kuma wadanda gwamnatin jihar Borno ta bayar da su don mu yi aiki dasu, amma mun sheda wa gwamnati cewa muna bukatar Hilud 30 ne, saboda yadda adadin mafarautan suke da yawa. Kuma da zaran komai ya kammala, a cikin yardar Allah, wannan lamarin zai koma tarihi- In Sha Allahu Azeem”!
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: