Connect with us

LABARAI

Farfesa Kabir Bala Shi Ne Sabon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zariya

Published

on

Farfesa Kabiru Bala ya zama sabon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya. Malam Adamu Fika wanda yake shi ne shugaban hukumar gudanar da jami’ar shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Fika ya ce Farfesa Bala ya doke ‘yan takara 10 ne a zaben da aka gudanar a ranar Laraba a Kaduna. Inda ya kara da cewa sabon shugaban zai kwashe shekara biyar ne kamar yadda doka ta tanada, wanda zai fara daga 1 ga watan Mayun 2020.

Rahotanni sun nuna cewa da farko mutum 18 suka nemi kujerar inda daga bisani bayan tantancewa mutum 11 suka yi takarar.

Kabir Bala, Farfesan gine-gine ne, kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban Jami’ar a bangaren gudanar da mulki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: