Connect with us

LABARAI

Gobe Jami’ar Tarayya Ta Gusau (FUG) Za Ta Karrama Dauda Lawal

Published

on

A gobe ne Jami’ar Tarayya dake Gusau a Jihar Zamfara za ta karrama Dr. Dauda Lawal Dare.

Jami’ar za ta karrama shahararren dan siyasa, kuma gogaggen dan kasuwan ne sakamakon irin ayyukan bunkasa jami’ar da ya yi. Wanda suka hada da gina titi a cikin jami’ar, gina babbar kofar jami’ar, da kuma wurin tsayawar motoci ‘bus stop’.

Idan dai ba a manta ba, Dr. Dauda Lawal wanda tsohon Daraktan bankin ‘First Bank’ ne ya jima yana gina azuzuwa, dakunan kwanan dalibai, da muhimman wurare a jami’a da manyan makarantun jihar Zamfara.

Jami’ar FUG za ta yi wannan karramawar ne a ranar yaye dalibanta karo na farko. Taron da zai samu halartar muhimman mutane irinsu Sarkin Musulmi, gwamnonin Sakkwato, Kaduna, Bauchi da dai sauransu.

Bayanin wannan taro da karramawa ya fito ne daga bakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Magaji Garba a shekaran jiya. Inda ya ce, jami’ar za ta yaye dalibai 794. 12 daga cikinsu sun kammala da mataki mai daraja ta farko, 258 sun kammala da mataki mai daraja na biyu, sai kuma 222 suka kammala da matakin digiri na uku.

Farfesan ya ce, mutanen da za a karrama sun yi wa Jami’ar FUGA goma ta arziki, musamman wurin ganin bunkasar jami’ar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: