Connect with us

Da dimi-diminsa

Za A Rataye Maryam Sanda Sakamakon Kama Ta Da Laifin Kashe Mijinta

Published

on

Wata kotun tarayya dake Maitama a Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da aka sameta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Mai shari’a Yusuf Halliru ya ce hukuncin wanda ya yi kisa shi ne a kashe shi, a don haka ya yanke mata hukuncin kisa.

Tuni aka wuce da ita zuwa gidan yari na Suleja kafin inda za ta zauna har zuwa lokacin da za a zartas mata da hukuncin.

Kawo babu tabbas ko lauyoyinta za su daukaka kara ko kuma a’a.

Tun da farko Maryam, wacce ta rinka kuka a kotun, ta yi kokarin guduwa daga wurin da wadanda ake zargi suke tsayawa, amma jami’an kotu suka dawo da ita.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: