Connect with us

RAHOTANNI

An Karrama Shugaban Makarantar Sakandiren Ahmadiyya Da Ke Kano A Ghana

Published

on

A ranar Talatar da ta gabata, Jami’ar ‘Crown Unibersity’ da ke kasar Ghana ta karrrama Shugaban Kwalejin Sakadiren Ahmadiyya, Mista Munauwar Ahmad Kayyum, da ke Jihar Kano a Karamar Hukumar Nassarawa.

Wannan Makaranta dai na tsohon tarihi, domin kuwa ta haifar da man-manyan mutane daga cikinta, shi ya sa ma makarantar ta samu karbuwa a fadin wannan kasa da saurannan sassan kasashen Afirka baki-daya.

Wannan taron karramawa, ya samu halartar mutane daban-daban da ya hada da Malaman makarantu da ke Karamar Humumar Nassarawa da ma na wasu Kananan Hukumomin da ke fadin wannan jiha.

Shi ma Babban Sakatare mai kula da Makarantu masu zaman kansu a Jihar Kano, Alhaji Musa Abba Dankawu, ya samu halartar wannan gagarumin taron karramawa. Sa’annan Sakaren Ilimi na Karamar Hukumar Nassarawa Alhaji Rabiu Mukhtar, shi ma ya samu halartar wannan taro, domin taya Mista Munauwar Ahmad Kayyum, murnar samun wannan lambar girmamawa ta Digirin-digir-gir. Har ila yau, Sardaunan Gama, Alhaji Baba Lawan na daya daga cikin masu taimakawa harkokin ilimi da ke karamar Hukumar Nassarawa, shi ma ya halarci wannan gagarumin taro. Sai kuma, Kungiyar iyayen yara (PTA), su ma ba a bar su a baya ba, wajen halartar wannan taro.

Har wa yau, an fara gudanar da wannan taro ne, tun misalin karfe tara da rabi na safiyar ranar Talata, inda a ka gudanar da jawabai daban-daban kafin mika wannan lamba ta girmamawa ga Shugaban Makarantar. Kazalika, Sardaunan gama, Baba Lawan ya shi ne ya fara bayani ta hanyar bayyana matukar jin dadinsa da wannan karramawa da aka yi wa Mista Kayyum, “ko shakka babu, an yi wannan karramawa bisa cancanta, duba da irin gudunmawar da yake baiwa harkokin ilimi a wannan makaranta da sauran makarantun da suke wannan Karamar Hukuma ta Nassarawa.”

Daga nan ne kuma, sai ya yi kira ga sauran Shugabannin Makarantu Sakadire, da su yi koyi da irin ayyukan alhairi da wannan Shugaban Makaranta ta Ahmadiyya ke yi, domin cigaban al’ummar wannan kasa baki-daya. A karshe kuma, ya yi kira ga dalibai da su kara kaimi wajen ganin sun nemi ilimin Addini da kuma na Zamani.

Shi ma a nasa jawabin, Babban Sakatare mai kula da makarantu masu zaman kansu na Jihar Kano, Alhaji Musa Abba Dankawu, ya bayyyana jin dadinsa da wannnan gagarumin taron karramawa, waddda wannan Jami’a ta yi wa Mista Kayyum, ya ce abin alfahari ne ga mutanen wannan yanki da kuma Daliban wannan makaranta.

Don haka, sai ya yi kira ga sauran Shugabannin Makarantu da su yi koyi da irin abin alhairi irin naShugaban wannnan makaranta, domin cigaban al’ummarsu da kuma ilimin ‘ya’yansu. Sannan, sai ya ja hankalin iyayen yara da su kara mayar da kai akan ilimin yaran nasu.

Shi kuwa sakataren ilimi na Karamar Hukumar Nassarawa, Alhaji Rabiu Mukhtar ya kara da cewa, wannnan karramawa abin alfahari ce ga wannnan Shugaban makaranta da kuma wannan Karamar Hukuma tamu da ma Jihar Kano baki-daya. Sannan, sai ya yi kira ga sauran Abokan aikinsa, musamman Malaman Makarantu da su yi koyi da Mista Kayyum.

A karshe, ya ja hankalin dalibai su cigaba da jajircewa wajen ganin sun samu ilimi kamar yadda Gwamnatin Jihar Kano take ta kira da kuma jan hankalin iyaye wajen tura yara makaranta, domin a cewar tasa da ma wannan shi ne abinda Gwamnatin Kano ta sanya a gaba na bunkasa wannan harka ta ilimi,  karkashin jagorancin mai girma Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na bayar da ilimi kyauta kuma dole.

Su kuwa wadan suka yi takakkiya tun daga Kasar Ghana, Mataimakin Shugaban Jami’ar ta ‘Crown Unibersity’, ya gabatar da jawabinsa a wannan gagarumin taro da kuma dalilin karrama wannan gwarzo, wato Mista Kayyum. Ya ce, sun zabe shi ne a matsayin gwarzo shekara a Karni na ashirin da hudu, saboda irin gudunmawar da ya ke bayarwa a harkokin ilimi da kuma cigaban al’umma. “Babu shakka, Kayyum mutum ne mai hazaka da kuma kokari, yau kusan shekaru talatin da doriya kenan yana hidimta wa l’umma a bangarori daban-daban, musamman harkokin da suka shafi ilimi”, in ji shi.

Sannan, Mataimakin Shugaban Makarantar, ya yi kira ga al’umma da kuma sauran Shugabannin makarantu, su yi koyi da halayen wannnan Shugaban makaranta ta Kwalejin Ahmadiyya. Kazalika, baya ga Mista Kayyum, an kuma sake karrama wasu daga cikin Malaman da ke aiki a wannan makaranta.

Shi kuwa wanda aka shirya wannan taro domin shi, Mista Munawwar Ahmad Kayyum, godewa Allah ya yi da ya nuna masa wannan rana. Ya ce, ba kokarinsa ne ya ba shi wannan dama ba, illa dai kawai yin Allah ne duba da dubban al’ummar da suke bayar da ire-iren wannan gudunmawa a wannan bangare na ilimi a fadin wannan kasa, amma aka zabo shi domin karrama shi.

Haka nan, ya kara da cewa, ba kokarinsa ba ne har da ma na Malaman Makarantar da kuma dalibai da suke ba shi hadin kai da goyan baya, domin cigaban makarantar.

A karshe, ya ja hankalin sauran Malamai irin sa da su hada kai wajen bayar da gudunmawa a dukkanin harkokin da suka shafi ilimi, sannnan ya yi kira ga dalibai da iyayen yara, da su kara zage damtse akan neman wannan ilimi. Haka nan, ya godewa Shugabanin wannan Jami’a ta ‘crown Unibersity’, da suka zabe shi suka kuma ba shi wannan lamba ta karramawa, da sauran dukkkanin Jama’ar da suka halarci wannan taro, kama tun daga kan iyayen yara, ‘yan Jaridu da kuma tsofaffin daliban wannan makaranta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: