Connect with us

Taskar Rayuwa

Abin Da Ya Sa Nake Daukar Nauyin Karatun Marayu Sama Da 200 – Dafta Halima

Published

on

Shugabar Makarantar ‘Farmland Group’, Dafta Halima Usman Abdullahi, wacce aka fi sani da Uwar Marayu ta bayyana cewa, yanzu haka akwai Marayu sama da 200 da ke cikin wannan makaranta tata, wadanda take daukar nauyin karatunsu sakamakon mutuwar iyayensu.

Haka zalika, wannan al’amari ya samo asali ne sakamakon mutuwar wani Bawan Allah mai suna Mallam Rabi’u, wanda ya saba kawo ‘ya’yansa guda biyu akan babur dinsa, sai Allah Ya yi masa rasuwa. Don haka, kasancewar wannan makaranta mai zaman kanta ce  ba ta Gwamnati ba, sannan mai biya wa wadannan yara kuma ya kwanta dama, sai tausayinsu ya kama ni na yanke shawarar cigaba da daukar nauyinsu, wanda hakan ya fara ne tun a shekarar 2005.

Uwar Marayun, wacce da ma can Malamar Makaranta ce, ta bayyana haka ne ga Jaridar Leadership A Yau Juma’a, a wannan mako da muke ciki.  Ta ce, nauyin Marayu biyu na fara nauka, amma daga bisani sai wasu mutane daban suka fara kawo min wasu Marayun ina kuma karba. Daga nan ne kuma, Allah Ya kawo wata qungiya mai suna Gatan-Marayu, wacce ta qunshi Turawa, Larabawa da dai sauran makamantansu masu taimakawa Marayu kai tsaye.

“Bayan sun yi bincike sun gamsu da irin yadda nake nake taimakawa wadannan Marayu daidai qarfina, sai suka nemi  na qara yawan wadannan Marayu a wannan makaranta tawa, domin mu hada qarfi da qafe mu taimaka musu. Wannan a taqaice shi ne musabbabin fara wannan tallafawa Marayu da na fara yi kusan kimanin shekaru 15 kenan da suka gabata, wanda kuma a halin yanzu akwai Marayu sama da 200 da suke samun wannan tallafin karatu kyauta daga wannan Cibiya tawa ta Uwar Marayu a nan Jihar Kano”, in ji Dafta Halima.

Har ila yau ta qara da cewa, baya ga wannan na qananan Yara Marayu, kazalika ta sake bude wata Cibiya da take biyan hayar wurin, wanda ake horar da Mata marasa Mazaje, wadanda masu gidansu suka rasu ake koyar da su sana’o’in hannu, domin dogaro da kawunansu ta yadda za su taimaka wajen tura Marayun da ke hannunsu makaranta cikin tsafta, sakamakon wannan sana’a da suke gurgurawa da ita. Sa’annan, wadannan mata sun kai kimanin su 50 da doriya, kuma su ma kyauta ake koyar da su tare da gudunmawar wasu bayin Allah a wannan Cibiya.

Haka zalika a cewar tata,  yanzu haka akwai  dalibai guda 40 wadanda suka kammala Sakandare, ana kuma nema musu makaranta ta gaba, sai kuma wasu dalibai guda hudu, su ma da suka kammala Jami’a a wannan tsari na tallafawa Marayu.

“Har wa yau, zan so na yi amfani da wannan dama, wajen yin kira ko jan hankali ga Mawadata masu arziqi ba masu kudi ba, da su qara qoqari wajen taimakawa wannan tsari domin kuwa shi Da nakowa ne. Sannan, ka da su gajiya wajen cigaba da aiwatar da wannan abin alhairi. Haka nan, su ma Hukumomi su shiga wannan tsari na tallafawa Marayu a Hukumance.

A qarshe, Dafta Halima Uwar Marayu ta bayyana cewa, babban abinda ya fi ba ta tausayi a cikin wannan aiki shi ne, yadda suka yi jinyar Malama Binta Rabi’u, Uwar Marayu ta farko a wannan Cibiya, wacce ta sha fama da ciwon basir, daga bisani aka ce Ciwon Daji ne (Cancer), wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta. Ko shakka babu, wannan ya yi matuqar ba ni tausayi tare da tayar min da hankali qwarai da gaske. Sannan, babban abinda yake faranta min rai a kullum shi ne, addu’ar da ake yin min ni da Mahaifana a duk inda na samu kaina.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: