Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Risala’

Published

on

Suna: Risala

Tsara Labari: Yakumu M. Kumo

Kamfani: 3SP International Limited

Shiryawa: Auwal Sani

Bada Umarni: Abubakar S. Shehu

Jarumai: Sadik Sani, Rabi’u Rikadawa, Hafsa Idris, Abdu Karkuzu, Tanimu Akawu, Al’amin Buhari, Shu’aibu Lawan, Abubakar S. Shehu, Ahmad Shanawa. Da sauran su.

 

A farkon fim din an nuna Zakariyya (Sadik Sani) a zaune a cikin daji wajen farauta suna cin naman da suka gasa tare da abokan sa su Ma’aruf (Ahmad Shanawa) Suna cin naman da suka gasa cikin nishadi gami da yin wakoki don bayyana farin cikin da suke ciki, a wannan lokacin ne Zakariyya ya shaida musu cewa washe gari zasu koma cikin gari don haduwa da iyayen su.

A hanyar su ta komawa cikin gari ne suka shiga cikin wata gona wadda ke cike da ‘ya’yan itatuwa na marmari, su Zakariyya suka debi kayan marmarin suka ci sannan suka nufi cikin gari. Bayan sun idar da sallah a wani masallaci dake cikin gari sai suka saurari wa’azin limamin masallacin wanda yake bayani akan illar dake tattare da cin hakkin wani dan Adam, yayi bayanin irin hukuncin da ubangiji zai yiwa bawan sa bayan mutuwar sa matukar bai nemi yafiyar bawan da ya ciwa hakki ba.

Jin hakan ne yasa jikin Zakariyya yayi sanyi, bayan sun tashi daga masallacin sai ya bu’kaci abokan sa da suje wajen liman don yayi musu bayanin matsayin kayan marmarin da suka ci a gona wanda ba kyautar sa aka basu ba. Abokan Zakariyya suka ‘ki amincewa da zuwa wajen liman, hakan tasa shi yaje ya samu liman ya gaya masa abinda ke faruwa, anan ne liman yayi masa wasu tambayoyi kafin daga bisani ya tabbatar masa da matukar bai je ya nemi yafiyar mai gonar ba to Allah bazai yafe masa ba tunda ba yunwa ce tasanya shi cin kayan marmarin ba.

Cikin dan lokaci kadan Zakariyya ya koma gonar da suka ci kayan marmari, a sannan ne ya hadu da mai tsaron gonar wanda ya tabbatar masa da cewar ba gonar sa bace, kuma mai gonar yana zaune ne a wani gari mai nisan gaske, jin hakan ne yasa Zakariyya ya tambayi kwatancen garin sai aka fada masa sunan mai gonar wanda ba boyayyen mutum bane.

Lokacin da Zakariyya ya dawo gida ya sanar da iyayen sa halin da ake ciki sai mahaifin sa (Abdu Karkuzu) ya goyi da bayan tafiyar da zai yi don neman gafarar mai gona, mahaifiyar Zakariyya ce bata amince da tafiyar ba don tana tsoron irin dazuzzukan dake kan hanyar zuwa garin mai suna baihan. Amma haka ta hakura ta amince da tafiyar saboda goyon bayan da Zakariyya ya samu a wajen mahaifin sa.

Bayan Zakariyya ya fito cikin shirin barin gari ne sai abokan sa su ma’aruf suka so dakatar dashi, amma sai ya nuna idan suma zasu bishi to hanya a bude take idan kuma ba zasu je ba shi dole zai tafi, nan suka tafi suka ‘kyale shi don sun nuna abinda ya faru ba wani babban laifi bane. Haka Zakariyya ya bar ‘kauyen su ya shiga cikin daji dauke da jakar kayan sa ya nufi hanyar garin baihar don neman gafarar wanda ya ciwa kayan marmari a gonar sa.

Zakariyya yayi nisa a cikin tafiyar sa har ya isa cikin wani gari da tsakar dare, a sannan ne sanyi ya soma kama shi sai ya shiga cikin wani masallaci don neman mafaka, a wannan lokacin ne wasu mutane suka biyo barawo suna ihun neman taimako, bisa tsautsayi sai barawon ya gudu a lokacin da Zakariyya ya fito daga cikin masallaci don ganin abinda ke faruwa, fitowar sa ce tasa mutanen suka kama shi saboda kayan jikin sa irin na barawon da suka biyo ne, nan suka wuce dashi gidan sarki don a yanke masa hukunci, a wannan lokacin ne Sarkin garin (Al’amin Buhari) ya tambayi Zakariyya abinda ke faruwa, nan fa Zakariyya yayi masa bayanin gaskiyar abinda ya sani gami da dalilin shigowa cikin garin su da wajen da ya nufa, jin hakan ne yasa sarkin ya bada izinin a kai Zakariyya dakin ajiya kafin sanda za’a yanke masa hukunci domin an soma fahimtar cewa sahun barawon ya taka.

A cikin dakin da aka ajiye Zakariyya ne yaci karo da wata ‘karamar jaka wadda aka boye gwala-gwalai a ciki, ganin jakar ne yasa ya kawo ta gaban Sarki don neman mamallakin dukiyar. Ganin hakan ne yasa Sarki ya tabbatar da bashi da hannu a cikin abinda ya faru, ana tsaka da neman mai dukiyar ne sai wani bafatake (Abubakar S. Shehu) wanda bai jima da barin garin ba yazo yana cigiyar wannan dukiyar, ganin ya samu kudin sa ne sai yaji dadi har ya nawa Zakariyya kyautar kudi mai tsoka amma sai ya nuna baya bukata shidai burin sa yaje garin baihan.

Jin hakan ne yasa wannan bafatake ya dauke sa suka bar garin da nufin zai kai shi har garin da yake nema domin shima ta can zai bi, nan suka hau dawakai suka tafi, bayan sun yi nisa ne sai suka yada zango a cikin wani daji suna hutawa gami da yin hira, a wannan lokacin ne ‘yan fashi suka kawo musu sumame suka bisu da nufin hallaka su, hakan tasa Zakariyya ya fuskance su aka fafata, bisa tsautsayi sai ‘yan fashin nan suka kashe bafatake, amma kafin mutuwar sa sai ya mallakawa Zakariyya wannan dukiyar gwala-gwalan nasa a matsayin kyauta kuma ya fada masa sunan sa.

Haka Zakariyya yaci gaba da tafiya shi kadai cikin galabaita da wahala har ya isa wani gari inda Abu Zarr da matar sa suke zaune a cikin jeji,  a sannan ne Zakariyya ya fadi ya suma saboda wahala, haka su Abu Zarr suka soma jinyar sa har ya warke sannan suka dora shi akan hanyar garin baihan. Bayan Zakariyya yaci gaba da tafiya ne sai suka hadu da wani ‘kasurgimin dan fashi Gambo (Shu’aibu Lawan) wanda ya tare wata hanya yana zaluntar jama’a gami da kashe duk wanda ba shi da dukiya.

Kishirwa ce tasa Zakariyya ya fadi ya suma a cikin dajin da Gambo yake fashi da makami, ganin Zakariyya a cikin mugun hali sai Gambo ya ba shi ruwa yasha, bayan Zakariyya ya dawo cikin hayyacin sa ne sai Gambo ya ‘kwace dukiyar gwala-gwalan da yake tafe da ita, sannan ya tafi ya bar Zakariyya a wajen. Haka Zakariyya ya tashi ya cigaba da tafiya, yayin da shi kuma Gambo yaci karo da wasu Fulani sun shigo dajin, anan ne ya ‘kwacewa wasun su kudi wadanda basu da kudi kuma yayi musu kisan gilla. Bayan wani dan lokaci sai Gambo dan fashi ya sake cin karo da wasu almajirai wadanda suka fito don zuwa neman ilimi, jin basu da kudi ne sai ya soma ‘kokarin ya hallakasu amma sai suka yi ‘kokarin kare kansu, hakan yasa ya soma amfani da tsafi don ya hallaka su, amma sai suka dage da addu’ar neman tsari a wajen Allah, sai tsafin nasa ya kasa tasiri a kan su, nan suka yi nasarar yi masa mugun duka sannan suka tafi suka bar shi a galabaice. A wannan lokacin ne hanya ta biyo da Zakariyya ta inda Gambo dan fashi ke kwance a ‘kasa, nan Gambo ya roki Zakariyya akan ya kai shi cikin garin su wajen yayan sa, haka Zakariyya ya dauke shi suka nufi garin su Gambo, bayan sun yi doguwar tafiya ne suka tsaya hutawa saboda sun galabaita, a sannan ne Zakariyya yaga wani mutumi yana tafe da jakin sa, sai ya nufi wajen sa ya nemi taimakon ya basu aron jaki zai dora dan uwan sa don zuwa cikin gari, amma sai mutumin yaki amincewa har sai da Zakariyya ya ba shi zinare sannan ya sayar mass da jakin.

Nan Zakariyya ya dora Gambo akan jaki suka shiga cikin ‘kauyen har suka je gidan yayan gambo, bayan zuwan su yayan Gambo ya soma yiwa Gambo magani amma jikin Gambo yayi tsanani nan take ya mutu, bayan mutuwar sa ne fadawan Sarki suka zo don su kama Gambo saboda sun ji labarin shigowar sa cikin gari, amma ganin ya mutu sai suka kama Zakariyya suka tafi dashi gaban sarkin su a matsayin abokin Gambo wanda suke zaluntar al’umma tare, Sarki (Tanimu Akawu) ya soma tuhumar Zakariyya akan zaluntar jama’ar da suke amma sai Zakariyya ya fada musu gaskiyar abinda ya sani, Sarki bai amince da maganar sa ba musamman da yayan Gambo ya kawo jakar dukiyar Zakariyya nan aka soma tuhumar Zakariyya inda ya samu dukiya mai yawa, duk da ya fadi gaskiya amma basu yarda ba aka dinga gana masa azaba har zuwa lokacin da wani Sarki da mutanen sa suka zo ziyartar sarkin wannan gari don taya shi murnar mutuwar gambo, a wannan lokacin ne sarkin da yazo ziyara(Al’amin Buhari) yaga Zakariyya kuma ya tabbatar musu da cewar ba mai laifi bane sannan ya fada musu inda ya samu dukiyar.

Hakan tasa suka nemi yafiyar Zakariyya sannan aka hada shi da dawakai da ‘yan rakiya har zuwa garin baihan da yake nema, bayan zuwan sa ne ya hadu da sarkin garin wanda yazo nema (Rabi’u Rikadawa) lokacin da Zakariyya ya fadi dalilin zuwan sa garin don a yafe masa laifin da yayi na cin ‘ya’yan itatuwa sai sarkin ya’ki yafe masa har sai in ya yarda zai auri ‘yar sa wadda ta kasance miskiniya, jin hakan yasa Zakariyya ya amince aka yi auren aka kawo amarya dakin sa(Hafsa Idris) amma sai yaga ‘kalau take babu abinda ya same ta, a sannan ne amaryar tayi masa bayanin dalilin da yasa mahaifin ta yayi masa haka. Bayan dan wani lokaci Zakariyya da matar sa suka koma ainahin garin iyayen sa dauke  da dukiya mai yawa suka cigaba da rayuwa a can.

Abubuwan Birgewa:

1- An nuna tsantsar jin tsoron Allah gami da jajircewa kan tafarkin gaskiya.

2- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin

3- An samar da kayan aiki masu kyau, sauti ya fita radau.

Kurakurai:

1- Lokacin da bafatake (Abubakar S. Shehu) ya dawo gidan sarki don neman dukiyar sa, me kallo yaji bafataken yace ya baro ayarin tafiyar su a baya shi kuma ya dawo neman dukiyar sa, amma lokacin da Zakariyya yabi bafataken don tafiya garin baihan sai mai kallo yaga Zakariyya da bafatake su biyu kacal akan dawakai ba tare da gayyar ayarin da bafatake ya fada ba, shin ina sauran ayarin suke?

2- Me kallo yaga Zakariyya ya iso garin su Abu Zarr rike da jakar kudin sa kadai ba tare da kuttun ruwan sa ba, amma bayan su Abu Zarr sun yi masa magani a raunikan sa a sanda suke bankwana sai aka ganshi dauke da kuttun ruwan sa wadda ya baro a baya, tunda ba’a nuna cewa su Abu Zarr ne suka ba shi wani kuttun ruwan ba, shin ya aka yi nashi kuttun ruwan da ya baro a baya  ya dawo hannun sa? Ya dace a bayyanawa me kallo yadda hakan ta faru.

3- Lokacin da Zakariyya yaje garin su Abu Zarr rigar dake jikin sa ruwan hoda ce, amma bayan sun yi masa magani a raunikan jikin sa sai aka ganshi dauke da shudiyar riga a jikin sa, a sanda suke  bankwana dasu Abu Zarr kuma sai aka ganshi da ainahin rigar sa ruwan hoda, tunda an nuna wa mai kallo cewa Zakariyya ya baro jakar kayan sa a inda suka yi gumurzu da ‘yan fashi shin a ina ya samu rigar da ya sauya? Idan kuma Abu Zarr ne ya ba shi aron tasa ya dace ko da baki ne a yiwa me kallo bayani don gudun kar a rikita tunanin sa.

4- Lokacin da ‘kasurgumin dan fashi Gambo ya hadu da Zakariyya wanda ke cikin halin suma har ya taimaka masa da ruwa sannan ya ‘kwace jakar dukiyar dake jikin sa, tunda Gambo bai bude jakar yaga abinda ke ciki ba, shin ya aka yi yasan cewa dukiya ce a ciki mai yawa wadda bai taba mallakar irin ta ba? Ya dace Gambo ya fara bude jakar yaga abinda ke ciki kafin ya furta hakan.

5- Bayan Gambo ya ‘kwace jakar kudin Zakariyya ba’a nuna lokacin da ya mayar masa da dukiyar ba, amma sai mai kallo yaga Zakariyya ya ciro jakar a jikin sa ya dauki zinare ya sayi jaki a sanda zai kai Gambo gidan yayan sa, ya dace a bayyana lokacin da jakar ta koma hannun Zakariyya koda ta hanyar fada da baki ne.

6- Lokacin da Zakariyya ya baro garin su an nuna ya shiga cikin wani daki wanda aka bayyana cewa masallaci ne don ya fake saboda yana jin sanyi, wanda dalilin hakan ne ya taka sahun barawon da mutane suka biyo, masallacin da Zakariyya ya shiga shine kuma ainahin gidan da aka nuna a matsayin na yayan Gambo wanda yake can wani garin, ya dace a samar da wani muhallin na daban tunda an nuna ba gari daya bane, domin me kallo zai gane cewar duk muhalli daya ne tunda ba fasalin wajen aka sauya ba.

Karkarewa:

Labarin ya fadakar kuma ya taba zuciya domin an nuna tasirin alkawari da amana, sai dai kuma akwai abubun da ya dace su fi haka inganci, sannan kuma zaren labarin bai dire har karshe ba, don an bar wata sarkakiya wadda ba’a warware ta ba. Wallahu a’alamu!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: