Connect with us

LABARAI

APC Na Gina Wa Kanta Kabari A Jihar Katsina- ‘Ya’yan Jam’iyya

Published

on

Wata kura da ta taso a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina na ci gaba da turnuke siyasar jihar.

Al’amarin dai ya zo ne bayan wasu ‘ya’yan jam’iyar sun yi ikirarin cewa APC na ginawa kanta kabari.

Sun koka kan yadda suka ce jam’iyyar ta yi watsi da ‘ya’yanta da suka yi wahala da ita tare da fifita wasu baki da suka kira su da tsoffin makiyan APC.

Sai dai Uwar jam’iyyar ta musanta haka inda ta ce masu wannan zargi irin mutanen nan ne da gwamnatin jihar ta bai wa mukami amma suka raina, suka tafi Abuja saboda dogon buri. Kamar yadda rahoton Bbc Hausa ya tabbatar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: