Connect with us

LABARAI

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika

Published

on

Shahararen dan kasuwarnan, Aliko Dangote an sake ayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afrika baki daya da zunzurutun kudin da ya kai Dala Biliyan 10.1. Wannan shi ne shekara na tara ke nan a jere.

A rahotan baya-bayan nan da aka saki na da Jaridar Forbes mai lura da sana’o’i, kasuwanci, kimiyyar zamani, da sauran su, cikin rahoton da ta saki na masu kudin duniya, ta bayyana cewa kudin Dangote ya kai Dala Biliyan 10, wanda hakan ke nuna cewa kudinsa ya ragu wanda hakan ya faru sakamakon faduwar darajar kamfanin Simintinsa.

Nahiyar Afrika dai na da kasashe 54, sai dai a cewar Forbes mutum takwas ne kawai za a iya kiran su suna da biliyoyin Daloli, ciki kuwa harda kasashen Afrika ta Kudu da Misra, inda dukkanin mutum 10 na farko da suka fi kowa kudi a Afrika suka fito daga wadannan kasashen da mutum biyar-biyar.

Inda kuma Nijeriya ke da mutum hudu ciki kuwa harda Aliko Dangote wanda aka ayyana a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afrika.

Nassef Sawiris daga Mista shi ne sabon mutumin da ya zama mutum na biyu da ya fi kowa kudi a Afrika da darajar Dala Biliyan 8, wanda kudinsa ya karu daga shekarar da ta gabata daga dala biliyan 6.3 zuwa Dala biliyan 8. Sai kuma dan Nijeriya Mike Adenuga, da dala biliyan $7.7.

Mike Adenuga dai shi ne mamallakin kamfanin waya na GloMobile da kuma kamfanin man fetur na Conoil sannan yana da kadarori a bangarn gidaje.

Kamfaninsa na Glo shi ne kamfanin waya na uku mafi girma a Nijeriya, wanda mutum miliyan 43 ke amfani da layin, yayin da kamfaninsa na Man Fetur ke da rijiyoyi akalla shida a yankin Neja Delta.

Shi ko Dangote, shi ne dan Afrika mafi kudi, wanda shi ke jagorancin kamfanin Dangote Cement. Bayanai sun tabbatar da cewa yana rike da kashi 85 na kamfanin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: