Connect with us

KIWON LAFIYA

Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Wayar Da Kai Kan Cutar Tarin Fuka

Published

on

An bayyana cewar kungiyoyi masu zaman kansu sun hada da Gidauniyar Tonto Dikeh, gidauniyar Godspower Oshodin Global Foundation da Taimako daga Gidauniyar Kudu.

Jakadar kamfanin, Miss Tonto Dikeh, ta bayyana cewar wannan kamfen din an yi shi ne don kaddamar da shirin yaki da Tarin fuka, cutar zazzabin cizon sauro, wacce aka bayyana a matsayin cutar da tafi kamari a duniya.

Dikeh ya bayyana cewar Nijeriya na cikin hadarin kamuwa da cutar, wanda hasashen Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ke jagoranta, saboda haka akwai bukatar fara wani shirin wayar da kai na zamani don kare kai daga yaduwar.

“Cutar tarin fuka tana zama tare da mu a cikin al’ummarmu, dukkanmu muna cikin hatsarin gaske; abin tsoro ne idan muka ji labarin cutar ta kashe yanzu fiye da cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro.

“Kuma, abin bakin ciki shi ne cewa ana iya warkar da shi, kuma mun yaba da abin da gwamnati ke yi, amma, za mu dauki wayar da kan jama’a game da cutar Tarin fuka zuwa matakin na gaba,” in ji ta

Dikeh ta kara da cewar za ta yi amfani da matsayin shahararriyar ta don yin tasiri ga kamfen din bayannan kuma za ta rika sanar da magoya bayanta a ko’ina a kasar da kuma bayan fagen Nijeriya game da hadarin cutar tarin fuka.

Ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi kulawar likita da zarar sun gano alamun cutar.

Mista Seunmanuel Faleye, na Taimako daga Gidauniyar Kudu, ya ce kungiyoyi masu zaman kansu za su zagaya wasu yankuna shida na siyasa da ke Geo-Siyasa don kaddamar da kamfen din cutar tarin fuka, musamman ma yankunan da ke cikin kasar.

A cewar Faleye, cutar guda ce da dole ne dukkan ‘yan Nijeriya su tashi tsaye kafin su kashe kowa.

“Kididdiga ta nuna cewar wanda yake dauke da kwayar cutar  guda daya na iya shafawa ko kuma yasa mutane fiye da 15;  su kamu da cutar, har ila yau kuma  ita wannan cutar wata cuta ce wadda take bukatar dole ne mu tashi  nu canza yadda muke tafiyar da dabi’oin mu, ”kamar dai yadda ya jaddada.

Mista Godspower Oshodin, wanda ya kafa, Godspower Oshodin Global Foundation, ya bayyana cewar an kwashe mutane da yawa daga kasar ta Dubai, sakamakon cutar Tarin fuka yayin da suka gwada ingancin cutar.

Oshodin ya ce, kamfen din shi ne wayar da kan ‘yan Nijeriya game da cutar  bugu da kari kuma  ya ce wani hasashen na WHO ya nuna  cewar za  a samu ‘yan  Nijeriya miliyan hudu da ke dauke da cutar Tarin fuka a shekarar 2020.

“Mu na da kukatar wayar da kan mutane kafin ita cutar ta kasance sanadiyar mutuwar su, WHO ta fada mana cewar muyi yaki  da wannan cutar, za mu zagaya wasu jihohi domin mu bayyana shi wannan labarin,” kamar dai yadda ya furta.

Misis Itoho Uko, mataimakiyar darekta, ta shirin kula da tarin fuka da cutar kuturta, ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya ta ce an gano kashi 24 cikin 100 na masu cutar Tarin fuka a Nijeriya.

“Cutar Tarin fuka wata cuta ce wadda take shafar huhu  da sauri, amma  idan aka gano ta da wuri maganin zai  iya taimakawak wajen magance cutar a farkon wadanda suka kamu da cutar tare da sanya su a magani.

“A na kuma bukatar wayar da kan mutane  dangane da ita cutar yanzu kafin ta dauki rayukan  wasu mutane kamar dai yadda ta bayyana.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: