Connect with us

Uncategorized

Hada Soyayya Da Karatu Na Kawo Matsaloli Ga Dalibai Maza Da Mata – Zainab

Published

on

Galibin al’umma ta san irin yadda daliban sakandare kan varke da soyayya a tsakaninsu yayin da suke zaman makaranta ko kuma gwagwarmayar dalibta. Daya daga cikin abubuwan da ke sabbaba haka shi ne kasancewar daliban a kan gavar rayuwa ta tashen balaga. Shi ya sa ‘yan samari ke kyallara ido a kan ‘yan mata, sannan su kuma ‘yan matan suna so a ce ana son yin soyayya da su domin su kara gaskata abin da yake zuwa a ransu cewa su ma sun cika ‘yan mata. To, da yake an ce da dangari ake cin gari, Shafin Dunyar Makarantu ya tattauna da wata daliba da take kan wannan mataki na sakandare, inda ta zayyana irin matsalolin da daliban da suka tasa soyayya a gaba a sakandare ke fuskanta. Bayan wannan, har ila yau ta yi tsokaci a kan sauran harkoki na rayuwa da karatu duk dai a matakin na sakandare. Mai karatu, a karanta hirar har zuwa karshe domin jin abubuwan da ta kunsa. Mu je zuwa:

 

Da farko, kafin mu fara komai za ki fada wa masu karatu cikakken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi…

Sunana Zainab Shua’ibu amma an fi sanina da Walidation S. Mapi.

 

Ko za ki bawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

Da farko dai ni haifaffiyar garin Biu ne da ke Jihar Borno, an haifeni ne a shekara ta dubu biyu da uku a unguwar Nasarawa, na yi nursery/primary school nawa ne a Godiya private secondary school inda na yi JSS1 da JSS2 a can, sai kuma mahaifina ya canja min makaranta zuwa Progressive private secondary school. To da na je can din na yi JSS3 na a can sai muka lura da cewa can din bai kai wanda na fita daga ciki kokari ba, sai ya kuma maida ni Godiya private school na yi SS1 nawa, yanzu a haka ina SS2.

 

Da kyau, ya za ki bayyanawa masu karatu yadda farkon shigarki makarantar Sakandare ya kasance?

Farkon zuwana ba wata matsala ina zuwa aji na nufa don na san ajinmu tun da dama a can na yi firamare na zauna ne a benci na farko don da na je mu uku ne a cikin ajin kuma mun yi firamaren da su masha Allah ba ni da matsala irin rashin sabo ko wani abin.

Kafin ki kammala Firamare din kina da makarantar da kike da burin shiga cikinta?

A’a kamar yadda nace a baya nursery na acan na yi shi don haka na saba kuma da akayi min maganar canji har kuka nayi don haka banida burin shiga wata makarantar bayan na gama firamare.

 

Da kyau, kasancewar kin shiga makarantar da kika saba da ita, shin ya mu’amularku da sauran dalibai ya kasance, ko kuwa su ma sauran duk tare kuke?

A’a akwai new comers (sabbin zuwa) da yawa kuma gaskiya saida muka saba dasu sosai dan ni din akwai surutu sosai to gaskiya mu’amalata da su me kyau ne.

 

Ya kika ji karatun, kasancewar kun bar firamare kun shiga sakandare?

Eh, gaskiya yanayin karatun ya canja duk da yake canjin ba masu yawa bane amma mun dan sha fama saboda malamin da yake daukarku a firamare ba shi ke daukarku a sakandari ba kuma can din mun saba.

 

Bayan kawayenki da kuka yi firamareda su ko akwai wata kawa da kika ci karo da ita a farkon shigarki makarantar sakandare, shin me ya had’a ku kawance?

Eh, akwai wata kawa da na yi sunanta Fa’iza, dalilin da ya sa muka zama kawaye kuwa shi ne yarinyar kirki ce duk da tana da karancin ilimi amma hankalinta ne yake burgeni.

Ya darasin ranar ya kasance a farkon zuwanku?

Eh, masha Allah ba na mantawa ranar da muka fara zuwa aka fara teaching kuma ranar ne muka karvi bulala daya daya da sunan welcome to jss1 (lale marhabin da shiga aji dayan sakandare).

 

Kamar wacce irin bulala,sabida kasa karatun da kuka yi ko kuma sabida wanne dalili?

Kawai don a yi dariya da kuma sharholiya.

 

Idan na fahimce ki ba wata bulala bace wadda jiki zai ji zafinta kenan?

Kwarai kuwa daya daya ne ma.

 

Wanne darasi aka fara yi muku farkon zuwanki?

English ne darasi na farko da aka fara yi mana.

 

Wanne abu ne ya tava faruwa farkon zuwanki wanda ba za ki iya mantawa da shi ba?

Abin da ya faru farkon zuwana wanda ba zan manta ba shi ne wani malamine ya shigo koyar mana da Hausa, sai yace wa zai iya kawo mana labari? Aiko tsaf na daga hannu na ba da labari tsaf daga farko har karshe nan ya min kyautan naira dubu daya.

Toh ya batun rayuwar cikin makarantar tsakaninku da na saman ku wanda suka fi ku aji, ya abun ya kasance?

Gaskiya ana rayuwar jin dadi tsakanin mu ba mu da wata matsala dasu. Gaskiya basa nuna mana komai na azabtarwa domin malaman mu basa barinsu su yi mana mugunta ko kadan.

 

Duk da cewa a makarantar kika yi firamare dinki da sakandare ya za ki banbantawa masu karatu rayuwar makarantun biyu?

Gaskiya akwai banbanci sosai domin can ana treating (tafiyar da kai) a matsayin yaro while (sannan) a nan kuma ka fara girma.

 

Akan samu marasa tarbiyya a makarantun sakandare shin kuma taku makarantar akwai irinsu?

A’a Gaskiya ba a taruwa a zama duka daya akwaisu kam sai dai ba su da yawa sosai.

 

Ya batun soyayya fa, lokacin da kika je aji hudu ko akwai wanda ya kwanta miki a rai wanda har ta kai kun fara soyayya da shi cikin makarantar?

A’a, gaskiya ni abin da ban sa a raina ba kenan soyayya, bare ma da dan sakandare, a’a gaskiya ban yi ba.

 

Toh ya kike ganin wadanda suke yi, shin hakan ba kya ji yana burgeki?

A’a ko kadan ba ya birgeni hasalima haushinsu nake ji. Domin ina ganinshi a matsayin lalata karatu

Wacce irin shawara za ki bawa masu hada soyayya da karatu musamman na cikin makaranta?

Ina basu shawara da su daina in ma suna yi domin wasu daga cikin samarin ba su kai aure ba amma ‘yan matan sun kai kuma ana son soyayyar da za ta kai mutum har aure kuma wannan soyayya tana kawo matsaloli da yawa ga samarin da kuma ‘yan matan, don haka ina mai basu shawara tun da wuri su tsayar domin samun cikar burinsu.

 

Wanne irin namiji kike da burin aura?

Gaskiya ina son miji nagari me hankali da ladabi da kuma biyayya da son mutane kuma ina son namiji me sa manyan kaya.

 

Allah ya kawo na gari, mu dada komawa baya kadan, a cikin darussan da ake muku wanne darasi ne yafi burgeki Kuma me yasa yake burgeki?

Chemistry ne ya fi burgeni kaf darussan da ake mana, saboda gaskiya ina son in iyata in ga ina ‘deriving formula’ kuma darasin ya yi ne sosai.

 

Wanne darasi ne bakya so cikin darussan Kuma me yasa bakya son sa?

Gaskiya darasin da baya birgeni babu shi, gaskiya duk ina sonsu.

 

A vangaren malamai fa, wanne malami ne yafi burgeki kuma me ya sa?

Malamin da y afi birgeni shi ne Malam Umar Rara, saboda ina gane teaching nashi fiye da kowa.

 

Wanne malami ne a duk lokacin da ya shigo sai gabanki ya fadi sabida rashin son shigowar shi, kuma me ya sa?

Eh, akwai wani ana kiranshi Ambassador, dalili kuwa kullum yana shigowa da bulalarshi.

 

A vangaren dalibai fa, wanne dalibi ne ko daliba ce tafi ko yafi burgeki kuma me yasa ?

Abdul’azeez shi ne dalibin da yake burgeni da kuma Aisha da Hauwa saboda sun san me ya kai su makarantar.

 

Me ya fi burgeki a gaba daya makarantar?

Yadda ake kula da dalibai da yanayin karatunsu.

 

Ya za ki banbanta wa masu karatu banbancin da ke tsakanin macen da ta yi karatu da wadda ba ta yi karatu ba?

Eh, gaskiya akwai bambanci domin duk wacce ta tava zama a aji da ka ganta za ka gane daga yanayin wayewarta da kuma mu’amala da mutane tabbas akwai banbanci ko a yanayin zamantakewar aure, mace me ilimi ko Arabic ne ko boko ta fi iya zaman aure.

 

Menene burinki na gaba game da karatunki?

Ina son in kai kololuwa a karatu domin ina da burin zama cikakkiyar Likita.

 

Idan kika yi aure kika haifi ‘ya ta kammala karatun sakandarey shin za ki bar ta ta ci gaba da makarantar gaba?

Gaskiya zan barta in dai ta nuna tana so.

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga makarantun sakandare har ma da masu kokarin shiga makarantar gaba da sakandare?

Shi ne su sa hankali ga karatunsu ban da bin kawayen banza domin yanzu yawancin abin da ke faruwa kawaye ne sila.

 

Me za ki ce ga makaranta wannan shafi na Duniyar Makarantu?

Ina yi musu fatan alkhairi su ci gaba da bibiyar wannan shafi mai albarka dan karuwar abin da ba su sani ba da wanda yake na gyara su gyara.

 

Me za ki ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a?

Su ci gaba da karanta wannan jarida domin yana fadakarwa ilimantarwa gami da nishadantarwa, Allah ya daukaka ma’aikatanta amin.

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Gaisuwa gareki uwata Ladingo ‘yar mutan Nijer ina ji da ke, Hassan Etike da Dan’uwana Hussain etike, Abubakar Kuraymie, my Fatima sardauna keta dabance, my Khulsum ba zan tava matawa da ke ba, Aunty Hassana dan larabawa, my Sadeeya sanaz, my ‘YAR JARIDA (BIG GURL) Hafsat Amjad my Eyman our King, sai kuma ‘yan kungiyar mu wato Zamani Writers Association ina mika sakon gaisuwata ga kowane marubuci.

Muna godiya da ba mu lokacinki da kika yi.

Ni ma nagode.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: