Connect with us

LABARAI

Kano Ba Ta Bukatar Jami’an Tsaro Na Daban – Ganduje

Published

on

Sakamakon gamsuwa da kyawawan tsare-tsare tare da fahimtar juna da ke tsakanin Hukumomin tsaro da kuma Gwamnatin Jihar Kano, Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, Jihar Kano ba ta bukatar wasu jami’an tsaro na daban, ba ya ga cikakkun jami’an tsaron da doka ta amince da su, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Juma’a. Gwamnan na yin wannan jawabi ne, lokacin da sabon Mataimakin Sufetan ‘Yan Sanda, mai kula da shiyya ta daya AIG Sadik Abubakar Bello, ya ziyarci Gwamnan a Fadar Gwamnatin Kano, domin gabatar da kansa ga Gwamna Ganduje tare da sauran manyan Jami’an Rundunar ta ‘Yan Sanda, ciki har da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Habu Sani a ranar Larabar da ta gabata. “Ba mu da niyyar amincewa da wasu jami’an tsaro na daban, wadanda ba su da wani horo, wanda ma ba su fahimci aikin harkokin tsaro ba. Ba zai yiwu a ce ka kawo wa jama’a abinda ba shi suke bukata da sunan tsaro ba haka kawai.” Mun gamsu kwarai da yadda Hukumomin tsaro ke gudanar da ayyukansu ta fuskar tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar Kano, hakan ne ma ya kara mana karfin guiwar fahimtar haka, musamman kyakkyawar fahimtar da ke tsakanin  Hukumomin tsaro, wanda al’umma ke samun ingantaccen tsaro ta bangaren ayyukansu. Ya kara da cewa, babu wani sabani tsakanin Jami’an tsaro a Jihar Kano, “dukkansu na yin aiki tare domin cimma bukatun al’umma. Dukkaninsu kuma na hada kai da juna wajen gudanar da harkokin tsaron Jihar Kano. Sannan, a koda-yaushe muna yin amfani da dukkanin damar da muke da ita, wajen farautar masu aikata laifuka”, in ji Ganduje.

Wasu daga ciki a cewar tasa, sun hada da samar da hanyar bincike ta hanyar bin kwakkwafin ababan hawa tare da samar da na’urorin daukar hoto ta (CCTV), a muhimman wurare a Jihar Kano. “Don haka, ta yaya daga baya za ka sake shigo da wasu jami’an tsaron rana tsaka? wanda hakan ka iya zama wata barazana ga harkokin tsaron al’umma. Saboda haka, ba ma bukatar abinda zai mayar da hannun agogo baya, wanda ka iya zama kalubale ga harkokin tsaro”, a cewar tasa. “Muna da Hukumar Hisba, wadda ke aiki tare da hadin guiwar Rundunar ‘Yan Sanda. Sannan suna samun kyakkyawar kulawar wadannan ‘Yan Sanda da sauran Hukomin tsaro kamar yadda al’amarin yake, ba ma kallon su wasu daban a cikin jami’an tawagar jami’an tsaro (Hukuma Hisba), kamar kowa suke suna taimakawa Hukumomin tsaro tare da yin aiki tukuru”. Gwamna Ganduje ya kara da cewa, “bisa kyakkyawar fahimta da yin aiki tare  tsakanin dukkanin bangrorin tsaro, da kuma taimakon Allah da sanya albarkarsa, Jihar Kano a halin yanzu na ta fi dukkanin sauran jihohin kasar nan zaman lafiya. Kazalika, zuwanka wurinmu ne ke sake bayar da tabbacin cewa ka zo yin aiki a wurin da aka turo ka, wanda ya kunshi Jihar Kano, Katsina da kuma Jigawa.” Saboda haka, sai ya kara tabbatar da cewa, dukkanin jihohin da ke wannan shiyya za su cigaba da yin aiki tare, domin tabbatar da cikakken zaman lafiya da tsaron jihohi da ma kasa baki-daya. Da yake kara yin tsokaci kan wasu dabarun tsaro a Jihar Kano, Gwmna Ganduje ya bayyana cewa, “mun bujiro da wani tsari a cikin harkokin tsaronmu, wanda zai tafi tare da yin aiki irin yadda duniya ta runguma ta kuma cigaba.” “Ya zama wajibi a fahimci cewa, a koda-yaushe muna bukatar samun bayanai a tsakanin al’umma. “Za mu tabbatar da samar da tsarin samar da bayanai na boye a dukkanin kasuwanni da sauran wuraren zaman al’umma”, kamar yadda ya bayyana.

Har ila yau, da yake yin tsokaci akan Cibiyar nan ta lura da harkokin tsaro da Gwamnatin Jihar Kano ta samar a Shelkwatar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano da ke Bompai, ya bayyana cewa Kano na yin amfani da dukkanin damammaki ta hanyar amfani da sabon tsarin harkokin ‘Yan Sanda. Ciki kuwa, har da fadadawa tare da shigar da Masarautu daga guda daya da ake da ita zuwa biyar, wanda suna cikin dalilanmu na samar da ingantaccen tsaro, tare da kara fadada shirin Jami’an ‘Yan Sandan da ke cikin al’umma, ta yadda Sarakunanmu za su kara samun damar bayar da gudunmawarsu tare da hada hannu da Gwamnati, domin samar da ingantaccen tsaro a Jihar Kano”, in ji Gwamnan. Haka zalika, shi ma da yake gabatar da nasa jawabin, AIG Sadik Abubakar Bello, jinjinawa Gwamna Ganduje ya yi,  bisa samar da kyakkyawan yanayin aiki ga jami’an tsaro, domin yin ingantacce aiki a Jihar Kano. Ya ce “a shirye nake domin yin aiki tare da hada karfi da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano. Samar da wannan Cibiyar Lura da Harkokin Tsaron, ko shakka babu wata alama ce da ke nuna cewa, mai girma Gwamna na yin abubuwan da suka dace, domin cigaban al’ummar Jihar Kano.” Saboda haka, sai ya yi alkawarin cewa za su cigaba da yin duk abinda ya kamata wajen inganta harkokin tsaro a Jihar ta Kano da sauran jihohin da ke karkashin ikonsa. Haka zalika, ya bukaci dukkanin al’umma su cigaba da bayar da goyon baya ga jami’an tsaro, domin samun cigaban da ake bukata a wannan jiha da ma kasa baki-daya. “Har wa yau, wannan kokari na Gwamna ta fuskar sake fasalin masu taimakawa ‘Yan Sanda, wani al’amari ne a bayyane da zai kara inganta tsarin na ‘Yan Sanda a cikin al’umma, wanda a fili yake kowa ya fahimci yadda Gwamnan ke yin iyakar bakin kokarinsa akan hakan” a cewar ta AIG.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: