Connect with us

MANYAN LABARAI

Batun Sauke Shugabannin Tsaro… Ina Ganin Abinda Ba Ku Gani – Buhari

Published

on

Masu dakon jiran Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami shugabannin hukumomin tsaro na Nijeriya, sai dai su cigaba da tsumayi har zuwa wani lokacin da ba a sani ba, domin kuwa ko da wasa Shugaban Kasar bai shirya raba gari da shugabannin hukumomin tsaron ba a daidai wannan lokacin, kamar yadda fadar Shugaban Kasar ta tabbatar a daren ranar Lahadin da ta ba gabata, 16 ga Fabrairu, 2020 cikin wata sanarwa.

Akwai dai masu kiraye-kirayen da sai lallai Shugaban Kasar ya sallami shugabannin hukumomin tsaron domin ya maye gurbinsu da wasunsu, saboda kara wa yakin da a ke yi da masu tayar da kayar baya kaimi.

Sake bullar kashe-kashen da masu tayar da kayar bayan su ka yi ta yi a shiyyar ta Arewa maso Gabas da ma wasu sassan kasar, kamar jihohin Neja, Katsina, Kogi da Zamfara, a kwanan nan ya kara balbala wutar masu matsin lambar sai lallai Shugaban kasar ya sallami shugabannin hukumomin tsaron kasar.

Akwai ma wani yunkuri da wasu su ke yi na gudanar da zanga-zanga, domin ganin lallai an tilasat shugaban ya sallami shugabannin hukumomin tsaron; zanga-zangar da gwamnati ta ce wasu ne su ka dauki nauyin gudanar da ita, musamman ma ’yan adawarta.

Fadar Shugaban Kasar a ranar ta Lahadi da dare ta fitar da wata sanarwa ta bakin Kakakin Fadar, Malam Garba Shehu, inda ta ke cewa, “sallamar shugabannin hukumomin tsaron ba zai hana faruwar abubuwan da su ke faruwa ba. Ko mu yarda ko kada mu yarda, tabbas mu na cikin yanayi ne na yaki. Shugaban kasa kuma babban Kwamandan Askarawan Nijeriya ya na ganin abinda wasu ba sa gani. Hakan ne kuma ya sanya tilas a sarara ma sa ya yi abin da ya ke ganin shi ne ya dace.

“Mutanen da ba su san abinda gwamnati ke yi ne ba su ke cewa Shugaban Kasa bai damu da yanayin da a ke ciki ba. A zatonsu, lamarin tsaro tamkar kasuwa ce, inda kowa ma masani ne. Shugaban kasa soja ne, ya na kuma yin aiki tukuru ta hanyar gabatar da hanyoyi daban-daban, domin ganin an warware wannan matsalar.”

Fadar shugaban kasar ta bayar da tabbacin za a kara aikewa da dakaru tare da manyan kayan aikinsu a can bakin dagar.

Haka nan, kimanin sojoji 3,000 ne za a yaye a watan Maris ko na Afrilu, domin su fafata da ’yan ta’adda masu tayar da kayar baya a fadin kasar. Rundunar Sojin sama ma ta yaye sama da dakaru 2000, in ji sanarwar.

Haka nan, Gwamnatin Tarayya ta na sa ran karbar karin wasu jiragen yaki guda 12 samfurin A-29 Super Tucano fighter jets daga kasar Amurka.

Shehu ya bayyana cewa, matsalolin tsaron da su ke addabar kasar ba wai Nijeriya ce kadai ta ke fama da su ba; akwai kasashen Afrika masu yawa, wadanda duk su na fama da irin wadannan matsalolin na tsaro.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: