Connect with us

LABARAI

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Lissafo Sharuddan Bude Iyakokin Nijeriya

Published

on

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada sharadin bude iyakokin kasar nan don barin kaya su shigo daga kasashe masu makwabtaka. Ya bayyana cewa bude iyakokin kasar nan ya dogara ne a kan rahoton kwamitin bangare uku da ya hada da gwamnatocin Nijeriya, jamhuriyar Benin da jamhuriyar Nijar. Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a lokacin da ya hadu da Shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore na kasar Burkina Faso, wanda ya kai masa ziyara a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Abuja, kamar yadda Channels Tb suka ruwaito. “Babbar matsalarmu shine tsaro, shigo da makamai, harsasai da kuma kwayoyi,” ya ce kamar yadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya sanar. Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara da cewa, “mun fahimci raguwa a ta’addanci tun bayan da muka rufe iyakokin kasarmu. Hakazalika, manonanmu yanzu na iya siyar da shinkafar gida tunda mun dena shigo da ta Turai wacce ke cika kasar nan.
“Zan yi aiki da gaggawa matukar na samu rahoto,” Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tabbatar wa da Kabore. Shugaban Burkina Faso din shine shugaban kwamitin ECOWAS wanda hakkin shawo kan matsalar rufe iyakoki ya rataya wuyansu. Ya sanar da shugaban kasar Nijeriya din cewa ya zo ziyarar ne don sauke hakkin ECOWAS da ke kansa. Shugaban kasa Kabore ya ce, akwai kalubale da yawa wadanda suka sa Nijeriya ta garkame iyakokinta wadanda shugaban Nijeriya ya sanar masa. Yayi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da ya kara duba matsayarsa. Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya halarci taron, ya bayyanawa manema labaran gidan gwannati abinda aka tattauna. Ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya damu da damuwar kasashen da ke da makwabtaka da Nijeriya ballantana idan ya duba yarjejeniyar sahale kai kawo tsakanin kasashen ECOWAS din. Onyeama yayi bayanin cewa an rufe iyakokin kasar nan ne saboda dalilan tsaro, duk da ya ce akwai fatan budesu nan ba da dadewa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: