Connect with us

RA'AYINMU

CBN Za Ta Farfado Da Noman Auduga

Published

on

Mafi yawancin tallalin arzikin kasashen Asiya ya tallaka ne ta hanyar sarrafa amfanin gona, musamman ma noman auduga. Kasashen irin su China da Indiya da Bangladesh suna sarrafa auduga zuwa wadanda kayayyaki domin su sayar da su a kasuwannin duniya.

Kasar Indiya ta bunkasa tallalin arzikinta ne ta hanyar sarrafa auduga wanda ita ce ta biyu wajen hayar ma’aikata a duniya, inda a yanzu gwamnatin tarayyar Nijeriya take kokarin bunkasa kamfanonin yadi. Abu daya da kasar Indiya ta kware dai shi ne, tana sarrafa auduga zuwa yin wasu kayayyaki ne a cikin gida domin bunkasa tattalin arzikinta. Idan muka duba a yanzu za mu ga cewa, tattalin arzikin duniya ya samu matsala sakamakon manufofin daban-daban na gwamnatoti wanda ya raunata kasuwancin fita da kayayyaki a kasuwan duniya. Kamfanonin Nijeriya da ke kokari a bangarori daban-daban sun dukushi sakamakon dogaro da kayayyakin kasashen waje.
Sun kara dukushewa ne tun lokacin da kasar Amurka ta nuna ra’ayinta a kan dokar na bunkasa tattalin arzicikin kasashen Afirka, wanda yake cewa, bangaren majalisa ita za ta amince da majalisun kasa, dokar wanda aka kafa a wajen wani taron da ya gabata a watan Mayun shekara 2000. Nijeriya ba za ta amfana da wannan doka ba, domin dokar zai bunkasa tattalin arzikin wani bangaren yankin kasashen Afirka da ke yankin Sahara da kuma kasar Amurka. Babban makasudin wannan doka shi ne, domin kasar Amurka ta samu damar yin kasuwancin yadi da wasu kayayyaki.
Ra’ayin wannan jaridar dai shi ne, wannan manufar zai harfar da matsala wanda a dai-dai lokacin da Nijeriya take yunkurin sake farfado da noman auduga, domin ya kasance ya zama hanyar da Nijeriya za ta dunga samun kudaden shiga. Kamfanonin da ke sarrafa auduga sun dakushe sakamakon an fi amfani da kayayyakin da ake shigawa da su daga waje. Haka kuma, manoma sun samu koma baya ne sakamakon rashin ishasshen kudaden gudanar da ayyukansu. Lamarin ya yi kamari ne sakamakon sashin samaun yabanya da kuma inganta iri, wannan shi ya kasha musu kwarin giwa wajen bunkasa ayyukansu a wannan bangare. A gaskiyar Magana ita ce, tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa idan har babban bankin Nijeriya (CBN) a karkashin jagorancin Mista Emefiele zai aiwatar da wannan lamarri, da irin wannan lamari ne za a samin damar kara samar da kayayyaki da dama a cikin kasar nan musammam ma a bangaran fannin noma. Domin kara farfado da noman auduga da bangaran yadi, babban bankin Nijeriya (CBN) ya amince da bai wa kamfanonin sarrafa auduga guda tara bashin kudi har na naira biliyan 19.18 mai kudin ruwa kalilan. Ba zato ba tsammani, sai kungiyar manoman auduga ta kasa tare da hadin gwiwar kamfanin Ginning Companies sun dauki alkawarin samar da iri wanda zai bayar da damar samar da iri mai kyau a cikin kasar nan.
Tsarin yana daya daga cikin hanyoyin da ake kokarin bi wajen ganin kamfanonin su ci gaba da bunkasa tare da samun yabanya mai kyau. Babban dabarar dai shi ne, a samu inganta alaka a tsakanin manoman auduga daga kuma kamfanoni masu sarrafa audugan, domin a tabbatar da cewa, kamnanonin masu sarrafa auduga za su iya sarrafa audugan da manoman suke noma cikin inganci. Haka suma kamfanoni masu yin atamfa da yadudduka suna cikin wannan tsari ba a bar su a baya ba. Wannan lamari yana daya daga cikin hana shikowa da kayayyaki daga kasashen ketare. Koda yake gwamnatin tarayya ba ta samun gwarin kwiwa a kan hakan. An bai wa kowani ma’aikatu da bangarorin gwamnati da su karfafa gwarin giwa wajen tallata kayayyakin cikin gida.
An dai bayyana cewa, bangaran noman auduga a baya yana samar da kudi wanda ya kai na naira biliyon 50, inda a yanzu ake sa rai zai samar da kudi wanda ya kai na naira biliyan 100. An dai kafa kwamitin farfado da kamfanonin sarrafa auduga domin ta tabbatar da cewa bangaran ya ci gaba da aiki yadda ya kamata.
Lallai wannan mataki na babban bankin Nijeriya yana bukatar a aiwatar da shi cikin gaggawa. Haka kuma yana bukatar wasu hanyoyi wajen gudanar da shi domin zai taimaka wajen bunkata tattalin arziki. Irin wannan lamari na bukatar bin wasu ayyuka kafin a yi gudanar da shi, duk da dai hanyoyin ci ke suka da matsaloli masu yawa, amma dai idan aka samu aiwatar da shi, to zai bunkata tattalin arzikin kasar nan ta hanyar amfani da harkokin noma.
Muna kira ga Emefiele ya yi kokarin wajen aiwatar da wannan tsarin cikin gaggawa kafin ya kawo karshen shugabancinsa tare da batan wanda zai gaje shi ya ci gaba da wannan yunkuri, domin tabbatar da ci gaban wannan tsari.


 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: