Tsohon gwamnan Jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar PDP, Ayodele Fayose, ya ce bayan shafe shekaru takwas na shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, dole ne shugaban kasa ya fito daga yankin Kudu.
Ya ce dole ne shugaban kasa ya fito daga Kudu a 2023.
- An Gurfanar Da Masu Gadi Kan Zargin Satar ‘Cornflakes’ Din Miliyan 2.1
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 3 Da Kwato Makamai A Wani Farmaki Da Suka Kai Musu
Fayose ya tsaya takara kuma ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a watan Mayu.
LEADERSHIP ta tattaro cewa tsohon gwamnan alakarsa ta yi tsami da shugabancin jam’iyyar PDP da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, a kan zaben gwamnan jihar Ekiti da aka kammala, wanda dan takararsa Bisi Kolawole ya sha kaye.
Haka kuma, mai yiwuwa dan takarar Fayose ba zai rasa nasaba da zabin gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takarar Atiku a zaben 2023 ba, inda ya marawa abokinsa baya, gwamna Nyesom Wike, na jihar Ribas.
Fayose, ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba da yamma, ya ce nemawa Kudu shugabancin kasar yana samun goyon bayan sassa daban-daban da kuma masu ruwa da tsaki da abin ya shafa na kundin tsarin mulkin PDP.
Ya kara da cewa ‘yan Nijeriya su jira cikakken bayanin matakin da zai dauka nan ba da dadewa ba.
Ya rubuta cewa: “Shugaban Nijeriya na yanzu dan Arewa ne kuma ya shafe wa’adi biyu, don haka yana nuna cewa dole ne shugaban kasa ya fito daga Kudu a 2023.
“’Yan Nijeriya su jira cikakken bayani nan ba da jimawa ba.
“Tsarin mulkin PDP ya tanadi shugabancin karba-karba. Sashi na 3 (c) ya tanadi cewa jam’iyya za ta ci gaba da yada manufofinta ta hanyar karba-karba da na ma’aikatun zabukan jama’a domin tabbatar da daidaito, adalci da gaskiya.