• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Ko Takarar Gwamnan Kano Ta Yi Wa Sadiq Aminu Wali Girma?

by Buhari Abba Rano
3 years ago
in Rahotonni
0
2023: Ko Takarar Gwamnan Kano Ta Yi Wa Sadiq Aminu Wali Girma?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da ake kara kusantar zabe a Nijeriya, jam’iyyun siyasa da wadanda su ka fito takara a mukamai na ci gaba da yada manufa tare da bayyana irin kyawawan manufofin da suke burin aiwatarwa, idan sun kai ga nasara a zaben shekarar 2023 da ke tafe.

A Jihar Kano, da ta zama cibiyar siyasar Nijeriya, akwai masu neman kujerar gwamna a jam’iyyu daban-daban kuma ake jin duriyarsu da kuma bayyana wa Kanawan irin tanadin da suka yi musu idan su ka kai ga nasara.

  • Gobara Ta Kone Shaguna 15 Da Lalata Kaya Na Miliyan 19 A Jihar Kwara
  • Gobara Ta Yi Barna A Kasuwar Sayar Da Kayan Masarufi Ta Singa Da Ke Kano.

Jami’yyar APC ce ke mulkin Jihar Kano, inda suke da Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin dan takara, sai kuma jami’yyar NNPP ta tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso da suke da Abba Kabiru Yusuf da kuma jami’yyar PDP da suke da Sadiq Aminu Bashir Wali a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar takara a 2023.

Wali, wanda tsohon Kwamishinan albarkatun ruwa ne a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ya zama dan takarar gwamnan ne a jam’iyyar PDP bayan da ya yi nasara a zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.

Tun da farko jam’iyyar PDP a Kano ta fuskantar rikici a kan wane ne halastaccen dan takarar gwamnan a jami’yyar.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

Abin Fargaba Ne Yadda Bashin Nijeriya Ya Haura Tiriliyan 149 – Shugaban Majalisar Wakilai 

Muhammad Abacha da Sadiq Aminu Wali kowane a cikinsu na jin shi ne halastaccen dan takarar jam’iyyar, biyo bayan rikicin zaben fidda gwani da kowanne bangare ya gudanar karkashin sa idon hukumar zabe ta kasa INEC.

Shugabancin jam’iyya bangaren Shehu Wada Sagagi, ya gabatar da zaben fidda gwani na jam’iyyar kuma a matsayarsa, Muhammed Abacha ne ya samu nasara.

Bayan zuwa kotu da aka yi, kotu ta sake ayyana Sadiq Wali a matsayin halastaccen dan takarar da zai yi wa PDP takarar gwamna a Kano.

Sai dai duk da wannan damar da Wali din ya samu amma har yanzu ya gaza fitowa fili ya bayyana wa Kanawa manufofinsa da kuma irin tanadin da gwamnatinsu ta yi musu idan ya kai ga nasara.

Haka kuma wani abin mamaki ga lamarin Sadiq Aminu Wali, shi ne yadda ya ke biris da gayyatar da manyan kungiyoyi ke shirya wa ‘yan takarar gwamna a Kano, inda al’umma suke kallon ko bai shiryawa takarar ba.

Haka zalika, ko a lokacin da Sadiq Wali din ya ke Kwamishinan ruwa na Kano, babu wani abin a zo a gani da ya tabuka domin sai da ta kai ga yara ‘yan makaranta ba sa samun zuwa makaranta ko kuma ba sa zuwa da wuri sakamakon fadi-tashin neman ruwa.

Masu sharhi a kan al’amuran siyasar Kano da sauran ‘yan siyasar jihar, sun dade da bayyana Sadiq Aminu Wali, a matsayin dan gatan da bai san wanne hali talaka a Jihar Kano ke ciki ba, kuma ba shi da wani kuduri ko manufa da zai ciyar da Kano gaba idan ya zama gwamna a 2023.

Mafi yawan al’ummar Jihar Kano na kallon Sadiq Aminu Wali a matsayin “Sabon Yankan Rake” a siyasa domin ba shi da wata kwarewa ko gogewar da zai ja ragamar shugabancin Jihar Kano da ke da sama da mutum miliyan tara.

Kuma shi ma ya tabbatar wa da duniya hakan la’akari da yadda ya gaza fitowa fili ya tallata takararsa da manufofinsa ga Kanawa.

Babu shakka ya zama wajibi ga al’ummar Jihar Kano da su zabi jajirtaccen mutumin da ya ke da ilimin addinin Islama da kuma na zamani tare da gogewar aiki da kuma manufa wanda ya ke da sanayya tsakanin manyan ‘yan kasuwa da ‘yan boko da ma’aikatan gwamnati da kuma goyon bayan kungiyoyin fararen hula, ba wai su bi rububi wajen zabar “Yankan Rake” ko dan gatan da bai san daga ina zai fara magance matsalolin da su ka yi wa jihar katutu ba.

Buhari Abba dan jarida ne ya rubuto daga Kano, Najeriya

[email protected]


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCkanoNNPPPDPSadiq Aminu WaliTarakarar GwamnaZabe
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gobara Ta Kone Shaguna 15 Da Lalata Kaya Na Miliyan 19 A Jihar Kwara

Next Post

Yawan Adadin Mutane A Fadin Duniya Ya Doshi Mutum Biliyan 8 — MDD

Related

Ahlul Faidhati Mai Diwani Group
Rahotonni

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

2 days ago
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Rahotonni

Abin Fargaba Ne Yadda Bashin Nijeriya Ya Haura Tiriliyan 149 – Shugaban Majalisar Wakilai 

6 days ago
Arewa
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Bullo Da Sabbin Matakan Yaki Da Ta’addanci

7 days ago
'Yan Bindiga
Rahotonni

Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina

1 week ago
Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
Rahotonni

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

2 weeks ago
Sin Ta Fara Amfani Da Tauraron Dan Adam Wajen Duba Manyan Hanyoyin Wutar Lantarki A Karo Na Farko
Rahotonni

Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago

2 weeks ago
Next Post
Ambaliyar Ruwa A Jihar Bayelsa Kalubale Ne Mai Girman Gaske – Majalisar Dinkin Duniya

Yawan Adadin Mutane A Fadin Duniya Ya Doshi Mutum Biliyan 8 — MDD

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta

September 14, 2025
Likitoci

NARD Ta Janye Yajin Aikin Gargaɗi Da Ta Fara

September 14, 2025
APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC

APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC

September 14, 2025
An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Rushewar Masa’antu Ya Jefa Al’umma Da Dama Cikin Ƙangin Talauci A Arewacin Nijeriya

September 14, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

September 13, 2025
Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

September 13, 2025
Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

September 13, 2025
An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

September 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.