Shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Kano sun bayyana cewa a kasar da babu manufa ce kadai, jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai iya zama shugaban kasa. Sun kara da cewa NNPP za ta sha wahala wajen sake neman a zabenta a Jihar Kano a 2027 ba kamar yadda suke ikirarin cewa, Shugaban kasa Bola Tinubu ne zai wahala ba.
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa a yanzu haka jam’iyyarsu ta kara samun hadin kai tare da dinke barakar da suka samu a zaben da ya gabata kuma sun shirya tsaf wajen kayar da NNPP a Jihar Kano.
- Jagororin Siyasar Arewa Raunana Ne Kuma A Rarrabe Suke – Salihu Lukman
- Cika Shekara 100 A Duniya: Tarihin Shaikh Dahiru Bauchi Daga Bakinsa
Jigon APC ya ce sabanin rahoton da kafafen yada labarai suka bayar ga shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashimu Dungurawa, jam’iyyar da ke mulkin jihar da jagoranta na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ne za su fuskanci mummunar matsala kan rikicin masarautar Jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano ya ce rikicin sarautar Jihar Kano na iya yin illa ga burin Shugaba Bola Tinubu wajen ci gba da mulki a karo na biyu a 2027.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano ya ce ikirarin da shugaban jam’iyyar NNPP, Dungurawa ya yi alama ce da ke nuna gazawar jam’iyyar a jihar da kuma kasa baki daya.
Abbas ya kara da cewa abun kunya ne ya bayyana haka ganin irin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP da kuma jagoranta, Kwankwaso, abin kunya ne ya yi ikirarin sake lashe zabe a 2027.
“An ce Kwankwaso ya samu kuri’u 1,454,649 a zaben 2023, wanda ke wakiltar kashi 6.23 ne kawai, kuma yawancinsu daga Kano ne ya samu kuri’un. Amma binciken da kafafen yada labarai suka yi bayan zaben ya nuna cewa Kwankwaso bai samu kuri’u 100,000 a wata jiha ban da Kano.”
Abbas ya yi nuni da cewa Kwankwaso ya samu kuri’u miliyan 1.2 ko kashi 19 cikin 100 na kuri’un da aka kada a yankin arewa maso yamma a yankinsa, kuma kusan bai samu komai ba a sauran yankunan kasar nan.
“Ta yaya za a yi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi daga kudu maso gabas ya yi wa Kwankwaso fintinkau a jihohi 13 na arewa kamar Kaduna, Taraba, Borno, Gombe, Kebbi, Kogi, Kwara, Neja, Sakkwato, Nasarawa, Filato, Adamawa da kuma Benuwai,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar APC ya ce al’ummar Kano da masu tunani a arewacin Nijeriya sun fahimci cewa, abin da gwamnatin tarayya ke bukata a rikicin masarautar Kano shi ne, ta tabbatar da doka da oda domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma jihar.
A cewarsa, a zaben 2027, al’ummar Jihar Kano wadanda aka rusa gidajensu ba za su manta ba, al’ummar Jihar Kano wadanda aka lalata musu hanyoyin samun tattalin arziki da kasuwanci ba za su sake zaben NNPP ba. Mutanen da dama gwamnatin Jihar Kano ta daidaita.
Shugaban APC na Jihar Kano ya bayyana cewa batun zaben shugaban kasa a 2027 da shugaban jam’iyyar NNPP na Kano ya yi barazanar za su kayar da su a Kano manuniya ce ga gazawar gwamnatinsu, sannan kuma za su yi amfani da dukiyar al’ummar Jihar Kano wajen tallata Kwankwaso wanda ba zai iya zama shugaban kasa ba.