Akwai alamun da ke nuna cewa tattaunawar maja a tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi, da kuma Rabiu Kwankwaso ta cika da shakku game da yiwuwarta.
Shakkun dai ya dabaibaye majan ne tun lokacin daKwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya bayyana cewa shi ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2027.
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
- Dakta Gadan-ƙaya Ya Bada Haƙuri Kan Zargin Auren Jinsi Da Ya Yi A Bauchi
Rahotanni sun nuna cewa jagorar jam’iyyar NNPP ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya kaddamar da sakatariyar jam’iyyar a Jihar Katsina kwanan nan.
Tsohon gwamnan Jihar Kano, wanda Atiku da Obi suka yi zawarcinsa, ya ci gaba da cewa jam’iyyarsa ta NNPP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasa, jihohi da sauran mukamai a fadin Nijeriya a zaben 2027.
Baya ga sanarwar tasa, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, kuma ta fita daga kan layi.
“Ina so in tunatar da ku cewa jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, saboda da muna cikin jam’iyyar, tun da suka fita daga kan layi, muka yanke shawarar barin jam’iyyar,” in ji shi.
Kafin kalamun na Kwankwaso, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa manyan jiga-jigan ‘yan adawa na neman hadaka domin kalubalantar APC a zab0en 2027.
Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na asa, Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa a gidan talabijin na Channels.
Abdullahi ya tabbatar da cewa Atiku, Obi, da Kwankwaso suna tattaunawa kan yiwuwar yin kawance.
Ya koka da yadda jam’iyyar ta yi asarar kuri’u sama da miliyan daya, inda ya kara da cewa da Kwankwaso ko Obi sun ci gaba da zama a jam’iyyar, “da mun rufe gibi da kuma kauce wa matsalolin siyasa da tattalin arziki da ake ciki a yanzu.
“Tabbas. Ana ci gaba da tattaunawa. Kun ga Peter Obi yana tattaunawa da Atiku. Kun ga Peter Obi yana ganawa da el-Rufai,” inji Abdullahi, inda ya kara da cewa jam’iyyarsu na kokarin ganin Obi, Kwankwaso, da sauran shugabannin da suka bar PDP sun jam’iyyar kafin zaben 2027.
“Daya daga cikinsu zai yarda da sauran, sannan za mu sami alkibla. Damuwarmu a matsayin jam’iyya da kuma wadannan mutanen da na ambata shi ne za su ceto ‘yan Nijeriya daga irin wannan kunci da yunwa da fatara da rashin tsaro da ke damun kasar nan,” ya kara shaidawa.
Idan za a iya tuna kafin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku, a wata hira da BBC, ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar kawance da Obi da Kwankwaso, amma hakan bai faruwa ba.
Bugu da kari, an kuma samu rashin nasara a tattaunawar da aka yi kan kawance tsakanin Peter Obi na jam’iyyar LP da Rabiu Kwankwaso na NNPP, a daya bangaren.
Da yake magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na News Central, Obi ya ce ba ya neman shugabancin Nijeriya ta kowacce hanya.
Ya ce zai amince a yi aiki tare da wasu ne kawai idan ya ga mutanen da za su iya yin aikin da kyau.
A cewarsa, ba zai hada kai da kowa ba don manufar kama jihar ko kuma ya ci zabe.
Masana harkokin siyasa na nuna shakku kan kawancin Atiku da Kwankwaso da kuma Obi wajen kawar da jam’iyyar APC daga kan karagar mulkin Nijeriya. Wanda suke ganin kamar an samu matsala duba da irin kalamun da Kwankwaso ya furta da kuma irin martanin da PDP ta mayar masa.