Jam’iyyar hadaka ta ADC ta bayyana cewa sauyin sheka na gwamnonin da sauran ‘yan siyasar da aka zaba zuwa jam’iyyar APC ba zai iya tabbatar da tazarcen Shugaban kasa Bola Tinubu zuwa Aso Rock a zaben 2027 ba.
A yayin da yake yin hira ta musamman ga manema labarai a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyya a ranar Asabar a Yola, shugaban jam’iyyar ADC reshen Jihar Adamawa, Shehu Yohanna, ya ce ‘yan siyasa da ke komawa jam’iyyar APC mai mulki suna shiga cikin bautar siyasa.
Ya ce jam’iyyar ta riga ta yanke shawarar bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, sannan Peter Obi a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
“APC na jan ‘yan siyasa masu matukar bukata da marasa muhimmanci cikin jam’iyyarsu, suna neman jama’a marasa amfani da marasa muhimmanci wadanda ba su da amfani a lokacin zaben 2027.
“Gwamnonin da ke barin jam’iyyarsu zuwa APC su ne wadanda suka gaza matuka kuma suna kokarin dawowa don samun wa’adinsu na biyu.
“Sauran gwamnonin da suka sauya sheka da mambobin majalisar dokokin kasa sune wadanda ke kokarin tsere wa hukuncin hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Ka tuna lokacin da tsohon shugaban jam’iyyar APC, Sanata Adams Oshiomhole, ya ce, ‘an yi maku gafara idan kuka shiga APC.
“Wannan na nufin sun rasa tasirin siyasa a cikin jam’iyyunsu da jihohinsu. Kuri’u ba sa tare gwamnonin, amma suna tare da talakawa,” in ji Yohanna.
Dangane da zaben cike gurbi na majalisar karamar hukumar Ganye, ya ce, “Zaben cike gurbin majalisar na karamar hukumar Ganye na nuni ga Shugaba Tinubu cewa ya tara mutane marasa amfani a APC. An tura jami’an tsaro sama da 6,000 zuwa Ganye tare da ministoci daga jihohi daban-daban, duk da haka APC ta samu nasara da kuri’u 96, wannan abin kunya ne.
“Idan a shekarar 2023 APC ta lashe wannan kujerar da kuri’u sama da 4,000 kuma a shekarar 2025 APC ta lashe da kuri’u 96 kawai, hakan na nufin jam’iyyar ta rasa tasirinta a Nijeriya,” in ji shi.
Yohanna ya bayyana cewa Atiku ne kawai dan takara da ke da karfin doke APC a zaben shugaban kasa na 2027.
“Manufofin gwamnatin yanzu na yin kamfen ne wajen kalubalantar dawowar Tinubu. Ta yaya za mu ci gaba idan gwamnati ta ce mutum daya zai iya cire kudi na naira 500,000 a mako daya kawai, kuma kungiyoyin kasuwanci su kuma naira 10,000,000 a mako? Tinubu ya jawo koma baya ga kasar nan,” in ji shi.
Ya yi kira ga mambobin ADC su yi rajistar katin zabe, yana cewa hakan shi ne mabudin cire Shugaba Tinubu daga ofis.
“Wadanda ke sa ran yin magudi a zaben 2027 za su ji kunya lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta fitar da sakamakon zabe,” in ji shi.
Yohanna ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su kare kuri’unsu ta hayar da shari’a ta taada don amfanin dimokuradiyya, yana gargadin cewa tsarin jam’iyya guda zai sanya dimokuradiyya a cikin mawuyacin hali.
Bisa ga zaben kananan hukumomi na Jihar Adamawa, ya tabbatar wa mambobin jam’iyya cewa ADC za ta lashe dukkan kujerun shugabancin kananan hukumomi 21 da dukkan mazabun da ke jihar baki daya.














