Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci al’ummar Arewacin Nijeriya da su goyi bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Shettima ya tabbatar wa ’yan Arewa cewa Tinubu zai ci gaba da aiki domin ci gaban yankin idan ya sake lashe zaɓen.
Ya buƙaci al’ummar Arewa da ka da su ji tsoron sake zaɓen Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar yana ƙaunar yankin kuma yana da niyyar kawo masa ci gaba.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, inda ya yi kira ga ’yan Arewa da su haɗa kai tare da mara wa gwamnatin Tinubu baya.
Ya ce, “Mu haɗa kai a matsayin al’umma, mu yi aiki domin ci gaban yankinmu da kuma inganta rayuwar al’ummarmu ta hanyar sake zaɓen wannan gwamnati.”
Shettima ya ƙara da cewa tuni ’yan Nijeriya suka fara ganin amfanin manufofin gwamnatin, kuma za su iya samun ƙarin alheri idan Tinubu ya sake komawa kan mulki.
Ya ce, “Ina tabbatar muku cewa shugaban ƙasa yana ƙaunar Arewa kuma zai ci gaba da yi wa Arewa aiki.”
Ana sa ran Tinubu zai fuskanci hamayya mai ƙarfi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar ADC, wanda shi ma ɗan Arewa ne.
Akwai Rabiu Kwankwaso, wanda shi ma ɗan Arewa ne, a matsayin wani jigo a siyasar ƙasar gabanin zaɓen 2027.














