A ranar 3 ga watan Satumba, Sin ta gudanar da babban bikin faretin soja a birnin Beijing, don tunawa da cika shekaru 80 da yakin da Sinawa suka yi da mamayar Japan kana yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan bikin faretin soja ya nuna sabbin makamai na zamani na Sin, wadanda suka nuna ci gaban fasahohin tsaron kasar.
Bikin da kuma kayayyakin aikin soja na zamani sun sa wasu mutane shakku: Shin Sin za ta kama hanyar nuna fin karfi? Amsar ita ce, a’a. Kamar yadda wani soja da ya halarci bikin ya ce: “Ba karfi muke nuna ba, sai dai niyyarmu ta kare adalci.”
A wannan bikin faretin soja, rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya, ya ja hankalin al’umma sosai. Yawancin sojojin da ke cikin wannan rukuni sun taba yin aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya, kamar Sudan ta Kudu, Lebanon, Liberia, Mali, da Jamhuriyar dimokuradiyyar Kongo. Bugu da kari, wannan shekara ce ta cika shekaru 35 da sojojin Sin suka fara shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin za su ci gaba da kare zaman lafiya a duniya bisa kwarewarsu.
Kwarewar yaki ita ce take iya hana yaki. Kasar Sin ta bunkasa sojojinta ba don nuna fin karfi ne, sai dai don hana yaki, kuma ba don nuna barazana ba, amma don kare zaman lafiya. Daga samar da ka’idoji biyar na yin zama tare cikin lumana har zuwa “kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil Adam,” daga shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na duniya har zuwa sa kaimin kaddamar da kotun sulhu ta duniya, kullum kasar Sin ta kasance mai kiyaye zaman lafiya da kuma mai kiyaye tsarin duniya.(Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp