Babban Shugaban Hukumar Kula da ke Kula da Harkokin Man Fetur da ake Hakowa na Kan Tudu Injiya Gbenga Komolafe ya bayyana cewa, bisa ingantattaun sauye-sauyen da aka samar a kasar nan, na kara bunkasa tattalin arzikin kasar, sun sanya Nijeriya ta samu dala biliyan 18.2 a bangaren zuba hannun jari.
Hakan na kunshe ne, a cikin sanarwar da Hukumar ta fitar, inda sanarwar ta ce, ana kuma sa ran hako ganguna Man Fetur biliyan 1.4 da kuma wasu ganguna biliyan 5.4 na Iskar Gas.
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- Ƴan Bindiga Sun Harbe Wanda Suka Sace Saboda Rashin Isassun Kuɗi A Asusunsa
Sanarwar ta kara da cewa, ana kuma sa ran hako ganguna 591,000 na Man a kullum da kuma wasu ganguna 2.1 na Iskar Gas.
Hakan zai kuma kara sanya burin da ake da shi, na samar da sarrafa ganguna miliyan uku na danyen Mai.
Komolafe wanda ya bayyana hakan a wani taro mako na Mai na Afrika da ya gudana a babban birnin Accara na kasar Ghana, ya kara nuna kokarin da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ke ci gaba da yi, na cimma kuurin da gwamnatinsa ta sanya a gaba.
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana.
Ya ci gaba da cewa, sabon sauyen da aka samar a kasar nan a karkashin dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 ta samar da sabon sauyi, a bangaren gudanar da shugabanci na gari.
Shugaban ya kara da cewa, Hukumar musamman a karkashin shugabancin shugaba Tinubu, ta kara zagayewa wajen sanya ido sosai a fannin na sarrafa Mai da Iskar Gas.
Ya ce, Hukumar kusana a cikin shekaru hudu da suka gabata, ta samar da sabbin ka’idoji sanya ido guda 24 a fannin sarrafa Mai da Iskar Gas, inda ya zuwa yanzu, guda 19, aka sanya su a cikin kundin gudanar da ayyuka.
A cewarsa, Hukumar ta kuma kaddamar da cikakken shiri na RAP, wanda ya yi daidai da tsarin dokar ta Masana’antar Man Fetur ta 2021, wanda hakan ya taimaka wajen magance kalubalen da ake fuskanta da kuma tabbatar da ana samar sa Lasisi, a cikin sauki.
Ya kara da cewa, an samu sakamako mai kyau a shirye-shiryen da Hukumar ta kirkiro da su, inda Jaren Ruwan dakon Man suka karu daga takwa zuwa 43 daga watan Satumbar 2021 zuwa watan Satumbar 2025.
“A 2025 kadai Hukumar ta amince da sabbin ayyukan bunkasa FDP guda 28 domin a ci gajiyar gangunan Mai miliyan 1.4 da kuma Iskar Gas 5.4, inda kuma ake sa ran samun gangunan Mai guda 591,000 a kullum da kuma karin wani Iskar Gas 2.1,” A cewarsa.
“Wannan ayyukan na FDP wanda ya kai na dala biliyan 18.2 hakan ya nuna kokarin da ake yin a janyo masu zuba hannun jari a fannin hako da Man na kan Tudu,” Inji Shugaban.
Ya kara da cewa, sauran sun hada da, aikin dala biliyan biyar na FID wanda ake gudanarwa a arewacin Bonga da kuma aikin dala miliyan 500 na Gas da ake yi a yankin Ubeta tare da kuma karin wani akin ne FID kamar na yankunan Ima Gas, Owowo da kuma na Preowei.
Ya ci gaba da cewa, bayan da shugaba Tinubu ya zama shugaban kasa, ya amince da wasu manyan ayyuka guda biyar da suka kai na sama da dala biliyan biyart, wanda hakan ya kara bayar da dama ga masu ruwa da tsaki, na cikin gida da ke a fannin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp