Jam’iyyar hadaka ta ADC, ta kaddamar da sabon hedkwatarta ta kasa da ke Wuse 2, Abuja, a ranar Litinin.
Sakataren yada labarai na jam’iyya, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a shafin sada zumunta ta Tuwita. Abdullahi ya bayyana taron a matsayin babban mataki na hadin gwiwa na kokarin jam’iyya na hidima ga gina kasa.
- Allah Ya Tsarkake Iyalan Annabi (SAW) Daga Kazanta
- Ƙungiyar IPOB Ta Yi Watsi Da Hukuncin Ɗaurin Rai-Da-Rai Ga Nnamdi Kanu
A cewarsa, an kaddamar da sabon shalkwatan ne da misalin karfe 2 na rana a gini mai lamba ta 121 Adetokunbo Ademola Crescent, Wuse 2, Abuja, kuma ‘yan Nijeriya da dama sun sami halartar taron.
Ya ce, “Wannan taron yana da matukar muhimmin ga kowa da kowa. An gayyaci kowa ya shaida wannan sabon shalkwatar jam’iyyar ADC,” in ji shi.
An dai kafa jam’iyyar ne a shekarar 2005, inda ta shiga cikin jerin manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya.
Idan za a iya tunawa dai, an sake gabatar da jam’iyyar ne a ranar 2 ga Yuli a matsayin jam’iyyar hadika don kalubalantar Shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Lokacin da aka amince da ADC a matsayin jam’iyyar hadaka, manyan ‘yan siyasa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa Dabid Mark, da kuma tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, sun shiga cikin jam’iyyar.














