… ci gaba daga makon da ya gabata.
Bugu da kari ma ya halarci bikin nadin Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta biyu a shekarar 1953, a madadin majalisar wakilai ta Nijeriya, an kuma bashi nambar girmamawa saboda samun damar halartar shi Bikin.
A shekarar 1954 ne Alhaji Isa Kaita ya tafi aikin Hajjin farko inda ya samu damar ziyartar Makka da Madina. A shekarar da ta biyoni bayanta ta 1955, aka nada shi Amirul Hajji, wato shugaba kuma jagoran Alhazan Nijeriya a kasar Saudiyya. A shekarar 1956, ce sai kuma Sarkin Katsina Usman Nagogo, ya nada shi a mukamin Sarauta ta Madawakin Katsina.
A shekarar ce kuma Sarauniyar Elizabeth ta Ingila ta ba shi lambar girmamawa ta O. B. E, duk dai a cikin shekarar ce, aka nada shi Ministan Albarkatun kasa, in da ya canji Mista. Peter Achimugu.
A shekarar 1957 ce aka nada Alhaji Isa Kaita Ministan ilimi in da ya canji Alhaji Aliyu Makaman Bida, mukamin da ya ci gaba da rikewa har zuwa ranar 15 ga watan Janairu 1966. A shekarar 1959 ce, ya kai ziyara zuwa Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, domin taimakawa wakilan Ingila a muhawarar, da suka yi lokacin da muka yi nasarar jawo hankalin duniya kan kamaru ta Arewa ta zama wani bangare na Nijeriya har ma aka rika kiran wurin da sunan Sardauna Probince masana tarihi ba za su manta da wannan ba, kai akwai ma wani mawakin Hausa da ya yi wakar North Eastern State da akwai wurin daya ambaci sunan na Sardauna Probince wato lardin da aka mai da shi Lardin Sardauna daga baya, ya kuma ambaci cewar, Maiduguri ce Hedikwatar Jihar Arewa maso gabas ko kuma North Eastern State, yanzu shiyyar ce take da Jihohi shida. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya kai ziyara zuwa kasar Amurka.A shekarar 1962 ce, aka ba shi Lambar girmamawa ta C. B. E., wadda ta fi ta O. B. E., daraja, bugu da kari a wannan shekarar ce aka nada shi mukamin Sarautar gargajiya ta Wazirin Katsina.
A shekarar 1963 ce, Alhaji Isa Kaita ya halarci taron majalisar kungiyar kasashen da Ingila ta mulka da aka yi a kasar Malaysia, ya ci gaba da zama wakilin majalisar har tsawon shekaru 14. A shekarar 1964 ce, Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar Yabo ta C. O. N. Inda kuma a ranar 22 ga watan Nuwamba 1965 ne, shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya na wancan lokacin wato Marigayi Sardaunan Sakkwato ya ba shi kyautar Digirin girmamawa na jami’ar, mai suna (Doctor, Of Laws) a Bikin saukar karatun Jami’ar na farko , daga baya kuma a shekarar 1986 ce jami’ar Bayero ta Kano ta sake bashi Digirin girmamawa irin wancan.
Ana gama shi Bikin Saukar karatun ne Alhaji Isa Kaita, ya tashi a jirgin sama daga Kaduna zuwa Legas daga can kuma ya zarce New Zealand, domin halartar taron majalisar wakilai ta kungiyar kasashen da Ingila ta mulka ko rena wanda aka yi a Washington. Alhaji Shehu Shagari, shi ma yana daga cikin wadanda suka halarci taron, ya yi kuma jawabi mai ban sha’awa game da kasar Rhodesia wadda yanzu ake kira da suna Zimbabwe.














