Darakta a Cibiyar Binciken Aikin Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Rabi’u Adamu, ya bayyana cewa; dogaro da noman gargajiya kadai, ba zai iya wadadar da kasar nan da abincin da ake bukata ba, musamman duba da karuwar yawan al’ummar da kuma yadda kasar noma ke kara lalacewa.
Ya kara da cewa, kasancewar Nijeriya da ke da yawan al’umma a nahiyar Afirka, amma ana noma tan miliyan 12.4 na Masara ne kadai, wanda hakan ya gaza da tan miliyan 18 da kasar ke bukata.
- An Yi Jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Sanya Dokar Ta -Ɓaci Kan Tsaro Bai Da Amfani – Datti Baba-Ahmed
Haka zalika, Farfesan ya yi nuni da cewa; za a iya cike wannan gibin ne kadai, idan gwamnatin tarayya ta amince da gabatar da shuka ingantaccen Irin Masara, mai saurin girma tare da kuma jurewa kowane irin yanayi da kuma jurewa kamuwa da kwari da lalata amfanin gona.“Har yanzu, akwai bukatar Nijeriya ta kara yawan adadin amfanin gonar da ake nomawa a kasar,” in ji Farfesan.
Hak nan, a kan batun tantamar da wasu ke da ita na shafar lafiyar jama’a wajen amfani da Irin da aka sarrafa a zamanance, wato GMO, Farfesan ya bayyana cewa; hatta amfanin gonar da ake shigowa da shi daga ketare zuwa cikin kasar nan, sai an tabbatar da hukumomin da abin ya shafa sun tantance su, domin tabbatar da cewa; ba za su shafi lafiyar mutane ba, kafin a sahale sayarwa mutane. Ya sanar da cewa, wasu alkaluman bincike sama da 200 da aka gudanar kan nau’in na GMO, Tarayyar Turai da kasar Amurka da kuma wasu kasashen da ke Afrika, sun bayyana cewa; kan nau’in na GMO, wanda hakan ya tabbatar da sahihancin, wannan nau’in tare da kuma sahalewar, ana iya cin amfanin gonar da aka shuka aka kuma noma ba tare da wata matsalar shafar lafiyar jama’a ba.
Kazalika, ya kara da cewa; babu wani rahoto da ya fito daga Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya da kuma Sashen Kula da Aikin Noma na Majalisar Dinkin Duniya, suka bayyana cewa; yin amfani da wannan nau’in, na shafar lafiyar jama’a da kuma ta dabbobi. Ya yi nuni da cewa, a yanzu haka, akwai irin wannan nau’in da ake ci gaba da amfani da shi, wanda aka shuka Masara da Tumatir da Waken Soya, wadanda kuma ake sayarwa a kasuwanin kasar nan.
“Yin amfani da wannan nau’in ne ya bai wa Nijeriya kwarin gwiwar shiga cikin yarjejeniyar Geneba, musamman domin kasar ta bayar da umarnin a rika yin amfani da nau’in a wajen yin noma.
Ya kara da cewa, hatta ita kanta Nijeriya, ta sahale wa manoma amfani da wannan nau’in, wanda a farko ta amince kan yin Auduga samfurin Bt a shekarar 2020 da noman farin Wake samfarin SAMPEA 20T a shekarar 2021, sai kuma noman Masara samfarin Tela maize, a shekarar 2024.














