Sakamakon sace dalibai a makarantun sakandare na Jihohin Kebbi da Neja da wasu jihohin da kuma na gwamnatin tarayya, ya sa daukar matakan rufe wasu makarantu a Arewacin wannan kasa.
An dauki wadannan tsauraran matakai ne, kan damuwar da ake da ita game da yadda matsalar sace dalibai ta sake kunno kai a Nijeriya, a cewar hukumomin.
- Kuskure Ne Tattaunawa Da Ƴan Bindiga, Yafi Dacewa A Nemi Tallafin Ƙasashen Waje – Obasanjo
- An Bukaci ‘Yansanda Da Likitocin Dabbobi Su Samar Da Tsaro Ga Fannin Kiwon Dabbobi
Har ila yau, a ranar Alhamis ne da dare; wasu ‘yan bindiga suka far wa sakandiren da ke Jihar Neja dauke da muggan makamai tare da sace dalibai fiye da 300 da kuma malamansu su kimanin 12.
Kazalika, kafin wannan, ‘yan bindigar sun sace dalibai mata 25 a wata makarantar sakandare da ke garin Maga ta Karamar Hukumar Danko da Wasagu a Jihar Kebbi, duk da cewa; biyu daga cikinsu sun samu damar kubuta daga hannunsu.
Babu shakka, wadannan matakai na rufe makarantu; sun yi matukar haifar da dimuwa tare da firgici a tsakanin al’uumar kasar nan, amma hukumomi na cewa; wannan wani shiri ne na kaucewa jefa yara da iyayensu cikin wani mummunan hali.
Haka zalika, Gwamnatin Nijeriya ta bayar da umarnin rufe makarantun hadaka na tarayyar Nijeriya kimanin 41 da ke kasar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar, ta bayyana cewa; Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya bayar da umarnin rufe makarantun hadaka kimanin 41 na tarayya, ba tare da wani bata-lokaci ba.
Har ila yau, Ministan ya ce; sakamakon sabon kalubalen tsaro da ya kunno kai a wasu sassa na Nijeriya, ya zama dole a dauki matakin da ya dace.
Sanarwar ta kuma bukaci shugabannin makarantun da abin ya shafa, da su tabbatar da aiwatarwa tare da bin wannan umarni nasa sau-da-kafa.
Duk da cewa, sanarwar ta yi nuni da cewa; rufe makarantun na wucin gadi ne, amma ba ta sanar da ranar da za a bude su ba.
Rahotanni sun nuna cewa, a makon da ya gabata ne Nijeriya ta yi fama da hare-hare mafi muni a kan makarantu cikin kankanin lokaci.
‘Yan bindiga sun far wa makarantar kwana ta ‘yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi tare da sace dalibai 25 a ranar Litinin.
Har ila yau, kwanaki kalilan bayan nan, a ranar Juma’a kuma, sai wasu ‘yan bindiga suka shiga makarantar kwana ta St Mary da ke garin Papiri a Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja, a kan babura suka sace dalibai da malamai da ake hasashen sun kai kimanin 300.
Kazalika, har yanzu ‘yan kasar na ci gaba da bayyana fushinsu kan yadda ake ci gaba da samun karuwar hare-hare a makarantu da kuma sace kananan yara.
Sai dai, har yanzu gwamnatin kasar na nanata cewa; tana daukar matakan dawo da wadanda aka sace, amma har yanzu ba ta kai ga yin nasara ba, koda-yake dai; akwai wadanda rahotanni suka bayyana cewa; sun samu damar tserewa.
Wannan ne ya sa jihohin da lamarin ya shafa, da ma wasu jihohin da ke makwaftaka da su ko wadanda ke fama da matsalar tsaron, suka fara daukar matakin kariya ta hanyar rufe makarantun jihohin nasu, musamman makarantun kwana.
Jihohi Takwas Da Suka Rufe Makarantun Sakamakon Matsalar Tsaro:
Jihar Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da rufe dukkanin makarantun jihar na gwamnati da kuma na masu zaman kansu, sakamakon wannan matsala da ta kunno kai ta sace dalbai.
Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, da takwararsa ta ilimi a matakin farko, Dakta Halima Bande suka fitar, sun bayyana cewa; matakin ya kunshi makarantun sakandire da na gaba da sakandire da ke fadin jihar.
Sanarwar ta ce, matakin ya zama wajibi sakamakon samun matsalar hare-hare cikin wasu sassan jihar a baya-bayan nan.
Har ila yau, matakin ya shafi dukkanin manyan makarantun jihar, amma ban da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma na binrnin na Kebbi, kamar yadda sanarwar ta yi karin haske.
Jihar Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rufe dukkanin makarantun sakandire na fadin jihar, sakamakon matsalar tsaro da kuma satar dalibai a wasu jihohin.
Kwamishinan ilimi na jihar, Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya, ya bayyana cewa; gwamnatin ta dauki matakin ne, sakamakon matsalolin da ke afkuwa a makwabtan jihohin, na satar dalibai.
“Wannan dalili ne ya sa muka kara tsananta matakan tsaron da muke dauka da su a makarantunmu, domin kuwa masu iya magana na cewa; idan gemun dan’uwanka ya kama da wuta, sai ka shafa wa naka ruwa”, in ji shi.
Kwamishinan ya kara da cewa, wannan rufe makarantu; na wucin gadi ne, da zarar komai ya lafa; za su umarci daliban su koma makarantunsu, domin rubuta jarrabawar karshen zango, wadda ita ce a halin yanzu damar da ta rage.
Haka zalika, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya shafi dukkanin makarantun sakandiren da ke fadin jihar, amma ban da na firamare, duk da cewa; a cewar tasa su ma idan hali ya yi za su iya rufe su.
Ya kuma yi karin haske a kan cewa; sun dauki wannan mataki ne domin kariya, saboda bai kamata a hango matsala a nesa; sannan kuma a tsaya har sai ta karaso inda kake ba, babu shakka, yin hakan zai iya zama ganganci.
Jihar Filato
Ma’aikatar ilimi ta Jihar Filato ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun jihar na firamare da sakandire, sakamakon karuwar matsalar satar dalibai a kasar.
Hukumar ilimi a matakin farko ta jihar (PSUBEB), ta bayyana daukar matakin, a matsayin matakin kariya ga daliban jihar.
Haka zalika, ma’aikatar ilimin jihar ta ce, matakin na wucin-gadi ne; sannan kuma ya zama dole a yi la’akari da halin da ake ciki a halin yanzu na firgici da kuma dimuwa.
Cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar makarantu, su yi biyayya ga wannan umarni.
Bugu da kari, matakin ya shafi dukkanin makarantun sakandire da kuma firamaren da ke fadin jihar.
Kazalika, batun sace mutane don neman kudin fansa da ‘yan bindiga ke yi a Nijeriya, ya zama gagarumar matsalar da ke matukar ci wa al’ummar kasar tuwo a kwarya a wurare daban-daban na fadin kasar.
Duk kuwa da cewa, hukumomin kasar na cewa; suna daukar matakai iri daban-daban tare da halaka wasu daga cikin manyan ‘yan bindigar da suka addabi Jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Kebbi.
Haka nan, a baya-bayan nan; an samu dawowar hare-hare kan makarantu tare da sace dalibai, bayan kwashe kimanin shekara guda da samun saukin al’amarin.
Jihar Yobe
Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun sakandiren kwana da ke fadin jihar, sakamakon barazanar tsaro, musamman na sace daliban makaranta.
A cikin wata sanarwa da babban darakta yada labaran gwamnan jihar ya fitar, Mamman Mohammed, ya bayyana ce; gwamnatin ta dauki wannan mataki ne, domin kare daliban da ke makarantun kwana na fadin jihar.
Har ila yau, sanarwar kara da cewa; an dauki matakin ne bayan taron koli na tsaron jihar da Gwamnan Mai Mala Buni ya jagoranta, domin nazarin tsaron makarantu a wasu sassa na kasar.
Jihar Kwara
Gwamnatin Jihar Kwara, ita ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun da ke wasu kasanan hukumomi hudu da ke fadin jihar.
Har ila yau, kungiyar malamai ta kasa (NUT), reshen jihar ta Kwara ce ta sanar da matakin, sakamakon karuwar matsalar tsaro a wasu yankunan sassan kasar.
Shugaban hukumar, Yusuf Agboola, ya bayyana cewa; an rufe makarantu a Kananan Hukumomin Isin da Irepodun da Ifelodun da kuma Ekiti.
Jihar Neja
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da rufe dukkanin makarantunta da ke fadin jihar, sakamakon sace wasu daliban makarantar St. Mary mai zaman kanta a garin Papiri na Karamar Hukumar Agwara.
Gwamnan Jihar Umaru Bago ne ya sanar da hakan, yayin da yake zanta wa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar.
Har wa yau, Bago ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da ceto daliban tare da maido da su cikin kwanciyar hankali cikin iyalansu.
Jihar Taraba
Gwamnatin Jihar Taraba ta bai wa dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu na kwana, umarnin komawa tsarin jeka-ka-dawo, sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro da ta sake kunno kai.
Cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar a shafinta na D, ta bayyana cewa; matakin ya biyo bayan wani nazari da ta yi a kan tsaro, wanda ya duba lamuran da suka faru a baya-bayan nan a Jihohin Kebbi da Neja.
Har ila yau, ta kara da cewa; rahoton nazarin ya nuna daliban makarantun kwana a matsayin wadanda suka fi zama cikin barazana na satar daliban.
Jihar Bauchi
Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkanin makarantun firamare da sakandire da manyan makarantu na gwamnati da kuma masu zaman kansu.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce; ta dauki matakin ne, biyo bayan shawarwari masu zurfi, sakamakon matsalolin tsaron da ke shafar dalibai da malamai da kuma makarantu baki-daya.
A bangare guda kuma, gwamnatin Nijeriya ta musanta rahotonnin da ta ce ana yadawa da ke nuna cewa; ta umarci a rufe makarantu a dukkanin fadin kasar daga ranar Litinin din da ta gabata.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar ta bayyana cewa, wannan rahoto ko kadan ba gaskiya ba ne.
Rahoton ya ci gaba da cewa, sanarwar ba daga gwamnatin tarayya ko ma’aikatar ilimi ko wata hukumar tsaro take ba.














