’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Irunda Ile da ke Yagba ta Gabas, a Jihar Kogi, da safiyar ranar Laraba, inda suka kashe ’yan sa-kai biyu.
Bayan kai harin, matasa sun yi zanga-zanga saboda yawan hare-haren da ake fama da su a yankin.
- Sin Da Rasha Sun Bukaci A Kare Nasarar Da Aka Samu Daga Yakin Duniya Na II
- Yadda Aka Ba Mu Labarin Wata Fasahar Fenti Mai Tarihin Fiye Da Shekaru 900 A Kasar Sin A Aikace
Ganin hakan, lokacin da ’yansandan suka iso, matasan suka nemi su bi ’yan bindigar cikin daji.
Rikici ya ɓarke, kuma ’yansanda suka kashe matasa biyu bisa kuskure, sannan da dama suka jikkata saboda hayaƙin barkonon tsohuwa.
Shugaban al’ummar yankin, Cif David Oni Sunday, ya tabbatar da cewa “’yan bindiga sun kashe ’yan sa-kai biyu, sannan ’yansanda sun kashe wasu matasa biyu bisa kuskure.”
Mai bai wa Gwamnatin Kogi shawara kan harkokin tsaro, Kwamanda Jerry Omadora (mai ritaya), ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce jami’an tsaro na aiki sosai don fatattakar ’yan bindiga, kuma sun kashe wasu daga cikinsu a kwanakin baya.
Ya ce gwamnati ba za ta bari ’yan ta’adda su samu wajen zama a jihar ba.














