Assalamu alaikum. Malam, mene ne hukuncin sallar mutanen da suka tarar an idar da sallah a masallacin da ke da tabbataccen limami, suka yi tasu sallar a jam’i?
Wa’alaikum assalam. Malamai sun cimma daidaito a kan halaccin yin jam’i biyu a masallacin da ba shi limami Ratibi, kamar masallacin tasha da na kan hanya, sai dai sun ƙara wa juna sani game da masallacin da yake da tabbataccen limami zuwa zantuka guda biyu:
- Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano
- Fityanul Islam Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Da Ake Shirin Yi
- Makaruhi ne yin hakan, saboda Annabi SAW ya taɓa zuwa masallacinsa mai alfarma, sai ya samu an yi sallah, sai ya juya, ya yi sallah a gida, Haisami ya ambaci wannan hadisin a cikin Majma’uzzawa’id, kuma ya ce; maruwaitan hadisin amintattu ne.
- Mustahabbi ne yin jam’i na biyu a masallacin da yake da limami Ratibi, sun kafa hujja da hadisin da wani mutum ya zo masallacin Harami, bayan an gama sallah, sai Manzon Àllah ya ce; “Wane ne zai yi sadaka ga wannan mutumin, ya yi sallah tare da shi”?, sai wani sahabi ya tashi ya taimaka masa, suka yi sabon jam’i da izinin Manzon Tsira SAW, kamar yadda Abu Dawud da Tirmizi suka rawaito.
Magana ta biyu ta fi inganci, saboda nassin da suka kafa hujja da shi kaifi ɗaya ne, ga kuma tarin hadisan da suke magana a kan falalar sallar jam’i.
A ilimin USULU, nassin da yake kaifi ɗaya; ana gabatar da shi a kan nassin da yake ɗaukar sama da ma’ana ɗaya.
Komawar Annabi SAW gida, yana ɗaukar fuskoki da yawa, zai yiwu Manzon tsira ya koma gida ne, saboda duba maslaha, da ya yi jam’i na biyu, da wasu sun sake sallah, hakan kuma yana iya buɗe ƙofar zace-zace a kan limamin farko.
Allah ne mafi sani.














