ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta’addanci: Ko Matakan Shawo Kan Taɓarɓarewar Tsaro Za Su Yi Tasiri?

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
2 weeks ago
tsaro

A yayin da yankin Arewa ke ci-gaba da kamawa da wuta ba ƙaƙƙautawa a bisa ga ƙaruwar taɓarɓarewar sha’anin tsaro; shugabannin Arewa da al’ummar ƙasa na ci-gaba da nuna damuwa kan yadda yankin Arewa ya zama tarkon mutuwa.

A baya- bayan nan mayaƙan ISWAP da Boko- Haram a Arewa- Maso- Gabas da ɓarayin daji a Arewa- Maso- Yamma da Arewa ta Tsakiya sun ƙara zafafa kai hare- haren ta’addanci, garkuwa da ɗalibai da kisan gillar jami’an tsaro ta hanyar fito na fito da hukumomin tsaro tare da cin karen su ba babbaka.

  • Borno Ta Kashe Naira Biliyan 100 Kan Samar Da Tsaro A 2025 – Gwamna Zulum
  • Ƴan Majalisar Dokokin Amurka Da Na Nijeriya Sun Gudanar Da Taro Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro

Nijeriya wadda ta kasafta kashe naira tiriliyan 2.98 a sha’anin tsaro a kasafin kuɗin 2023 da naira tiriliyan 3.25 a 2024 da kuma naira tiriliyan 4.91 a 2025 duk da jajirtattun jami’an soji amma jama’a na kuka da kokawar rashin gani a ƙasa a bisa ga yadda ake ci-gaba da fuskantar mummunan ƙalubalen taɓarɓarewar sha’anin tsaro ta yadda dubun- dubatar al’umma ke bacci da idanu ɗaya.

ADVERTISEMENT

tsaro

Kisan gillar da mayaƙan ISWAP suka yi wa babban jami’in sojin Nijeriya Birgediya Janar Musa Uba ba tare da ceto rayuwarsa ba duk da samun rahoton halin da  yake ciki gabanin faruwar bahagon lamarin ya nuna rayuwar jami’an tsaro na cikin haɗari mafi muni.

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Sace ɗalibai mata 24 a Maga da ke Kebbi, da yadda ‘yan ta’addan suka kai farmaki a sakandiren katolika da ke Papiri a jihar Neja suka yi awon gaba da ɗalibai 300 da malamai 12 ya nuna kasawar hukumomin tsaro wajen sauke nauyin da ke kan su.

Ta’addancin bai tsaya a nan ba domin kuwa wasu mayaƙan sun kai farmaki a cocin CAC a jihar Kwara a inda suka kashe mutane biyu da ke ibada da garkuwa da mutane 38, sai dai an samu ceto su bayan kwanaki.

Garkuwa da ɗaliban ta tilasta rufe makarantu da dama a jihohin Kebbi, Bauchi, Yobe, Adamawa, Taraba, Filato, Neja, Kastina da Kwara a bisa ga barazanar abin da zai iya biyowa baya.

A kan hakan gwamnatin tarayya ta rufe makarantun sakandiren haɗin guiwa na tarayya 41 a faɗin ƙasa domin kare ɗaliban daga farmakin da ‘yan ta’addan ke iya kaiwa a kowane lokaci.

Dokar Ta Ɓaci

A bisa ga yadda matsalar tsaro ta kasa ci ta kasa cinyewa da yadda al’ummar ƙasa ke neman ɗauki ne dalilin da ya sa Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro da manufar kakkaɓe ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

Tuni dai al’ummar ƙasa suka yabawa matakin gwamnatin tarayya na kafa dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro da zummar sake ɗaura ɗamara da sa ƙafa wando ɗaya da ‘yan ta’addan da suka jima suna gasawa jama’a aya a tafin hannu.

Daga cikin matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka kan dokar agajin gaggawa kan sha’anin tsaro akwai baiwa rundunar ‘yan sanda damar ƙarin ɗaukar jami’ai 20, 000 ta yadda adadin jami’an za su koma dubu 50, 000.

Sai dai kasancewar adadin jami’an ‘yan sanda bakiɗaya a matakin ƙasa bai wuce 300, 000 ba da ke kariyar al’umma sama da miliyan 250, masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro na ganin akwai buƙatar ɗaukar dubban ɗaruruwan jami’an a kowace shekara domin yaƙi da matsalar tsaro yadda ya kamata.

Haka ma jama’a na bayyana cewar jaye jami’an ‘yan sanda daga bayar da kariyar manyan mutane da shugaba Tinubu ya yi muhimmin mataki ne da ya zo daidai lokacin da ya kamata musamman kasancewar babu wadatattun jami’an tsaro da za su tunkari matsalar tsaro gadan- gadan.

Bugu da ƙari shugaban ya kuma buƙaci Majalisar Ƙasa da ta fara aikin tabbatar da dokokin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi da aka jima a na cece- kuce a kai domin shawo kan yawaitar ayyukan ta’addanci a faɗin ƙasa.

Dokar ta ɓacin ta kuma bayar da umurni ga hukumar jami’an tsaron farin kaya na DSS da ta tura jami’an tsaron gandun daji a cikin dazuka domin artabu da ‘yan ta’adda da ɓarayin daji tare da ɗaukar sababbin jami’ai domin tunkarar miyagun da ke aika- aika a cikin duhun daji.

Matakin shugaban ƙasa ya nuna sabon ƙudurin sake fasalin tsarin tsaron ƙasar bakiɗaya ta hanyar ƙara yawan jami’ai, inganta hanyoyin leƙen asiri da daidaita dabarun tsaro domin fuskantar sabbin barazanar da ke tasowa.

A cikin manyan sauye- sauyen da ake shirin aiwatarwa, Shugaban Ƙasa na ƙoƙarin ganin an samar da dokokin da za su ba jihohi damar kafa ’yan sandar jiha, matakin da masana ke ganin zai ƙarfafa sha’anin tsaro a jihohi da ƙananan hukumomi.

Sai dai akasin nuna goyon bayan gwamnati kamar yadda suka saba, mafi yawan wakilan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun soki matakin gwamnatin tarayya kan daidaitawa da ‘yan ta’adda wajen biyan kuɗin fansar waɗanda aka yi garkuwa da su a a jihohin Kwara da Kebbi.

‘Yan majalisar sun buƙaci gwamnati ta dakatar da sulhu da ‘yan ta’adda tare da ɗaukar matakin ladabtarwa ga jami’in da ya ba da umurnin jaye jami’an tsaro da ke hadin makarantar ‘yan mata ta Maga da ke Kebbi wanda ya zama silar garkuwa da ɗalibai 24 a watan Nuwanba. Sai dai gwamnatin tarayya ta kare sulhu da ɓarayin dajin ta hanyar bayyana cewar ta ɗauki matakin ne domen kare ɗaliban daga kowace irin cutarwa.

Bugu da ƙari a na gani da kallon murabus ɗin Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar a kwanan nan da maye gurbin sa da tsohon babban hafsan sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ƙasa da kwana ɗaya wani mataki ne da Shugaba Tinubu ya ɗauka domin ƙalubalantar matsalar tsaron gadan- gadan.

Sai dai a yayin da jama’a da dama ke tambayar dalilin sake baiwa Janar Musa babban muƙamin a makwanni biyar bayan cire shi daga shugaban hafsan sojoji, wata ƙwaƙƙwarar majiya ta bayyanawa manema labarai cewar mataki ne da Tinubu ya ɗauka domin bunƙasa sha’anin tsaro.

Ƴan Majalisar Dokokin Amurka Da Na Nijeriya Sun Gudanar Da Taro Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro

Ta’addanci: Ko Matakan Shawo Kan Taɓarɓarewar Tsaro Za Su Yi Tasiri?

Majiyar ta bayyana cewar wasu Ministoci da ke kusa da Tiinubu sun ba shi shawarar sanya ɗaya daga cikin tsofaffin sojoji da ke da ƙwarewa da gogewa a matsalar tsaro da ke addabar ƙasa a matsayin ministan tsaro

A yayin da aka tuntuɓi ra’ayin Birgediya Janar Muhammad Kabir Galadanchi (mai ritaya) ya bayyana cikakken tabbaci kan ƙwarewar Janar Musa wajen tallafawa shugaban ƙasa wajen magance matsalolin tsaro a Nijeriya.

Ya ce “Muna buƙatar wanda ke da cikakkiyar fahimtar rundunar soji da ayyukan ta domin taimakawa Shugaban Ƙasa wajen aiwatar da yawancin manufofin da suka shafi magance matsalar tsaro kuma Janar Musa na da cikakken horo da laƙantar dabarun magance wannan matsalar.”

Ya ce “Musa ya taɓa kasancewa kwamandan Depot wato cibiyar rundunar sojoji a inda ake horas da sojoji domin shiga fagen yaƙi, ya kuma kasance kwamandan yaƙi da abokan gaba, babban jami’in runduna, sannan daga baya ya zama shugaban rundunar tsaro ta ƙasa waɗanda suka nuna Janar Musa na da duk wata ƙwarewa da ake buƙata.” Ya bayyana.

Sai dai daga cikin ƙalubalen da ake ganin zai fuskanta shi ne yawaitar matsalolin tsaro a Arewa- maso- Yamma, ƙaruwar ayyukan Boko- Haram da suka sake kunno kai a Arewa- maso- Gabas tare da sake ɓullar ayyukan ta’addanci a Arewa ta Tsakiya da ƙarin sace-sace a jihohin Kudu-maso- Kudu kamar Edo da Delta da kuma wasu sassan Kudu- maso Yamma.

Sai dai akwai masu ra’ayin a bisa ga zamansa babba a kan dukkanin shugabannin hukumomin tsaro hakan zai taimaka masa ba tare da samun wani saɓani tsakaninsa da waɗanda za su yi aiki a tare.

A bayyane yake dai bayyana sanarwar dokar ta- ɓaci kan rashin tsaro da Shugaba Tinubu ya ayyana a faɗin ƙasar ta jawo muhawara mai zafi daga ɓangarori daban- daban na al’umma da masana a arewacin Nijeriya.

Yayin da yawancin masana ke ganin shugaban ya ɗauki mataki mafi dacewa domin kakkaɓe ayyukan ta’addanci, wasu kuma na ganin akwai kuskure saboda rashin sauke Gwamnonin ta hanyar miƙa mulkin jihohin da rashin tsaro ya yi mummunan ƙamari ga tsofaffin jami’an rundunar soji domin gudanar da aikin kakkaɓe ayyukan ta’addanci domin tabbatar da tsaro da kariyar rayukan al’umma kamar yadda ya yi a jihar Ribas.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Next Post
’Yansanda Sun Kama Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano

’Yansanda Sun Kama Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.