Ministan Bunkasa Fannin Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, ya karbi bakuncin Jakadan Kasar Indonesia a kasar nan, Bambang Suharto.
Jakadan ya jagoranci tawagar mai dauke da mutum biyar da suka halarci ma’aikatar kiwon dabbobi da ke babban birnin tarayyar Abuja.
- An Bukaci ‘Yansanda Da Likitocin Dabbobi Su Samar Da Tsaro Ga Fannin Kiwon Dabbobi
- An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea
A yayin ziyarar Jakadan, sun gana da minister na musamman kan ci gaba da hada kai, a tsakanin kasashen biyu, domin kara bunkasa fannin kiwo na kasar nan da bayar da horo a fannin da kuma yadda za a yi amfani da kimiyya da fasahar zamani, domin kara habaka fannin kiwon dabbobi na kasar nan.
Maiha a jawabinsa a lokacin ziyarar ya bayyana cewa, fannin na kiwon dabbobi, ya kasance wani bangaren ne, na samar da wadataccen abinci, inda kuma ya yaba wa kasar ta Indonesia, kan ci gaba da taimaka wa fannin kiwon dabbobi na kasar nan.
Ministan ya kara da cewa, aikin fasahar zamani da ake amfani da ita, wajen samun maniyin wata saniya zuwa wata saniya, wanda ake ci gaba da gudanarwa a Jihohin Sakkwato da Kebbi, Gwamnatin Kasar Indonesian, ta taimaka da allurar da ake gudanar da aikin, kimanin 1,000, wanda ya ce; hakan ya taimaka aikin ya kai kashi 70 cikin 100, duba da yadda aka samar da ‘yan marakan shanu 20.
A abincin dabbobi da tsarin kula da lafiyarsu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cututtuka.
Ministan ya kuma bayyana kwarin guiwa kan cewa, sauran jihohin da ke kasar nan, su ma za su bi irin wannan sahu na yin kiwon dabbobi na zamani.
A nasa jawabin, Jakada Suharto ya yaba da irin salon shugabancin da ministan ke gudanarwa a ma’aikatar tare da kuma bayar da tabbacin cewa; kasar ta Indonesia, za ta ci gaba da samar da dauki ga fannin kiwon dabbobi na kasar nan.
Ya bayyana cewa, kwararru biyar da za a zabo daga ma’aikatar, za su tafi zuwa kasar ta Indonesia a mako mai zuwa, domin yi musu horo a fannin na kiwon dabbobi, wanda ya sanar da cewa; horon na daga cikin tsarin hadakar da Nijeriya ta kulla da kasar ta Indonesia.














