Babu shakka, ‘ya’yan gwanda na da matukar amfani; musamman ta fuskar magunguna iri daban-daban da suka hada da kamar haka:
Mace Mai Nakuda: A nan, mai ciki za ta samu ‘ya’yan danyar gwanda ta mayar da su gari, don haka; da zarar ta ji nakuda ta kankama, sai ta kwaba shi da manja ta rika lasa, in sha Allahu za ta haihu a cikin dan kankanin lokaci.
- Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
- Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar
Ciwon Olsa: Ga mai fama da ciwon Olsa, sai ya nemi garin ‘ya’yan gwanda cokalin shayi daya; ya zuba a kunu sau daya a rana, har tsawon kwana bakwai, za a rabu da ita da yardar Allah.
Karancin Ruwan Maniyyi: Ga masu fama da karancin ruwan maniyyi, sai su nemi garin ‘ya’yan gwanda da madara su hada su rika sha, wannan hadi na matukar kara ruwan maniyyi, musamman ga da namiji.
Ciwon Siga: Shan garin ‘ya’yan danyar gwanda cokali daya a ruwan dumi, na sauke siga cikin kankanin lokaci a jikin mutum da izinin Allah.
Hana Daukar Ciki: Ga masu son yin tsarin iyali, shan garin ‘ya’yan gwanda cokalin shayi daya a ruwan dumi bayan yin jima’i, na hana ciki ya shiga nan take.
Taifot Da Maleriya: Ana kiba ‘ya’yan gwanda a tace a ruwan, kimanin lita hudu (Galan daya), a zuba zuma kimanin cokali 10 a sha rabin kofi sau biyu a rana har ya kare, za a samu lafiya in sha Allah.
Cutar Daji (Cancer): Shan ruwan ‘ya’yan gwanda da aka kirba aka tace kofi daya a rana sau daya, yana rigakafin kamuwa da ciwon Daji kwarai da gaske.
Amma fa ban da masu jinjirin ciki ko kuma wadanda ba su da daya daga cikin wadannan cututtuka. Sannan, har masu ciwon hanta ma za su iya yin amfani da shi in sha Allahu.
Daga Taskar Dakta Salihannur














