ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rashin Bincike Ke Haifar Da Yawaitar Mutuwar Aure

by Rabi'at Sidi Bala
1 week ago

Kamar kowane mako shafin TASKIRA na zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi, rashin yin kwakkwaran bincike a yayin da ake kokarin fara yin aure tsakanin masoya guda biyu, duba da yadda a wasu wuraren ake samun yawaitar fasa aure yayin da ake tsaka da biki.

  • Wasu Kura-kurai Da Matan Aure Ke Yi ‘Yan Aiki Ke Aure Mazajensu (2)
  • Bayan Tsare Jami’an Sojin Nijeriya A Burkina Faso, Nijar Ta Sanya Tsauraran Bincike Kan Kayayyakin Nijeriya

Wannan al’amarin na kokarin zama ruwan dare gama duniya a wasu wuraren, wanda hakan ya faru ga wata baiwar Allah, inda ake tsaka da bikinta kafin daurin aure aka fasa. Sakamakon ganowa da aka yi saurayin tsohon mahaukaci ne bai dade da warkewa ba, wanda dalilin hakan ya sa aka fasa auren.

ADVERTISEMENT

Shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko laifin waye tsakanin dangin macen da kuma dangin namijin?, Ta wacce hanya ya kamata abi wajen yin bincike, idan za a aurar da ‘ya?, Me yake janyowa wasu mutanen suke kin fayyace gaskiya a lokacin da suke shirin aurar da mace ko namiji?, Wacce shawara ya kamata a bawa iyaye da kuma su ‘yan matan da ake soke auransu?.”

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

LABARAI MASU NASABA

Illolin Da Yawace-yawacen Mata Ke Haifarwa Ga Zamantakewar Aure

Matsalar Rashin Yarda Tsakanin Ma’aurata

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:

Laifi ai na iyayenta ne me ya sa basu yi bincike ba kafin azo wannan gabar. Ya kamata ace ana yin buncike kamar yadda a baya al’adar Malam bahushe ce buncike kafin Aure daga bangaren mijin har na matar. Wani yana gudun kar ya fadi aibin dansa ko ‘yarsa a karshe su rasa masu Aurensu, wanda hakan babbar matsala ce. Ka fadi gaskiya idan mutum ya ga zai iya to, shikenan in ba zai iya ba Allah ya kawo wani.

 

Sunana Khadija Auwal Koki, A Jihar Kano:

Aure

Eh to, gaskiya laifin mijin ne da kuma danginsa tunda an san maganar aure ba wasa bace ya kamata ace an fadawa juna gaskiya. Ya kamata iyaye su yi bincike da yawa, wajan tabbatar da nagarta da kuma mutuncin dan da za su bawa ‘yarsu, haka shi ma ayi bincike sosai akan yarinyar da zai aura. Da yawan mutane wasu da dama suna zabar su boye gaskiya sun fi san su fito da garya, suna ganin kamar za su fi karbuwa. Bacin ita kuma gaskiya daya ce ramin karya kuma kurarre ne. Idan har ba wani dalili ne mara kyau ba wanda ko da an yi auran za a yi da-na-sani ya sa za a fasa auran ba. To, a ganina a daina soke aure kawai ayi addu’a da fatan alkairi.

 

Sunana Hafsat Sa’eed

Aure

Tun farkon da suka fara soyayya zai aure ta, kamata yayi ayi bincike akai aga shi wane ne, kuma daga ina yake. Wani lokacin matsala daga iyaye ne, basa tsayawa su yi bincike, wani lokacin sukan dauki abin da yarinya ta zo da shi, wani lokacin akan sami akasarin matsala daga mazaje, su zo su yi maka karya su ce ga yadda suke, alhalin ba hakan suke ba. Ko kuma inda za a je a yi binciken su yi karya akan abin da za su fada, sai ka shiga gidan sai ka ga ba haka ba.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:

Aure

Kamar yadda addinin Musulunci yake koyarwa, bincike yana da matukar muhimmanci, yayin neman aure. Ba kawai binciken tushe ko asalin zuriya da tsatson wanda ake nema da mai nema ba ne, har ma da abin da ya shafi lafiya. Ma’aikin Allah (SAW) a wani hadisi ya tsawatar da sahabbansa daga auren mace daga gidan da bashi da tarbiyya ko tarihi mai kyau, komai kyanta. Don haka za mu fahimci cewa, lallai binciken dangin mata ko miji wajibi ne a addini, kodayake sau da dama soyayya da gaggawa tana rufe mana ido, da hana mu tsayawa mu yi bincike kan wadanda za mu aura. A irin haka ne ake samun zuriya da za su taso da wasu irin bakin al’amura, kamar sata, shaye-shaye, zinace-zinace da ta’addanci, wadanda masana suka ce duk ana gadonsu ne daga iyaye da kakanni. Lallai yana da kyau iyaye da masu shirin aure su natsu su daina gaggawa, su tabbatar sun zabawa ‘ya’yansu abokan zama nagari, da samun zuriya masu albarka.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu, Goben Nigeria:

Aure

Cab! Babbar magana, da farko dai Allah ya kyauta ya kuma kawo mana karshen wannan fashe-fashen auren da ake yi a zamanin nan, dan abu ne mai ciwo bayan iyaye sun gama shiryawa ‘ya’yansu, na ta yata jalje da yi mata addu’ar ubangiji ya bata wanda ya fi shi alkairi. Gaskiya mafi akasarin fasa auren zamanin nan gwajin jini, rashin amincewar zuriyoyi guda biyu, rashin yarda da juna wato zuciya na kokonto, da rashin tauhidi na arziki ko wadata. Za ki ga mutum ko gobe ne in wata asara ta hau masa sai an yi canfi ta fannin mace ko namiji. Dukka sunada laifi, Fannin makota da ‘yan’uwa, saboda soyayya ko biyan bukata da gajiyarwa zaman gwaurantaka. Shawara subi a hankali gudun rikicewar al’amari ana tsaka da yi.

 

Sunana Fatima Nura kila, A Jihar Jigawa:

Aure

A ganina laifi ne na bangaren amarya, domin matukar an yi kyakkaywan bincike komai zai bayyana, sabida bincike a aure yana da matukar amfani. Iyaye ya kama su tsananta bincike musamman wajen aikinsa da kuma garinsu da guraren da yake yawan ziyarta. Kwadayi da kuma san duniya matukar mace ko namiji tana da kudi wasu sukan ki bincike, koda wani a dangi yace ayi sai a fara hassada yake ku rabu da shi. Shawara ita ce a kodayaushe muna zurfafa bincike, musamman lamari na aure, domin rayuwa ne ake san ginawa har karshen rayuwa.

 

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Aure

Wanan matsalar na faruwa sosai wasu ba sa bincike su san wanda za su bawa auren diyar su, mafi yawanci idan mai kudi ya zo babu wani bincike sai kawai ya bashi. Yanzu kuma duniya ta canza duk in da za ka je bincike babu wanda zai gaya maka gaskiya ko an sani kuwa. Wasu suna jin tsoron yin haka saboda in tayi dadi kada ace sune. Gaskiya haka ta faru a gidanmu da muka tura bincike sai da a ka fada masa an zo bincike. Shawarata dan Allah mutane in an zo bincike kan aure su fadi tsakani su da Allah abun da suka sani kan mutun ban da karya, kada su fadi abu da ba halinsa bane. Su kuma iyayenmu Allah ya basu damar duba wanda yaransu za su aura. Bsnce basa kokari ba, amma su wara sosai, Allah ya shige mana gaba (Amin).

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Illolin Da Yawace-yawacen Mata Ke Haifarwa Ga Zamantakewar Aure
Taskira

Illolin Da Yawace-yawacen Mata Ke Haifarwa Ga Zamantakewar Aure

December 20, 2025
Matsalar Rashin Yarda Tsakanin Ma’aurata
Taskira

Matsalar Rashin Yarda Tsakanin Ma’aurata

December 7, 2025
Nijeriya
Taskira

Yadda Wasu Mahukunta Ke Amfani Da Muƙamansu Wajen Musguna Wa Al’umma

November 22, 2025
Next Post
Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji

Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.