Gwamnatin tarayya, ta nuna damuwarta kan yadda ake samun lalacewar kasar noma a fadin wannan kasa, inda ta bukaci a gagguta samar ingantattun sauye-sauye, domin bai wa kasar kariyar da ta kamata, musamman domin tabbatar da ganin an samu damar ci gaba da samar da wadataccen abinci a ƙasar.
Karamin Ministan Samar da Wadataccen Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya yi wannan kira ne a Abuja wajen taron bikin ranar kasar noma ta wannan shekara da aka gudanar a Abuja, inda ya yi nuni da cewa; ta hanyar samar da ingantacciyar kasar noma, za a samu dorarren ci gaba da kuma samun wadataccen abinci.
- Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Tara Naira Biliyan 160 A Noman Alkama
- FAO Ta Horar Da Manoma 100 Kiwon Kifi A Kano
“Ingantacciyar kasar noma, na samar da amfanin gona da ya kai kashi 95 cikin 100, wanda kuma ‘yan kasar ke amfani da shi, sai dai ya bayyana cewa; kashi 33 cikin 100 na kasar noman, kusan duk ta zaizaye,” in ji Ministan.
Ya kara da cewa, idan aka ce za a dawo da akalla kashi biyu zuwa uku na kasar noman, za a iya shafe nan da shekara 1000, ba a iya cimma hakan ba a wannan kasa.
Ministan ya kara da cewa, domin magance wannan matsala, ma’aikatar ta samar da wadataccen abinci tare da mayar da hankali kan bunkasa tsarin yin noma da suka hada da sauya yin noma zuwa wata gona da bai wa gandun dajin noma kulawar da ta kamata da sauransu.
“A watan da ya gabata, an kaddamar da shirin bai wa gonakin manoman kasar kulawar da ta kamata na kasa wato, NFSHS, wanda wasu manoma 600 da masu hadaka, suka samar da wajen da aka tsara na yin amfani da takin zamanin, domin kaucewa asarar da manoma ke yi da kuma yawan kashe kudade a wajen aikin noma.
“Shirin ya kuma hada da tanadar dakunan yin gwaje-gwajen kasar noma 774 da ke daukacin fadin kasar, wanda matasa da kuma mata ne za su tafiyar da su, tuni kuma an tanadi kayan aiki a jihohi 12 da ke kasar,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, Nijeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da suka kulla yarjejiyar ta Afirka ta samar da takin zamani a 2024, wadda aka rattaba hannu, a kasar NAIROBI, musamman domin samar da ingantaccen takin zamani tare da hadaka da abokan hadaka kamar su GIZ, AGRA, IITA, bankin duniya, shirin sasakawa na Afrika da sauransu.
Ya bayyana cewa, ana kuma kan ci gaba da gudanar da aikin gwajin kasar noma, a jihohi 12 na kasar nan, kuma an sanya wannan aiki a cikin kasafin kudi na bana.
Sabi ya bukaci a mayar da hankali, domin bai wa kasar noma kariyar da ta kamata, musamman domin kare ta daga lalacewa, wanda hakan zai iya shafar kokarin da ake yi a kasar na samar da wadataccen abinci.
A jawabinsa a wajen taron, mataimakin shugaban cibiyar nazarin kimiyyar kasar noma (NISS), Olumuyiwa James Jayeoba, ya sanar da cewa; zai yi wuya a samu amfanin gona da ake bukata, matukar kasar noma na da matsala.
Yawan samun karuwar al’umma, na kara haddasa samun zaizaiyar kasa da kuma samun gurbatar muhalli.
Ya sanar da cewa, cibiyar ta NISS na kara kokari, wajen bai wa kasar noma kulawar da ta kamata, inda ya kara da cewa; ana kuma ci gaba da samar da sauye-sauyen bai wa kasar noma, kariyar da ta kamata a karkashin aikin na NFSHS, wanda ake gudanar da shi ta hanyar sabuwar hadaka.
Ya yi kira ga masu kirkiro da dokoki da masu safiyin kasa da sauran ‘yan kasar nan, da su rungumi tsarin mutunta kasar noma, musamman domin bai wa kasar noma kulawar da ta kamata.














