ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Tara Naira Biliyan 160 A Noman Alkama

by Abubakar Abba
9 months ago
Gwamnatin

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na son tara kimanin naira biliyan 160 a noman Alkama, a yayin noman rani na 2025 zuwa 2026.

Yunƙurin gwamnatin, na daga cikin ƙoƙarin da take ci gaba da yi na ƙarfafa samar da wadataccen abinci, musamaman domin rage dogaro da abincin da ake shigo wa da shi cikin ƙasar daga ƙetare.

Abubakar Kyari, Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, ya sanar da haka ne a Jere da ke Jihar Borno.

ADVERTISEMENT

A cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, Kyari ya sanar da hakan ne a yayin ƙaddamar da kayan aikin noma cikin rahusa, a ƙarƙashin shirin bunƙasa aikin noma na ƙasa (NAGS-AP).

  • Manoman Rake Sun Tabka Asarar Kimanin Naira Biliyan Biyu A Kano
  • Jihar Kaduna Ta Ƙulla Yarjejeniyar Dala Miliyan 200 Da Ƙasar Sin Don Bunƙasa Noman Zamani

Kyari ya ce, gwamnati ta keɓe kimin hekta 40,000 tare da yi wa manoman Alkama 80,000 a ɗaukacin faɗin ƙasar, domin wanzar da shirin, wanda ake sa ran za a samar da noman Alkama da aka ƙiyasta kuɗin zai kai, na Naira biliyan 160.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Ya ƙara da cewa, Borno za ta bayar da gagarumar gudunmawa a ƙarƙashin shirin, duba da cewa; ta samar da hekta 3,000 tare kuma da yi wa manoman Alkama 6,000 rijista.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin na da yaƙinin tara naira biliyan 160, duba da nasarar ta Alkama ƙarƙashin shirin ta yadda manoman Alkamar da aka taimakawa, suka samu 107,429 a kakar noma ta 2023 zuwa ta 2024, inda aka tara naira biliyan 474.6.

Ya ƙara da cewa, a kakar noma ta 2024 zuwa ta 2025, manoman Alkama 279,297 aka taimakawa, a ƙarƙashin shirin inda aka tara naira biliyan 893.7.

Kyari ya ci gaba da cewa, shirin na 2025 zuwa 2026; zai mayar da hankalin ne, wajen ƙara ƙarfafa samar da kayan aiki tare da kuma tabbatar da cewa, an samar wa da manoman Alkamar ingantaccen Irin Alkamar takin da takin zamani tare kuma  da cewa, kayan sun isa ga manoman.

Kazalika, Ministan ya sanar da cewa; za a tura Malaman aikin zuwa ɗaukacin faɗin ƙasar nan, musamman domin su koyar da manomanta na zamani.

Bugu da ƙari, a ƙarƙashin wannan shiri na NAGS-AP, za a faɗaɗa shi, zuwa jihohi 16 da suka haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Kuros Riba, Gwambe, Kaduna, Kano, Kebbi, Neja, Filato, Sokoto, Taraba, Yobe da kuma  Zamfara.

Wannan ne karo na farko da aka sanya Jihar Kuros Riba a cikin wannan jerin jihohin.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yaba wa gwamnatin tarayya kan ci gaba da zuba jari a fannin  noman rani na Alkamar.

Gwamnatin
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Abubuwan Da Suka Kamata Mata Su Sani Game Da Mazajensu (3) 

Abubuwan Da Suka Kamata Mata Su Sani Game Da Mazajensu (3) 

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.