Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta karɓa ko sauya makarantar ɗalibai kai tsaye zuwa aji na uku na babbar sakandare (SS3) a duk faɗin ƙasar nan, a makarantu masu zaman kansu da na gwamnati. Sabon matakin zai fara aiki ne daga zangon karatu na shekarar 2026/2027.
Sanarwar, wadda Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta sanya wa hannu, ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin daƙile yawaitar maguɗin jarrabawa da ke ƙara taɓarɓara martabar tsarin ilimi a Nijeriya.
- Sabon Tsarin Harajin Tinubu: An Warware Zare Da Abawa
- Ranar Bikin Kasar Noma Ta Duniya: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Bai Wa Kasar Noma Kariya
Ma’aikatar ta nuna damuwa kan amfani da abin da ta kira “cibiyoyi na musamman” da kuma wasu dabaru rashin ɗa’a a lokacin jarrabawar kammala sakandare, inda ta ce sau da yawa ana sauya ɗalibai zuwa SS3 ne domin samun nasara a jarrabawa. Saboda haka, daga yanzu karɓa da sauya ɗalibai za a na yi ne kawai a matakan SS1 da SS2.
Gwamnatin ta umurci masu makarantu, da shugabannin makarantu da dukkan masu ruwa da tsaki da su bi wannan doka sau da ƙafa, tana mai gargaɗin cewa duk wanda ya bijirewa umarnin zai fuskanci hukunci bisa ƙa’idojin ilimin aiki. Ta jaddada cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin dawo da adalci, da inganci da sahihancin jarrabawa a ƙasar nan.














