Ana tsammanin jami’an Hukumar Farin Kaya ta (DSS), sun kai samame gidan Tukur Mamu, mutumin da ke shiga tsakani da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja.
Wasu mazauna unguwar sun shaida cewa jami’an tsaron sun isa gidan ne da ke Kaduna a motoci kimanin 10 da sanyin safiyar yau Alhamis, inda suka yi awon gaba da wasu kayyayaki.
- Chelsea Ta Nada Potter A Matsayin Sabon Kocinta
- Matakan Yayata Ilimin Kimiya Na Kasar Sin Zai Amfani Duniya Baki Daya
Tukur Mamu dai shi ne mutumin da ke shiga tsakanin ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa a Kaduna da kuma iyalansu domin kubutar da su.
Fasinjojin da aka kubutar daga hannun ‘yan bindigar kan fara zuwa ofishinsa da farko, kafin su hadu da iyalansu.
A jiya ne dai ‘yan sandan kasa da kasa na kasar a Masar suka kama Tukur Mamu a filin jirgin saman a birnin Al-khahira, lokacin yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don yin Umarah.
Hakan na zuwa ne bayan rundunar soji, da fannin shari’a sun bukaci abokan huldarsu na kasashen waje su dawo da Mamu gida domin amsa tarin tambayoyin da jami’an tsaron Nijeriya ke son ya amsa musu, masu alaka da batutuwan tsaro da kasar ke fama da su.
A jiya Laraba ne dai, DSS ta fitar da sanarwar cewar Mamu yana hannunta don yi masa tambayoyi.