A ranar 12 ga Satumbar 2022, Mai martaba Etsu Nupe, ALHAJI YAHAYA ABUBAKAR ke cika shekara 70 da haihuwa da kuma shekara 19 a kan karagar sarautar kasar Nupe.
Wakilin LEADERSHIP, TUNDE OGUNTOLA ya zanta da shi game da rayuwarsa da kuma abubuwan da ke faruwa a Nijeriya a wannan zamanin da irin abubuwan da sarakuna suke yi da wadanda ya kamata a sahale musu su rika yi a karkashin kundin tsarin mulki. BELLO HAMZA ya fassara tattaunawar kamar haka:
- Kashi 31 Na ‘Yan Nijeriya Ba Su Iya Karatu Da Rubutu Ba ― Gwamnatin Tarayya
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
Mai Martaba barka da warhaka, muna maka fatan karin wasu shekaru masu albarka cikin koshin lafiya. Tambayata ta farko ita ce, a cikin watan nan na Satumba ake murnar cika shekara 19 da nada ka sarauta da kuma cikar ka shekara 70 a duniya, me za ka ce kan haka?
Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bani tsawon rai da lokacin ganin wannan rana, game da duk wani buki ko wani al’amarin da ya same mu dole mu mika godiya ga Allah da ya bar mu da rai don kamar yadda ka sani “Daga Allah Muke kuma gare Shi za mu koma, saboda haka duk wani abin da kuma halin da muka samu kan mu dole mu gode wa Allah Madaukakin Sarki. Lallai rayuwar na tattare da al’amurra da dama da al’ajabi.
Akwai kalubale da dama a harkokin rayuwa, tun daga lokacin da aka haifi yaro zuwa tasowarsa zuwa balagarsa har zuwan sa makaranta, akwai kalubake da dama amma in ka yi imani ga Allah Madaukakin Sarki za ka tsallake kalubaken ba tare da sani ba. A yayin da kake zirga-zirga a harkokin rayuwa.
Za ka ga abubuwa masu yawa da kuma kalubale masu yawan gaske, wannan kuma tun daga lokacin da aka haife ka ne har zuwa wata shekarar da kake bikin murnar zagayowa a wannan lokacin ne ya kamata ka natsu don yin tunanin yadda ka taso, daga inda kake da kuma inda kake hankoron zuwa a nan gaba.
Amma da farkon farawa muna mika godiyarmu ga Allah madaukakin Sarki da ya bar mu a raye ya kuma ara mana lokaci. Tabbas kalubalen na da yawan gaske, amma muna matukar godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya nuna mana yau har gashi muna bikin cika shekara 70 a duniya a matsayin Sarki na 13 tare da kuma cika shekara 19 a kan karagar mulki. Ina matukar godiya ga Allah madaukakin Sarki.
Ko za ka yi mana tsokaci a kan rayuwarka ta soja kafin ka zama Sarki?
Lallai na samu alfarmar bauta wa kasata a matsayin soja na tsawon shekara 30 kafin in yi murabus in kuma dare karagar mulkin Bida, wata 3 kafin in dare karagar mulkin iyaye da kakanninmu. Tabbas rayuwar gidan soja ta ba mu dama mai yawa na sanin hakikanin kai waye? Da abin da za ka iya yi da kuma irin gudumawar da za ka iya bayarwa don tallafa wa al’umma.
Haka kuma gidan soja ya ba mu damar samun horo da kuma damar tambayar kanka yadda al’amurran ka ke tafiya da kuma yadda halayyar take ta yadda za ka fuskanci rayuwa tare da mutunta al’umma. Mun kuma samu horon yadda za mu kasance a cikin mutane mabanbanta ra’ayi, mutane da suka fito daga bangarori dabandaban na addini, kabila da sauransu.
Za ku kasance tare don gudanar da wasu ayyuka na musamman na ceton rayuka da dukiyoyin al’umma. In har ka kasance tare da mutanen da aka hada ku akwai yiwuwar za ka samu nasarar abin da kuka sa a gaba akwai kuma yiwuwar rashin nasara in har ka kauce wa kasancewa da mutanen da kuke tare, saboda haka ya zama dole ka kasance tare da su don samun nasarar.
Dole ka kasance tare da mutanen da kuke tare ka kuma bi dukakn umarnin da ya fito don samun nasarar da ake bukata, idan kuma muka koma a kan yadda ta kasance tare da ni a matsayina na Sarki, to ni dai mutum ne da ya samu cikakkiyar tarbiya ta fahintar al’umma da kuma iya zama da mutane tare da mutunta su, wannan na da matukar muhimmanci.
Dole ka fahimaci mutane ‘yan’uwanka ka mutunta su don ba zai yiwu ka ce kai ba ka da matsala ba. Ba ka sani ba watakila wani na da wani abin da kai ba ka da shi, kai ma kana da wani abin da ba shi da su, don haka dole ka mutunta mutane ta haka za su ba ka mutuncin ka ba tare da wata matsala ba.
Haka kuma dole ka jure wasu al’amurra don ya zama dole ka yi aiki tare da mutane, don watakila akwai wasu halayyar da da ba ka so daga wasu mutanen da zama ya hada ku, me za ka yi? Sai ka jure don babban burinka shi ne cimma abin da ka sa a gaba. Dole ka jure tare da fahimtar halin da ake ciki, wadannan su ne abin da muka koya a gidan soja kuma Alhamdu lillah muna amfani da su a halin yanzu da yardar Allah.
Mai Martaba zan so mu koma baya a lokacin da kake tasowa a matsayin matashi, ya rayuwa ta kasance? Na biyu kuma ya ka karbi labarin sanarwar zaben ka a matsayin Sarki?
Na taso a cikin iyalina musamman, ana tsayuwa a kan horon ka yadda yakamata. Mahaifina manomi ne Mahaifiyata kuma Malama ce ka kuma san Malamai mutane ne masu tabbatar da ladabi da biyayya, a matsayinsa na manomi kuma yana kusa da halittu.
Abin da nake nufi a nan shi ne a yayin da yake horas da mu ya san lokacin yin shuka da kuma lokacin da ya kamata a girbe. Wananna su ne halayyar Manomi da kuma Malami a lokaci daya don haka dole yaro ya yi ladabi da biyayya. Akan yi maka gyara a nan take in ka yi kuskure in kuma yaro ya ki daukar gyara sai a dauki bulala, wannan shi ne halayyar Malami.
A cikin irin wannan yanayin na taso kuma wannan ne muhimmancin samun Malama a matsayin mahaifiya da kuma Manomi a matsayin Mahaifi. Saboda haka girmama manya da mutunta tsaranka ya zama dole a gare mu.
Muna mutunta duk wani da ya grime mu muna kuma mutunta duk wani abin da muka ci karo da shi. Muna kammala makaranta Firamare da Sakandari sai kawai na zabi aikin soja. Na zana jarabarwar shiga NDA na samu nasara na wuce zaman ganawa da aka yi, a nan ma na samu nasara da maki 14 a shakarar 1973. Daga na muka samu shiga NDA a shekarar 1975 daga nan muka fuskanci horon aikin soja yadda yakamata.
Tun daga nan muka ci gaba da fuskantyar kalubalen aikin soja daban-daban wasu masu tsananin hatsari, muka ci gaba da samun karin girma tare da mukamai daban-daban, wasu mukaman muna so wasu ma ba ma so, amma ya muka iya? Za a tura ka wasu wuaren da ba ka so amma tunda yana cikin aikin, sai ka tambayi kanka, ya za ka yi in wani kalubale ya zo maka? A matasyinka na Kwamanda ana sa ran za ka jagorancin dakarunka tare da kula da lafiya da jindadinsu, dole kuma ka tabbatar da ka kare su kafin ka kaddamar da wani farmaki dole ka sanar da su abin da ke a gabansu tare da tanadar musu da isassun kayan aiki.
Ba zai yiwu ka tura soja ya kai farmaki da sanda ko da baki kawai ba, in ka yi haka wasu sojojin ma ba za su je ba in ma sun je wasu za su dawo maka ba shiri, saboda haka dole ka tanadar musu da kayan aiki tare da karfafa su don su cimma kammala aikin da aka sa su, wannan zai yi matukar amfani a yayin kara musu girma.
Saboda haka ya kamata ka karfafa su don hakan zai taimaka musu tare da basu kwarin gwiwar fuskantar kalubalen da suke son cimma a gabansu, wannan shi ne aikin Kwamanda don ba wai da baki ake aikin Kwamanda ba, ana zama Kwamanda ne ta hanyar lalama, karfafawa da kuma samar wa da dakarunka kayan aiki.
Ina yawan tuna lokacin da na je Laberiya karkashin ECOMOG. Duk lokacin da na tashi nakan dan motsa jiki, in kuma gwada makamai don suna iya kin yin aiki a kowanne lokaci, in kuma suka ki aiki mai zai faru? Saboda haka dole duk safiya mu duba makamai mu goge tare da tabbatar da suna aiki, ina kuma tuntubar dakaruna da karfafa su don tabbatar da ba su da wata matsala, don ta haka ne za su samu kwarin kwiwar fuskantar abokan gaba, amma bai kamata ka bar su haka kawai ba, ya kamata su saba da karar harsashi da sauransu.
Aikin soja na ba ka ilimi mai yawa. In ka samu issashen horo ko karar wani abu ka ji za ka iya tantance daga wani bangare yake zuwa, hagu ne ko dama, ta haka za ka iya kauce wa harsashi in an harbo. Horaswar na da matukar muhimmanci kamar yadda na ce tun da farko iyayena sun ba ni horo yadda ya kamata na taso a yanayi na yin biyayya ga shugabanni.
Ko akwai wani wani hatsari mafi girma da ka taba fuskanta?
Hatsari mafi girma da na fuskanta shi ne lokacin da nake jagorantar dakaruna, an umarci mu bar inda muke mu koma wani wuri a kasar Laberiya, wurin da za mu koma a taswira kawai muka sani an kuma umarci mu je mu mamaye can, tun da aka ayyana mana wannan aikin nake shirya kaina, amma cikin dare ba na iya barci, Dakaruna baccin su suna hutawarsu amma na kasa bacci don ba zai yiwu in bar su haka ba, wurin da ba mu taba zuwa ba, ba mu san abin da za mu tarar a wajen ba. Saboda haka na cire bacci a idona gaba daya.
Wasu daga cikin Dakarun in sun tashi da dare sukan ce, Oga je ka yi bacci mana, amma ba zan iya baccin ba, ina tambayar kaina a kan tsaronmu gaba daya amma babu wata amsa, amma dole mu je mu kwace wurin da aka umarce mu. Da kamar karfe 3 na dare na tayar da kowa da kowa don an shirya za mu tashi da asuba ne.
Sai kawai daga kamar mita 100 cikin daji muka ga abokan gaba sun dunfaro mu. Ba mu ga wadanda suke zuwa ba sai kawai muka ji harbi na fitowa, sai muka kwankwanta da muka lura daga inda ake harbin sai muka mayar da harbin muma.
 Ka san ba mu san daga inda ake harbin ba, ba mu gan su ba amma muna jin su. Sai muka natsu muka saurara don sanin daga inda wutar ke fitowa, cikin ikon Allah sai muka ga abokan gaba a cikin dajin ashe sun yi mana kwantan bauna ne amma cikin ikoin Allah muka gama da su, lallai akwai hatsari kwarai da gaske, bayan an kammala bata-kashi na yi ta tunanin yadda muka yake su, an kashe mun sojoji biyu.
Daya daga ciki shi ne mai kula da na’urar sadarwarmu, an harbe shi ta baya ne, ya kwantar da kansa kamar bai mutu ba sai da na nemi karbar na’urar na lura ya mutu. Tabbass mun ga tashin hankali, amma Allah bai sa kwanan ya kare ba. Lallaii mun fuskanci tashin hankali, wurin da ba ka taba sani ba a cikin kungurmin daji kuma cikin ruwan sama, Allah dai ya kare mu.
Daya bangaren fa, lokacin da aka sanar da nadin ka, ya ka ji?
Lallai na san ni dan Sarauta ne, na san mahaifina cikin kyakywar matsayi muna kuma addu’a, amma a can ciki a, ina ddau’ar Allah ya kawo wannan matsayin. Na tuna a lokacin rantsar da ni wasu da yawa cikin mutanenmu sun yi mamakin cewa, ni dan sarauta ne don ban nuna alama na jiji da kai da kuma nuna ni daga gidan sarauta nake ba. Ina cudanya tare da su, mu yi raha tare da su muna kusan komai tare da su.
Da yawa ba su san ni Sarki ne mai jiran gado ba, ba su san ni dan jinin sarauta ne ba, suna da tunanin bai kamata a ce Yarima na wasu ayyuka kamar sharar kwata da sauransu ba.
Ana umartar ka ka yi tsallen kwado, ina daukar wannan a matsayin horo na aikin soja, in har aikin soja ya umarci shiga kwata me zai sa ba zan shiga ba, in har kuma na ga wasu mutane na shiga mai zai hana ni ma in shiga. Saboda haka zan shiga, daga baya kuma mu fito mu yi wasu harkokin. A NDA muna kiran wannan da suna Puti, saboda haka bayan mun kammala Puti sai mu yi wanka mu dawo tsaftsaf kuma. A lokacin da na zama Sarki sun yi matukar mamaki, ni kuwa ina ta addu’ar Allah ya zama da ni Sarki.
A lokacin da al’amarin ya zo, an bukaci in rubuta takardar neman sarautar a lokacin ina cikin aikin soja, a haka na rubuta takardar, Allah kuma cikin ikonsa na samu nasara. Ba abu ne da na shirya fuskanta ba amma ina nan ina fatan Allah ya ba ni sarautar, don a jinina abin yake, don duk abin da Allah ya shirya za ka zama tabbas sai ka zama. Zama Sarki ba ya bukatar wani shiri na musamman ba kamar zama Likita ba ne, abu ne da yake a jini, in har kana son zama Likita ko Injiniya dole sai ka samu horon da ya dace.
Amma in har kana son zama Sarki ba bukatar wani horo na musamman, halayyar ka da mu’amalarka tare da ayyukan ka na alhairi su ne da kuma imanin ka na fuskantar duk abin da ya same ka daga Allah yake, Allah zai ba ka ilimin da za ka tafiyar da al’umma ba tare da matsala ba, Allah zai kuma ba ka mutane da za su taimaka maka a harkokin tafiyar da mulkinka. Karfafa al’umma don shiga harkar noma wani abu ne dake tattare a cikin abin da muka sa a gaba.
Amma sai kai ma ka zama manomin. Duk lokacin da zan je gona nakan ajiye duk wasu harkokin fada a gefe, in wasu suka zo nema na sai a sanar da su cewa, Sarki ya tafi gona, ta haka labarin zai bazu, ka ga ta haka in wani talaka na zama a gida ya ji labarin Sarki ya tafi gona sai ya ga shi ma ba shi da dalilin zama a gida.
Noma wani abu ne da kowa zai iya yi duk wanda ya fuskanci noma yana cin gumin kansa ne, ba zai yiwu ka ce don ka kammala Sakandire ko ka gama Jami’a ba za ka yi noma ba. Lallai ka yi noma don wata kafar samun kudaden shiga ne.
Ganin yadda ka yi rayuwa a matsayin soja, mene ne ra’ayinka a kan matsalar tsaron da ake fuskanta, kuma wace shawara za ka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari?
Abin takaici ne halin da aka shiga, mutane na cikin matsala saboda ayyukan ta’addancin da ake aikatawa a tsakaninmu. Suna shirya ta’asarsu da daddare suna kuma aiwatar da shi da rana.
A Laberiya, ka riga ka san abokan gabanka ka san sansanin su da inda suke, kwace makamai a hannun ‘yan ta’adda na da matukar hatsari, amma an ba ni jirgi mai saukar angulu, ana kuma iya harbin jirgin, da tuni mun mutu, na biyu kuma ina iya sauka su ki amincewa da ni, a yi bata-kashi, ana iya harbi na in mutu. Saboda haka sai na fuskanci addu’o’i, na shiga sansaninsu da mutane na 7 muka sauka lafiya kalau. Da farko ba su bari mun sauka ba suka ce mu tafi.
Sai da na fito da waya na da hankici ina nunawa a matsayin alamun zaman lafiya, suka kalla daga nan suka ce mu sauka, da muka sauka suka kewaye mu suka bukaci mu ba su makaman mu, muka ba su. Anan ma na yi addu’ar Allah ya bani hikimar da zan tafiyar da lamarin, da ma ina da wani katon goro a aljihu, sai na tambaye su ko suna bukatar goron zaman lafiya. Akwai bukatar yin takatsantsan, na fito da goron na gatsa, daga nan suka canza yanayinsu suka bukaci mu shigo cikin sansaninsu.
Suka ba mu makaman mu daga nan muka shiga tattaunawa. Mun dan fuskanci kalubale da farko, don sun ki mika makamai masu kyau da farko, ana basu Dala 100 a kan kowanne makami da suka mika daga baya suka fara bayar da makamai masu kyau. Amma a irin wannan halin da muke ciki abin da matsala, don me, a kan haka nake ganin akwai wahala a matsayina na uba in boye wani dan ta’adda ko da kuwa suna da dangantaka da matata, kamar ‘yan’uwanta maza ko mata, wani abin takaicin kuma shi ne wannan wayar hannu da muke amfani da ita tana kara kawo matsala a kan yadda za a fuskanci matsalar tsaron, ina tunanin akwa mastaloli masu yawa a kan haka tun da farkon farawa.
Matsaloli da dama, kamar dai aikin ‘yansanda, yadda yake fuskantar matsalar tsaron cikin gida, ba ka san inda mutanen nan suke ba ko suna dauke da makamai ko a’a, lamarin akwai daure kai saboda ba ka sani ba ko ‘yan Boko Haram ne ? ko kuma ‘yan ISWAP ne? Ko harkar garkuwa da mutane ne ko kuma harka ce ta ta’addanci kawai? Duk abin a hargitse yake. Bayan aikin da na yi na samar da zaman lafiya a Laberiya a matsayina na soja ina tunanin mai zai hana in yi irin aikin da na yi a Laberiya a nan Nijeriya?
Tabbas dakarun sojojin Nijeriya a shirye suke kuma suna da kishin aikin su amma saboda matsalar waye ba waye ba a kasar ayyyukan su ya kara wahala, lamarin ya kara haifar da wahala ga ayyukansu har ana ci musu mutunci da bata musu suna wasu ma na cewa, ba sa aikinsu yadda ya kamata, amma suna matukar kokarinsu amma abin da suke fuskanta ya banbanta. Zan ba ka misali, a lokacin da aka fara harkar Boko Haram a Maiduguri, lokacin da sojoji suka je don murkushe su sai aka fara tausaya musu don wasu daga cikin ‘yan Boko Haram na zaune ne a cikin gari tare da iyalansu da rana da dare kuma sun shiga daji.
Lokacin da sojoji suka fahimci haka kuma suna kai hare-hare cibiyoyin tsaro sai suka fara kai musu hari a gidajen su daga nan kuma sai mkutane suka fara ihun cewa ana kashe musu mutane, kuma su ne suke boye ‘yan ta’adda, a kan haka sojoji ba su da wani zabi illa su fuskanci duk wani gida da aka tabbatar da dan ta’adda don a kakkabe shi, wannan ya haifar da tausayi ga ‘yan Boko Haram, wasu ma da ba su san abin da ke faruwa ba suka shiga surutun wai ana kashe masu mutane. Ta haka al’amarin ya yi girma. Wannan ita ce matsalar da muke fuskanta a Nijeriya.
Uwa za ta fito don kare danta komai girman laifinsa, wannan na daya daga cikin matsalolin da ke kara ta’azara lamarin tsaro a kasar mu. A halin yazu suna bin su har zuwa sansaninsu, a da suna bari ne har sai sun kawo musu hari kafin su dauki mataki wannan na da matukar hatsari, don in sun fito suna shiga coci-coci ne da masallatai inda suke kashe kowa da kowa. Saboda haka a halin yanzu sojoji na kai musu farmakji ne a sansaninsu, za kuma ka ga banbanci a dan lokacin da aka fara wannan salon farmakin.
Sarakuna sun fi kusa da al’umma, ana kuma tunanin za a samu nasara a kan matsalar tsaron nan ce ta hanyar samun bayanan sirri daga al’umma. Wace gudunmawa kake ganin sarakuna za su iya bayarwa a wannan bangaren da ya kamata a shigar a tsarin mulki?
Mun dade muna kiraye-kirayen a samar mana da aikin yi a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya. Amma abin takaicin shi ne har yanzu hakarmu ba ta cimma ruwa ba. Amma dai har yanzu muna ci gaba da shawartar gwamnati a matakan jiha da kananan hukumomi da gwamnatin tarayya, saboda a halin yanzu muna da hadakar mu ta sarakuna na Nijeriya inda muke zama daga lokaci zuwa lokaci muna yanke shawara tare da ba gwamnati shawara a kan abin da ya dace. Duk da haka a matakinmu, mun kafa wani ofishi na musamman don sa ido da lura da halin da tsaron ke ciki a yankunan mu.
Muna tara shugababnin addnin Kirsita dan a Musulunci don yin addu’o’i, muna kuma sanar da Sarakuna da Dagatai da su sanya ido a kan duk wanda ke shigowa yankinsu. Muna shawartarsu da su gaggauta kai rahoton duk abin da ba su gane ayyukansa ba don a dauki matakin da ya kamata.
Mun fuskanci ayyukan ‘yan ta’adda a wasu lokuta a nan yankin Bida, sun nemi su takura wa al’umma, ayyukan matasan ya kai ga wasu ba sa iya fita harkokinsu da zaran yamma ta yi a wasu unguwanni, don suna iya kwace duk abin da suka gani a hannunka, mata ne suka fi fuskantar matsalar, suna wulakanta mata fiye da yadda kake tunani, da muka samu rahoton, ‘yansanda suka shigo don kawo karshen lamarin amma da abin ya ci gaba sai muka shigo lamarin.
Muka yi tunanin cewa, tunda muna da matasa masu son zaman lafiya a yankinmu me zai hana mu hada wadannan matasan da wadannan ‘yan iskan? Saboda haka, muka kafa kwamitin tsaro na ‘yan sa-kai, muka sanar da su da su doki duk wani da suka gani yana ayyukan ta’addanci na tayar da hankalin al’umma, da muka fara wannan aikin wasu mutane da ba su iya ladabtar da yaransu ba suka fara rokon mu zo mu ladabtar da yaran nasu.
Ta haka muka samu yin maganin wannan lamarin gaba daya, hanyar da aka bi ta gargajiya ta yi aiki wajen kawo karshen wannan lamarin. Tarbiya da ladabi da biyayya daga gida ne ginshikina. Sun kuma hada da iyaye maza da iyaye mata daga nan kuma shugabanin al’umma.
In har uba zai zo ya nemi a ladabtar da dansa saboda ya tabbatar da kai ne shugaba to lallai ya kamata ka yi wannnan aikin. Watakila ya bar dan nasa ya kangare ne ya kasa ladabtar da shi amma a nan shugabanni na iya shigowa don tallafa wa al’umma. A kan haka ne muke kira a samar wa sarakuna wani aiki na musammana a kudin tsarin mulki musamman ganin muna kusa da al’umma, mun san dukkan abubuwan da suka fi dacewa ga al’ummarmu za kuma mu iya bayar da shawara da gaggawa ba tare da bata lokaci ba.
Muna yawan bayar da misali da lokacin da gwamnati ke shirin kafa cibiyoyin samar da lafiya daga matakin farko (Primary Health Care), gwamnanti ta fara gine-gine a kauyuka ba tare da samar da likitoci da magani ba. Mutanen da ya kamata su amfana har yanzu suna shigowa cikin gari don duba lafiyar su.
Inda sun tuntube mu da mun bayar da shawarar in har ana son gina cibiya 20 to sai a mayar da shi 5 don a samu kudaden da za a tabbatar da isashen magani da likitoci a cibiyar lafiyar da aka gina, amma da ba a nemi shawarrar mu ba yanzu cibiyoyin sun zama kango babu wani cikakken amfani ga al’umma.
Daga karshe, kwanaki Gwamna Yahaya Bello ya ce, ‘yan siyasa ne ke haifar da matsalar tsaro, mece ce shawararka ga ‘yan siyasa?
Ban san inda ya samo wannan tunanin ba amma na damu da yadda al’amarin ke faruwa. Ka san wannan lokaci ne na yakin neman zabe, ‘yan siyasa masu neman mukami za su fara neman matasa marasa aikin yi suna ba su kwayoyi kudi da albarusai don su yaki duk wani da baya ra’ayinsu, a siyasance za su ce abokan hamayyarsu.
Wannan babban kuskure ne, ‘yan siyasan yanzu ba kamar irin su lokacin marigayi Awolowo ba ne, suna zuwa ne suna farawa da bayyana wa mutane abin da za su iya yi tare da lura da abin da al’umma suke tsananin bukata da kuma yadda za su cimman abin da suka sa a gaba, amma a wannan lokacin ‘yan siyasa kan dora wa kansu cewa dole a zabe su, kuma dole a yi maganin duk wanda bai da ra’ayinsu, ta hakan yaran ba za su yi wani tambaya ba na mai yawa ake neman su kashe wani? Daga karshe kuma sai ya yi watsi da matasan in ya kai ga ci ya kuma riga ya mayar da su ‘yan kwaya saboda haka sai su shiga shaye-shaye.
Wannan shi ya sa wasu gwanmnonin ke fuskantar mastaloli na tsaro, sun kasa fuskantar al’umma saboda haka sai suka mayar da alkiblarsu zuwa tayar da zaune tsaye, babban burinsu shi ne kaiwa ga mukamansu.
Mene ne ka fi sha’awar yi a lokacin nishadi?
Ina sha’awar buga kwallon kafa wasu lokutan amma sau da yawa ba ni da lokacin zuwa don yin wasan, saboda haka na kan yi amfani da wayar hannu na. Ina da laptop da iPad. Nakan yi wasan ne don wattsake kwakwalwa ta, kuma lallai kwakwalwar ka na bukatar wattsakewa, idan ba za ka iya motsa jiki ba kai tsaye, dole kwakwalwarka ta zama a wattsake.
Ina da wayata kuma akwai wassani a ciki nakan samu kalubale a ciki, ina iya amfani da wadannan kalubalen wajen harkokina na yau da kullum.