Sanaar Zane-zane na abubuwan da ake tsara su na daya daga cikin sana’oin zamani da ake samun kudi da su sosai saboda yawan abubuwan da ake yi da suka hada da; Bukukuwa da kuma harkokin da suka danganci siyasa.
Yanayin sana’ar Zane na bugawa wato ko kuma dab’i wato (Printing). Ita dai wannan sana’a ta kunshi abubuwa da yawa Wanda ake yin su da Kwamfuta, ka ga akwai bukatar kafin ka fara ya zamanto Cesar ka iya fannonin Kwamfuta wanda ya kamata ka iya.
- Hukuncin Siyar Da Kaya Kafin Su Zo Hannu (Pre-Order)
- Malam Ina So Na Hadu Da Mijina Na Farko A Aljanna, Ko Zai Yiwu?
To a cikinsu sai ka iya Zane kato ka san yadda za ka yi amfani da manhajar zane ko daya ce ta Kwamfuta.
Domin da shi ne za ka zana ko kuma ka tsara yadda aikin da aka ba ka, kamar kalanda ko kuma katin gayyata (inbitation Card) zai iya kasancewa.
Za ka iya koyon Kwamfuta ko ta intanet, ko zuwa makaranta, za ka kuma iya koyo ko ta hanyar YouTube ta hanyar sauke manhaja (downloading).
Da farko dai muhimman abubuwan da kake da bukatar mallaka ko iyawa su ne: 1. Kwamfuta. 2. Iya manhajar Zane ta Kwamfuta. 3. Sanin yanayin takarda da abubuwan amfani. 4. Na’urar buga takardu (Printer). 5. Scanner.
Manhajojin da ake amfani da su:
le ne sai ka iya Kwamfuta musamman a fannin zane, kuma akwai wasu manhajojin da masu wannan sana’a suka fi yawan amfani da su a ko da yaushe.
Coel draw= In dai fannin zane ne ta yi kaurin suna sosai wajen zane da tsara abubuwa su fito sosai kamar su logo, inbitation, poster,certificate da kuma Kalanda.
Iya amfani da wannan manhajar ba karamin Abu ne mai amfani ba saboda kusan duk abubuwan da na ambata maka su a baya kana iya yinsu da ita har ma da karin wasu fiye da su. Manhaja ‘CE’ ta Zane wadda bayan ka yi kana iya fitar da shi a formate na jpg,jpeg da kuma png kuma kana iya dawo da shi normal png na zane zuwa bitmap yadda zai fito kamar hoto.
Amfanin hakan shi ne a lokacin da ka yi buga takarda za ka ga ta yi kyau kamar ba zane ba ta yi kama da hoto sosai.
Corel draw, ta gama duniya ka na iya koyonta a fadin internet irinsu bidiyon YouTube da sauransu, kuma kana iya sauke samfurin Zane.
Inkscape= Itama wata manhajar software CE wadda ake zane da ita kuma kana iya koyonta ko a internet ne. Ita dai kamar yadda Corel take ana yin abubuwan zane da ake kira da bector drawing saboda kusan kamfaninta domin hakan suka yi ta.
Kana iya fitar da zanen da ka yi na katin gayyata ko kuma wasu ayyuka na kalandoji lafiya lau kuma ka na iya sa hoto ka gyara shi yadda zai hau da aikin da kake yi.
Wani abun burgewa ga wannan software din shi ne ita lasisinta kyauta ne kana iya sauke ta daga website dinsu ka yi installing a window, Linud, ko kuma a mac operating sysm ba tare da an nemi ka biya ko sisi ba kuma ba tare da an ce ka sace lisece key ba.
Abubuwan da za ka iya yi=
Idan ka fara wannan sana’a ka samu sanaar hannu wadda ka na iya yin abubuwa daban-daban ga kwastomomin ka wadanda ga su kamar haka: Katin gayyata, Fasta, Banner, Memo, Littafi, Sticker da sauransu.
Yanayin yadda za ka fara:
Wannan sana’a ka na iya farawa da akalla dubu uku 3000 saboda yanayin abubuwan da za ka saya na kayan aiki da kuma yanayin wurin da za ka kama shago a matsayin haya.
Amfanin wannan sana’a kana iya ganin aikin dubu 3000 ko ma dubu goma10,000 ko fiye da haka ya zo maka a lokaci daya ka ga abu ne ba wanda za’a ce yana iya rubewa ba.
Da fatan mai karatu zai yi amfani da wannan don fara wannan sana’a mai albarka.