Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rasuwar Mahaifin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano Kuma Mai rikon kujerar Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano, Usman Bala Muhammad, Alhaji Bala Muhammad Tajuddeen, da babban rashi ga al’ummar Jihar Kano.
Kamar yadda babban Daraktan yaxa labaran gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya shaida wa LEADERSHIP Hausa.
- ‘Yan Bindigan Da Ake Fatattaka Daga Arewa Maso Yamma Na Kwararowa Arewa Maso Gabas – Gwamnoni
- ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Hadimin Gwamnan Bauchi, Sun Jikkata Mutum 1
Ya ce “Mun samu labarin wannan babban rashi wanda ya girgiza mu tare da jimami kwarai da gaske. Babu shakka rashin wannan Dattijo kuma uba a gare mu, rashi ne babba. Abinda ya rage mana shi ne ci gaba da roka masa ragamar Allah.”
Ya kuma nuna farin ciki da abin da mamacin ya bari gwamna Ganduje ya jinjina hakan, kafin rasuwarsa mamacin, mutum ne na gari, dan kasuwa, dattijon arziki abin girmamawa mai kyakkyawan hange sannan kuma guda cikin jajirtattun dattijan unguwa, wanda ya gudanar da rayuwarsa duk cikin tarbiyantar da yaransa.
“Saboda haka a madadin gwamnatin Jihar Kano da al’ummar Kano, ina mika sakon ta’aziyya ga Alhaji Usman Bala Muhammad, shugaban ma’aikatan Jihar Kano kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, tare da sauran iyalan mamacin, abokai da sauran masu yi masa fatan alhairi” In ji Shi.
Gwamna Ganduje, ya kuma yi addu’ar fatan Allah ya gafarta kurakurensa wadanda ya aiwatar a lokacin yana raye, Allah ya karbi kyawawan ayyukansa yasa Aljannatul Firdausi ce makomarsa, sannan Allah ya taimaki iyalan da ya bari tare da yin koyi da kyawawan halayensu.”