Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da asarar da ta yi ta £115.5m a kakar wasa ta 2021 zuwa 2022, duk da kuma kudin shigar ta ya karu da kashi 18 zuwa £583.2m kamar yadda kungiyar ta sanar.
Kungiyar ta bayyana asarar ne a bayanan da take fitarwa na hadahadar kudinta a karshen shekara a watan Yuni, wanda ya nuna asarar ta karu zuwa £23.3m idan aka kwatanta da wadda ta yi a shekarar 2021 kuma bashin da ake bin kungiyar shi ma ya karu, daga £419.5m a 2021 zuwa £514.9m a wannan shekarar, ya karu da sama da kashi 22.
- Hadin Kan Sin Da Argentina Ya Zamo Abun Misali Ga Kasashe Maso Tasowa
- Kiraye-Kirayen Neman Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Wasu Filayen Jiragen Sama Na Jihohi
“Abin da kungiyar ta sanya a gaba shi ne ta yi nasara a wasanni ta kuma
nishadantar da magya bayanmu,” in ji shi shugaban kungiyar Richard Arnold.
Ya ci gaba da cewa “Sakamakn ‘yan wasan da muka dauka a bara irinsu Cristian Ronaldo da Jadn Sanch da kuma Raphael Varane albashi ya karu da kashi 19.1m, yanzu ya kma £616.6m daga £384.2m”.
Wannan ne adadi mafi yawa da aka samu a tarihin Premeir, ya wuce na Manchester City na baya da ya kai £355m.
“Sakamakn da muka samu a 2022 na kudi, ya nuna muna warwarewa daga matsalar annbar krna, cikakkiyar dawowar magoya baya da kuma kara sanya kudin abkan hulda ga tawagarmu,” in ji Cliff Baty.
Sai dai rashin fita wasannin karshen kaka, wanda aka fi sani da wasannin share fagen fara kakar wasa da kungiyyi sukeyi da suka yi zuwa wasu kasashen a 2021, ya kara yawan abubuwan da suke kashewa.
Kudin da aka biya tsoho kcin kungiyar kungiyar le Gunnar Slskjaer wanda aka kra a watan Nuwamba 2021, da maganar Ralf Rangnick wanda ya rike kungiyar na rikn kwarya da sauran tawagarsa sun hada £24.7m.